KAI TSAYE, Sifaniya ta gayyaci Yamal kofin duniya amma ba ɗan Real Madrid ko ɗaya

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga Litinin 25 zuwa Lahadi 31 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

  • Conte ya bar Napoli shekara ɗaya tsakani da lashe Serie A
  • Messi ya ji rauni, ko zai shafi zuwansa gasar kofin duniya?
  • Pabregas ya kai Como Champions League a karon farko a tarihin ƙungiyar
  • United da Arsenal da PSG na son Fernandes, AC Milan za ta riƙe Modric
  • Iraola ya yi ban kwana da Bournemouth, bayan samun gurbin Europa League
  • Rangers ce ta lashe kofin Premier League na Naigeria na bana
  • Ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp
  • Djokovic ta tirki rawa bayan kai wa zagaye na biyu a French Open
  • Za ku iya tafka muhara a shafnmu na sada zumunta a BBC Hausa Facebook

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Sifaniya ta gayyaci Yamal gasar kofin duniya, amma ba ɗan Real Madrid ko ɗaya, Gasar kofin duniya

    Ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal, ya samu goron gayyata a cikin tawagar Sifaniya da za ta buga gasar FIFA World Cup, duk da cewa yana jinya.

    Matashin mai shekara 18 ya bai buga wasu wasannin karshen kakar La Liga ba, sakamakon raunin da ya ji ranar 22 ga watan Afirilu.

    Sai dai kuma a karon farko babu wani ɗan ƙwallo daga Real Madrid a tawagar ta Sifaniya, yayin da ba aka ajiye mai tsaron baya, Dean Huijsen da kuma Dani Carvajal.

    Kocin Sifaniya, Luis de la Fuente, ya ce bai duba ƙungiya ko ɗan wasa ya duba cancanta da wanda yake kan ganiya.

    Ƙungiyar Real Madrid ta ci karo da koma baya a kakar nan, bayan da ta kasa lashe kofi ko ɗaya kuma karo na biyu a jere a tarihi.

    Haka shima ɗan wasan Athletic Bilbao, Nico Williams, wanda ke jinya shima yana cikin tawagar ta mutum 16.

    Gasar Kofin Duniya za ta gudana daga 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yuli.

    Sifaniya za ta fara da fuskantar Cape Verde ranar 15 ga watan Yuni, sannan ta kara da Saudi Arabia ranar 21 ga watan Yuni, kafin ta haɗu da Uruguay ranar 26 ga watan Yuni a wasannin cikin rukuni.

    Ga jerin ƴan wasan tawagar Sifaniya:

    Masu tsare raga: Unai Simon (Athletic Bilbao), David Raya (Arsenal), Joan Garcia (Barcelona).

    Masu tsare baya: Marcos Llorente (Atletico Madrid), Marc Pubill (Atletico Madrid), Pedro Porro (Tottenham), Aymeric Laporte (Athletic Bilbao), Eric Garcia (Barcelona), Pau Cubarsi (Barcelona), Marc Cucurella (Chelsea), Alejandro Grimaldo (Bayer Leverkusen).

    Masu buga tsakiya: Rodri (Manchester City), Martin Zubimendi (Arsenal), Mikel Merino (Arsenal), Pedri (Barcelona), Gavi (Barcelona), Fabian Ruiz (Paris St-Germain), Alex Baena (Atletico Madrid).

    Masu cin ƙwallaye: Yeremy Pino (Crystal Palace), Victor Munoz (Osasuna), Mikel Oyarzabal (Real Sociedad), Ferran Torres (Barcelona), Lamine Yamal (Barcelona), Dani Olmo (Barcelona), Nico Williams (Athletic Bilbao), Borja Iglesias (Celta Vigo).

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Iraola ya yi ban kwana da Bournemouth duk da samun tikitin zakarun Turai, Premier League

    Magoya bayan Bournemouth sun rera waka suna cewa: “We’re all going on a European tour” yayin da suka yi murnar ganin ƙungiyar ta samu tikitin shiga gasar Turai ta baɗi a ranar Lahadi.

    Duk da cewa burinsu na kaiwa Champions League bai cika ba, ƙungiyar ta Andoni Iraola ta tabbatar da samun matakin shiga Europa League a karshen kakar Premier League.

    A wasan karshe da suka tashi 1-1 da Nottingham Forest a ranar Lahadi, Bournemouth ta tabbatar da matsayinta na shida a teburi, wanda ya isa ya ba su tikitin shiga gasar Turai. Wannan nasara ta zo ne bayan sauyi mai ban mamaki da Iraola ya kawo a cikin shekara uku da ya yi a ƙungiyar

    Iraola ya karɓi aikin horar da Bournemouth a lokacin da suka kare a matsayi na 15 a kakar 2022-23, wanda aka ɗauka a matsayin cigaba, bayan rikicin da ya biyo bayan doke su 9-0 da Liverpool ta yi musu da kuma sauya Scott Parker da Gary O’Neil.

    Yanzu kuwa, sun kammala kakar a matsayi na shida a Premier League, abin da ya ba su damar buga Europa League a kakar wasa mai zuwa.

    Tsohon kocin RB, Leipzig, Marco Rose, shi ne zai gaji Iraola, kuma shi ne zai ɗauki nauyin ci gaba da gina nasarorin da aka samu a Bournemouth.

    Bayan tabbatar da tikitin Europa League, Iraola ya samu tafi daga magoya bayan Nottingham Forest, abin dmagoya baya sun yi tafa masa da nuna irin girmamawar da suka yi masa a gasar.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  3. , Daga Jaridu

    Manchester United ta tuntubi West Ham a kan dan wasanta na tsakiya Mateus Fernandes, ko za a sayar mata da matashin mai shekara 21 da ke taka wa tawagar Portugal leda, wanda kuma Arsenal da Paris St-Germain su ma suke sa ido a kan shi, inda aka yi masa farashin fam miliyan 80. (Mail)

    Haka kuma Manchester United ta yi nisa a tattaunawa da Atalanta a kan cinikin dan wasan tsakiya Ederson, dan Brazil mai shekara 26, sai dai har yanzu akwai rashin cimma matsaya tsakanin kungiyoyin biyu kan farashin dan wasan. (Sky Sports)

    Tottenham ta dauke hankalinta daga dan wasan Roma mai kai hari Paulo Dybala mai shekara 32, wanda ya ci Kofin Duniya da Argentina a 2022. (Football Insider)

    Nottingham Forest na shirin cinikin dan wasan tsakiya na Middlesbrough, Hayden Hackney, dan Ingila mai shekara 23. (Teamtalk)

    Fenerbahce na sa ido a kan dan wasan Faransa, Randal Kolo Muani, mai shekara 27, wanda ya yi wannan kakar a Tottenham a matsayin aro daga Paris St-Germain. (Fanatik)

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  4. An sa hoton ƙwallon da McTominay ya ci Denmark a takardar kuɗin Scotland, Scotland

    Bankin Scotland ya ƙaddamar da takardar kuɗi ta musamman mai darajar £20, wacce ke ɗauke da hoton shahararriyar ƙwallon da Scott McTominay ya ci wa Scotland man ban sha'awa.

    An kirkiro wannan takarda ne domin murnar komawar Scotland zuwa gasar FIFA World Cup bayan samu tikitin shiga gasar a karon farko tun bayan shekarar 1998.

    Tsarin takardar ya haɗa abubuwan gargajiya na takardun kuɗi tare da hoton kwallon da Scott McTominay ya ci Denmark a wasan neman gurbin shiga gasar.

    Takardu 100 kacal aka buga daga wannan nau’i na musamman, inda guda 50 za su kasance ta hanyar gwanjon masu tara kayayyaki, ƙyautar caca, da kuma wasu wuraren nune-nune a Edinburgh da Glasgow.

    Tawagar Scotland ta samu gurbin shiga gasar Kofin Duniya bayan da ta doke Denmark da ci 4-2 a filin Hampden Park a watan Nuwamba.

    McTominay ne ya fara cin ƙwallon mai ban mamaki, wacce ta zama daya daga cikin manyan lokutan da suka taimaka wa Scotland komawa babban matakin ƙwallon kafar duniya.

    Liv

    Asalin hoton, Bank of Scotland

  5. Tarihin da Guardiola ya kafa a Manchester City, Manchester City

    Ga jerin wasu nasarorin da Guardiola ya samu a Premier League tare da Manchester City da ya horar.

    • Ƙungiyar Premier League da ta lashe Premier League huɗu a jere
    • Wadda ta haɗa maki ɗari a kaka ɗaya a Premier League (100 - 2017/18)
    • Ta farko a Premier League da ta samu maki 90 ko fiye da haka
    • Kocin da ya ci na 100 da 150 da 200 da kuma 250 a Premier League a karancin wasanni.
    • Kociyan da ya haɗa maki 500 da 600 da 700 da kuma 800 a Premier League.
    • Cin wasa da yawa a cikin shekara ɗaya (36 - 2021)
    • Kakar da ci wasanni da yawa a Premier League (32 - 2017/18 da kuma a 2018/19)
    • Cin ƙwallaye da yawa a kakar Premier League (106 - 2017/18)
    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Messi ya tsorata da raunin da ya ji daf a fara gasar Kofin Duniya, Argentina

    Ƙyaftin ɗin, Argentina, Lionel Messi, ya ji tsoro da rauni da ya ji daf a fara gasar Kofin Duniya, bayan ya nemi a sauya shi yayin wasan Inter Miami a gasar Major League Soccer a ranar Lahadi.

    Kocin Inter Miami, Guillermo Hoyos, daga baya ya bayyana cewa maye gurbin ɗan wasan mai shekara 38 a karawar da suka buga da Philadelphia Union ya kasance domin kariya, sakamakon yanayin fili da ya yi nauyi saboda ruwan sama a Miami.

    Messi, wanda ya lashe Kofin Duniya na 2022, ya bar filin a minti na 73 bayan da ya kama bayan cinyarsa ta hagu, sai dai an gan shi yana tafiya cikin kwanciyar hankali yayin da ya nufi ɗakin canza kaya.

    Messi bai tabbatar da cewa zai buga wa Argentina gasar Kofin Duniya mai zuwa ba, amma ana sa ran zai kasance cikin tawagar da za ta kare kambunta a gasar da za a fara a ranar 11 ga watan Yuni, wadda Amurka, Kanada da Mexico za su karbi bakunci.

    Argentina za ta fitar da jerin ƴan wasanta a mako mai zuwa, kuma za ta fara wasa da Algeria a ranar 16 ga Yuni.

    Tun lokacin da ya koma Inter Miami a 2023, Messi ya rika rage yawan wasanninsa saboda kula da lafiyarsa, duk da cewa ya sha fama da matsalar raunin cinyarsa a wasu lokuta.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Rangers ta amince da ɗaukar Lawrence Shankland, Rangers

    Ƙungiyar Rangers ta cimma yarjejeniya da Heart of Midlothian kan ɗaukar ƙyaftin ɗinsu, Lawrence Shankland da zarar an kammala yi masa gwajin koshin lafiya da za a yi masa a kwanaki masu zuwa.

    Ɗan wasan na tawagar Scotland, wanda aka dade ana danganta shi da komawa Ibrox, ana sa ran zai zama cefanen farko na sabon koci, Danny Rohl a wannan bazarar.

    Shankland mai shekaru 30 ya taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar Hearts zuwa matsayi na biyu a wannan kakar.

    Tun zuwansa Hearts a 2022, ya zura ƙwallaye 88 a wasa 171 da ya buga wa ƙungiyar. Haka kuma, yana cikin ƴan wasa mafi zura kwallaye a Scottish Premiership tun bayan fara gasar a 2013.

    A jimlace kuma, Shankland ya zura kwallaye 236 a wasanni 494 da ya buga a matakin ƙungiya, sannan ya zura kwallaye huɗu a wasa 18 da ya buga wa tawagar Scotland.

    Live

    Asalin hoton, SNS

  8. , Daga Jaridu

    Kyaftin din Tottenham Cristian Romero, mai shekara 28, zai so hadewa da dan kasarsa Argentina, Diego Simeone a Atletico Madrid. (Teamtalk)

    Ana sa ran dan bayan Crystal Palace Maxence Lacroix, mai shekara 26, zai bar kungiyar a bazara, inda kungiyoyin Firimiya da yawa ke son dan wasan na Faransa.(RMC Sport)

    Tottenham na duba yuwuwar neman mai tsaron ragar Benfica Anatoliy Trubin, dan Ukraine mai shekara 24, a bazara. (A Bola)

    Darektan wasanni na AC Milan Igli Tare na da kwarin gwiwa cewa tsohon dan wasan tsakiya na Croatia Luka Modric, mai shekara 40, zai sake kulla yarjejeniyar zama a kungiyar tsawon karin shekara daya. (DAZN via Football Italia)

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Fabregas ya kai Como zuwa Champions League a tarihi, Champions League

    Kungiyar Como ta Cesc Fabregas ta samu tikitin shiga gasar Champions League a karon farko a tarihinta, bayan da ta doke Cremonese da ci 4-1 a ranar karshe ta kakar Serie A.

    Wannan nasara ta Como, tare da doke AC Milan 2-1 a hannun Cagliari, ya tabbatar da cewa Como ta kare a matsayi na huɗun teburi, wanda ya ba su tikitin zuwa gasar zakarun Turai. A daya bangaren kuma, wannan sakamako ya tabbatar da faduwar Cremonese zuwa Serie B.

    Tsohon ɗan wasan Arsenal da Chelsea da Barcelona, Fabregas mai shekara 39, ya bayyana cewa wannan nasara tana daga cikin manyan nasarorin rayuwarsa.

    Kafin wasan, Como na bukatar nasara tare da fatan ko AC Milan ko Roma za su rasa maki, domin ta samu tikitin Champions League.

    Roma ta doke Hellas Verona, wadda ta kare a matsayi ta uku, amma rashin nasarar Milan da Cagliari ya bai wa Como damar tsallaka Milan zuwa huɗu na farko.

    Wannan kuma ya janyo Juventus ta rasa tikitin Champions League. Juventus ta fara wasa ranar Lahadi a matsayi na shida kuma tana bukatar nasara tare da fatan wasu ƙungiyoyi su yi kuskure.

    A wasan hamayya da Torino, wanda aka jinkirta na awa ɗaya saboda dalilan tsaro bayan rikici tsakanin magoya baya, Juventus ta tashi 2-2.

    A karshe, sakamakon Roma da Como ya tabbatar da cewa Juventus za ta buga gasar Europa League a kakar wasa mai zuwa.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  10. Conte ya bar Napoli kaka ɗaya da lashe Serie A, Napoli

    Kocin Napoli, Antonio Conte, ya sanar cewa zai bar ƙungiyar a karshen wannan kakar, watanni 12 kacal bayan da ya jagorance su zuwa lashe kofin Serie A.

    Tsohon kocin Chelsea da Tottenham ya karɓi ragamar Napoli a shekarar 2024, kuma a kakarsa ta farko ya jagoranceta zuwa lashe kofin gasar Serie A, wanda shi ne na huɗu a tarihin ƙungiyar ɗin.

    Sai dai a wannan kakar, Napoli ta kare a matsayi na biyu da maki 11 tsakani da Inter Milan, wadda ta lashe kofin bana.

    A gasar Champions League – wacce Conte ya sha wahala wajen samun nasara a cikinta – Napoli ta kasa kaiwa matakin zagaye na biyu.

    Bayan da Napoli ta doke Udinese da ci 1-0 a wasan su na karshe a kakar a ranar Lahadi, Conte ya sanar da ficewarsa a wani taron manema labarai tare da shugaba, Aurelio De Laurentiis.

    Lokacin da aka tambaye shi ko zai iya zama sabon kocin tawagar ƙasar Italiya, Conte ya ce: “Shawarata ita ce a ɗauki Pep Guardiola.”

    Conte ya kusan barin Napoli a bazarar da ta gabata, amma aka shawo kansa ya ci gaba bayan tattaunawa da De Laurentiis.

    Napoli ta ƙara ɗaukar sabbin ƴan wasa kamar Kevin De Bruyne da Rasmus Højlund, amma raunin da wasu daga fitattun ƴan wasa, ya sa Conte ya kasa kare kofin da ya ɗauka.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  11. Barkanmu da shiga fagen labarin wasanni

    Jama'a barkanmu da kasancewa a cikin shirin labarin wasanni da za mu ke sanar da ku wainar da ake toyawa daga wannan ranar zuwa Asabar 18 ga watan Afirilu.

    Sunana Mohammed Abdu za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko kuma ku bibiyi labaran da muke wallafawa a BBC Hausa WhatsApp.