Yadda ‘yan bindiga suka sace tsohon babban sojan Najeriya da matarsa a Katsina

A head and shoulders image of Rabe Abubakar wearing a military uniform.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Manjo Janar Rabe Abubakar
    • Marubuci, Makuochi Okafor
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, West Africa reporter
    • Aiko rahoto daga, Lagos
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 2

Yan bindiga sun sace wani babban babban jami’in sojin Najeriya da ya yi murabus, tare da maidakinsa a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Manjo Janar Rabeh Abubakar, wanda ya taba zama mai magana da yawun rundunar sojin kasa ta Najeriya tsakanin 2015 zuwa 2017, an sace shi daga cikin matorsa a lokacin da yake kan hanyarsa ta shiga Katsina daga Kaduna a ranar Asabar.

Hukumomin sun ce yanzu haka suna bakin kokarinsu wajen ganin yadda za su amso sojan, wanda dan asalin jihar ta Katsina ne amma ya fi yawan zama a birnin Kaduna, kamar yadda mai magana da yawun rundunar sojin Nakeriya Janar Michael Onoja ya sanar.

Katsina na cikin jihohin da suka fi fama da matsalar ‘yan bindiga masu satar mutane domin neman kudin fansa, sai dai a baya-bayan nan labarin ya yi sauki bayan matakan da al’umma da kuma gwamnati ta dauka.

Sai dai ci gaba da irin wannan garkuwa da mutane na nuna karuwar wannan matsala ta rashin tsaro wadda ta addabi arewa maso yammacin Najeriya.

A baya-bayan nan irin wannan garkuwa da mutane sun faru a wasu makarantu da ke jihohin kasar, lamarin da ya tayar da hankula, kuma har shugaban kasar ya sha walwaahi karbo wadanda aka sace.

A ranar 25 ga watan Disamban 2025 Amurka ta kaddamar da wani hari kan jihar Sokoto mai makwaftaka da Katsina, kan sansanin wasu masu dauke makamai wadanda aka ce suna da alaka da kungiyar IS.

Katsina na daga cikin jihohin da suka fi fama da wannan matsala.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Zamfara, daya daga cikin jihohin yankin ta shafe fiye da shekara 10 cikin wannan hali, inda was al’ummu suka yanke shawarar nema wa kansu mafita ta hanyar yin sulhu da ‘yan bindiga, sai dai wannan tsari ya kasa kawar da matsalar tsaron da yankin ke fama da shi.

Gwamnatin Najeriya ta ce ta tsananta ayyukan yaki da garkuwa da mutane, cikin har da haramta biyan kudin fansa, to amma hare-haren na ci gaba babu kakkautawa.

Akwai daruruwan dabobin ‘yan bindiga a dazukan yankin, sai dai har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin sace babban sojan.

Argotanni sun ce Janar Rabeh na kan hanyarsa zuwa Katsina ne domin wani bikin aure a lokacin da maharan suma kama shi

Sai dai direban motar tasa ya tsira da raunin harbin bindiga, inda shi kuma sojan da mai dakinsa aka garzaya da su cikin daji.

The abduction comes days after another deadly attack in Katsina state. On Friday, armed men reportedly raided Kiliya village in Dutsinma Local Government Area, killing at least 16 people.

Police have not yet commented on the reported killings.

Residents said the attack happened shortly after Friday prayers, as people gathered to celebrate the Eid al-Adha holiday.

Security agencies had issued warnings about possible attacks during the celebrations, prompting some state governments to introduce measures aimed at limiting large public gatherings and strengthening security.