Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tarbiyyar da mahaifinmu ya ba mu - Halima Dangote
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Halima Dangote da Fatima Dangote da Mariya Dangote su ne ƴaƴa uku na attajirin Afirka, Aliko Dangote, waɗanda a yanzu ke taka muhimmiyar rawa a wasu manyan sassan rukunin kamfanonin Dangote.
A cikin kwanakin nan, mutane da dama sun yi ta tattaunawa kan yadda matan uku ke rayuwa cikin sauƙi, ba tare da yawan bayyana kansu a kafafen sada zumunta ko nuna alfahari da dukiyar da mahaifinsu ya mallaka ba.
Da take magana a wata hira da Bloomberg Next Africa, Halima Dangote ta ce:
"Ba a lalata mana tarbiyya ba. Ba sangarta mu ba. Sau da yawa idan muka haɗu da ƴaƴan wasu abokan mahaifinmu, mu kan yi shiru ba tare da bayyana ko su waye mu ba. Rayuwa ta fi mana sauƙi kafin mutane su fara gane mu."
"Wasu suna son kafafen sada zumunta, amma mu ba haka muke ba. Burinmu shi ne mu taimaka wajen bunƙasa kamfanin mahaifinmu zuwa dala biliyan 100."
Fatima Dangote ce ke kula da harkokin kasuwanci da makamashi, ciki har da matatar mai da masana'antar taki da lantarki, yayin da Mariya Dangote ke jagorantar ɓangaren kayayyakin amfani da kuma siminti. Ita kuwa Halima na aiki tsakanin gudanar da ayyuka da tsara manufofin kamfanin a matakin duniya.
Daga cikin hirar tasu, BBC ta tattaro wasu muhimman darussa da suka ce mahaifinsu ya koya musu wajen gudanar da rayuwa da kasuwanci.
Ƴaƴan Dangote sun bayyana yadda mahaifinsu ya musu tarbiyya
A hirar da suka yi, Halima da Mariya da Fatima Dangote sun bayyana wasu darussa da suka ce mahaifinsu, ya koya musu tun suna tasowa, kuma har yanzu suke amfani da su wajen gudanar da rayuwa da harkokin kasuwanci.
1. Aiki mai nagarta kan kowane abu: Ƴaƴan Dangote sun ce mahaifinsu ba ya amincewa da sakaci ko aikin sangarta. A cewarsu, kullum yana buƙatar ya ga an yi aiki cikin ƙwarewa ta ƙarshe, domin a wurinsa "yana da kyau a samu nagartar aiki".
2. Dogaro da kai da rashin nuna isa: Sun bayyana cewa mahaifinsu ya taso da su cikin tarbiyyar tawali'u da kauce wa nuna isa. Duk da shaharar sunan Dangote, sun ce sun fi son ayyukansu su yi musu magana maimakon yin alfahari da matsayinsu ko dukiyarsu.
3. Samun matsayi ta hanyar jajircewa: Ƴaƴan Dangoten sun ce ba a ba su muƙaman da suke riƙe da su a kamfanonin Dangote saboda kasancewarsu ƴaƴansa ba. Maimakon haka, sun fara aiki a kamfanin a hankali kuma suka gina kansu da ƙwarewa ta hanyar aiki da sakamakon da suka samar.
Sun ce mahaifinsu ya nunar musu da cewa kada su saki jiki suna jiran a basu matsayi saboda gatansu ko kuma alfarmar da suke da ita.
4. Ɗabi'un mahaifinsu na zaburar da su: A cewarsu, ƙwazo da jajircewar mahaifinsu ne ke ci gaba da zaburar da su.
Sun ce ganin irin yadda yake aiki da himma duk da shekaru da nasarorin da ya samu na sa su ƙara ƙoƙarin yin fice a aikinsu.
5. Ci gaba da nuna ƙwarewa: Halima Dangote ta ce har yanzu suna ƙoƙarin tabbatar wa mahaifinsu da sauran mutane cewa sun cancanci matsayin da suke kai.
Ta ce saboda mahaifinsu na sa ran ganin nagarta a kowane lokaci, hakan na sa su ƙara himma wajen aikinsu.
Me ƴaƴan Dangote suka ce game da yadda suke rayuwa?
Halima da Marya da Fatima Dangote sun ce duk da kasancewarsu ƴaƴan fitaccen attajiri, sun taso da su cikin tarbiyyar tawali'u da kauce wa nuna isa.
Wani babban darasi da suka ce mahaifinsu ya koya musu shi ne tunanin gado da ɗorewar kasuwanci, inda burinsu ba wai samun riba ta ɗan lokaci ba ce kawai, sai dai gina kamfanonin da za su ci gaba har tsararraki masu zuwa.
A cewarsu, ba sa yawan bayyana rayuwarsu a bainar jama'a ko neman suna a kafafen sada zumunta. Sun ce sun fi son su yi shiru game da asalin danginsu, kuma ba sa son a riƙa kallonsu a matsayin ƴaƴan masu kuɗi da aka lalata tarbiyyarsu.
Sun kuma bayyana cewa muƙaman da suke riƙewa a rukunin kamfanonin Dangote ba kyauta aka ba su ba. Sun ce sun samu damar ne ta hanyar aiki tuƙuru da nuna ƙwarewa, kuma har yanzu suna ci gaba da tabbatar da cewa sun cancanci matsayin da suke kai.
A cewarsu, maimakon mayar da hankali kan shahara ko matsayin iyalinsu, sun fi son sakamakon aikin da suke yi ya yi musu magana.
Girman matatar Ɗangote
A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, ba Najeriya kaɗai ce ke nuna sha'awar sayen hannayen jarin ba.
A makon da ya gabata, Dangote ya kai ziyara Botswana domin yi wa masu zuba jari bayani kan shirin fitar da hannayen jarin ga jama'a.
Matatar Dangote tana yankin Ibeju-Lekki a Jihar Legas, kuma tana kan fili mai fadin kusan hekta 2,635.
A cewar Rukunin Kamfanonin Dangote, wannan cibiyar za ta kasance mafi girman matatar mai ta babban layi guda ɗaya na sarrafa danyen mai daga farko har ƙarshe, da ake kira da "Single-Train", a duniya mai ikon tace gangar danyen mai 650,000 a rana, tare da masana'antar nau'in roba da ake samarwa daga feutur da iskar gas na "Polypropylene" mai ƙarfin samar da tan 900,000 a shekara.
Idan ta fara aiki da cikakken ƙarfi, ana sa ran matatar za ta iya biyan kashi 100 cikin 100 na buƙatun Najeriya na dangogin man fetur da aka tace, tare da samun ragowar da za a fitar zuwa ƙasashen waje.
An tsara ta ne domin tace nau'o'in danyen mai iri-iri, ciki har da na ƙasashen Afirka da dama, wasu daga Gabas ta Tsakiya da kuma nau'in mai maras kauri na Amurka.
Matatar tana da tankuna 177 da ke da jimillar ƙarfin ajiya na lita biliyan 4.742.
A wata sanarwa daga Dangote, an ce an yi amfani da manyan injinan haƙo yashi mafi girma a duniya wajen cike wurin da yashi mai yawan mita kubik miliyan 65, aikin da ya kashe kusan euro miliyan 300.