Abun da ya sa muka tsayar da Jonathan takarar shugaban kasa - PDP

Asalin hoton, OTHERS
Jam'iyyar hamayya ta PDP bangaren Tanimu Turaki, ta bayyana dalilinta na sanar da tsohon Shugaban Kasar, Goodluck Jonathan, a matsayin wanda zai yi mata takarar shugaban kasa a zaben 2027 da ke tafe.
A cewar jama'iyyar tsohon shugaban shi ne mafi cancanta da zai sake jagorantar Najeriya, tana mai nuni da irin ayyukan da ya gudanar a lokacin mulkinsa, da jajircewarsa wajen kare dimokuradiyya, da kuma bambancin da ke tsakanin gwamnatinsa da halin da kasar ke ciki a yau.
Da yake magana bayan wani taron masu ruwa da tsaki, shugabannin bangaren sun bayyana cewa mulkin Jonathan ya kasance wani lokaci na kwanciyar hankali, bunkasar tattalin arziki, hadin kan kasa da kuma girmama cibiyoyin dimokuradiyya.
A cewar jam'iyyar, Najeriya ta samu gagarumar ci gaba a lokacin gwamnatin Jonathan, ciki har da habakar tattalin arziki, karuwar zuba jarin kasashen waje, inganta ababen more rayuwa da kuma gyare-gyare a muhimman bangarori kamar noma, ilimi da sadarwa.
A cewar Ibrahim Abdullahi, mashawarci ga Tanimu Turaki "Yawancin 'yan Najeriya na iya mantawa da irin kwanciyar hankalin da kasar ta samu a lokacin mulkin Jonathan, amma a yanzu halin da aka tsinci kai a ciki ya sa kowa ya tuna kuma jama'a na fatan Jonathan ya dawo don ya tsamo Najeriya daga irin wannan ukuba da take ciki''
Bangaren ya yabawa Jonathan musamman kan yadda ya tafiyar da al'amuransa bayan zaben shugaban kasa na shekarar 2015, inda ya bayyana yanke shawarar amincewa da shan kaye a matsayin daya daga cikin manyan sadaukarwar da wani shugaba a Afirka ya taba yi a tarihin zamani.
"A lokacin da kasar ke fuskantar wani muhimmin yanayi, Jonathan ya fifita zaman lafiya a kan muradin kansa. Ya amince da hukuncin jama'a tare da dora hadin kan Najeriya sama da makomarsa ta siyasa. Wannan mataki nasa ya kara karfin dimokuradiyya tare da jawo masa girmamawa a duniya baki daya," in ji Ibrahim Abdullahi.
Jam'iyyar ta ce mika mulki cikin lumana da Jonathan ya yi ya hana yiwuwar barkewar rikice-rikice tare da kafa kyakkyawan misali na dimokuradiyya wanda har yanzu ake yabawa a fadin Afirka da ma sauran duniya.

Asalin hoton, OTHERS
Yayin da ta kwatanta lokacin mulkin tsohon shugaban da gwamnatin da ke kan karagar mulki a yanzu, bangaren ya yi ikirarin cewa da yawa daga cikin nasarorin da aka samu a lokacin gwamnatocin PDP sun lalace. Ta nuna karuwar matsin tattalin arziki, hauhawar farashin kayayyaki, rashin tsaro da kuma tashin farashin kayan masarufi a matsayin hujjojin da ke nuna cewa kasar ta kauce daga tafarkin ci gaba.
"A yau, 'yan Najeriya na fuskantar kalubale da ba a taba ganin irinsu ba. Tsadar rayuwa ta yi muni, harkokin kasuwanci na fuskantar matsaloli, kuma iyalai da dama ba sa iya biyan bukatunsu na yau da kullum. Wahalhalun da ake ciki a fadin kasar sun sa mutane da dama na tambayar alkiblar shugabancin nan da ake da shi," in ji shi.
A cewar PDP, gogewar Jonathan, da tawali'unsa da kuma biyayyarsa ga manufofin dimokuradiyya ne suka sa ya zama wanda ya fi kowa dacewa da dawo da amincewar jama'a ga gwamnati tare da farfado da tattalin arziki.
"Ba mu gabatar da Jonathan ba ne kawai saboda ya taba zama shugaban kasa. Mun gabatar da shi ne saboda tarihinsa. 'Yan Najeriya sun samu zaman lafiya, kwanciyar hankali a dimokuradiyya da kuma bunkasar tattalin arziki a karkashin jagorancinsa. Sadaukarwar da ya yi wajen amincewa da shan kaye ta nuna kwarewa da dattaku a shugabanci, kuma mun yi imanin cewa irin wadannan halaye ne ake bukata yanzu fiye da kowane lokaci."
A karshe, bangaren Turaki na PDP ya yi kira ga 'ya'yan jam'iyyar da daukacin 'yan Najeriya da su mara wa wannan hangen nesa na shugabanci baya, wanda ya ta'allaka ne kan hadin kan kasa, farfado da tattalin arziki da kuma karfafa dimokuradiyya.
"Mun yi imanin cewa Najeriya za ta iya sake tashi tsaye. Mun yi imanin cewa kasar nan ta cancanci shugabanci da zai fifita bukatun jama'a. Wannan ne ya sa muka zabi Jonathan a matsayin dan takararmu." inji Ibrahim Abdullahi










