Yadda Iran ke amfani da ƙananan jiragen ruwa wajen gallaza wa Amurka a Mashigar Hormuz

    • Marubuci, Luis Barrucho
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

A kwannan nan shugaba Donald Trump na Amurka ya yi ikirarin cewa ya ''tarwatsa rundunar sojin ruwan Iran'', yana mai cewa ''a yanzu karfin ta bai wuce na amfani da kananan jiragen ruwa masu dauke da bindiga ba''.

Amma kuma wadannan ''kananan'' jiragen ruwan yaki da wasu masu sharhi a yammaci suka yi wa lakabi da ''sauro'' suna aikata barna sosai.

Tsawon watanni, wadannan jiragen ruwa sun janyo mummunar illa a mashigar Hormuz, wadda ke da matukar muhimmanci ga safarar kayayyaki zuwa sassan duniya, wani lamari da kwararru ke cewa mataki ne na durkusar da tattalin arzikin duniya da kuma tilastawa Washington ta dakatar da yakin da take da Tehran.

Amma ya wadannan jiragen suke kuma ko sun tabbatar da tasirin su?

'Tsoratarwa, rikitarwa da mamaya

An kirkiri kananan jiragen ruwan masu karfi da gudun gaske ne a 1980, lokacin yakin Iran da Iraq.

Duk da cewa Iran ta yi yaki ne da Iraq, amma fadan ya watsu zuwa sassan yankin Gulf, lamarin da ya sanya Amurka ta shiga domin bayar da kariya ga aikin jigilar mai.

Karawa da dakarun ruwan Amurka ya sa jiragen ruwan yakin Iran sun lalace sosai.

Daga nan ne kananan jiragen ruwa na yaki suka fara zama wadanda kasar ta dogara da su wajen kai hari da kuma samar da kariya daga harae-haren kasashe.

Jiragen sun kasance wani bangare ne na tsare-tsaren yaki da Iran ke amfani da su, baya ga jiragen sama marasa matuki da dasa nakiya da kai hari gabar tekuda kuma afkawa makwabtan ta masu alaka da kasashen da take yaki da su.

Jiragen wadanda dakarun juyin juya halin Iran ke amfani da su, an kera su ne domin ''tunzurawa da rikitarwa da kuma mamaye abokan gaba,'' in ji Saeid Golkar, wani farfesa a jami'ar Tennessee da ke Chattanooga kuma babban mai bayar da shawara ga wata kungiya mai rajin hana Iran mallakar makamin nukuliya, United Against Nuclear Iran (UANI).

Ya kara da cewa "Rundunar juyin juya hali ta Iran tana sane cewa ba za ta iya tunkarar Amurka a yakin gaba da gaba ba,''

A madadin haka sai ta karkata ga kai hare-hare kan jiragen ruwa masu wucewa ta Hormuz, lamarin da ya kawo cikas sosai ga jigila a mashigar.

Daga cikin dabarun da jiragen ke amfai da su sun hada da harbi kan jiragen jigilar kaya da dasa nakiyoyi a karkashin ruwa da kuma yin kawanya ga jirage daga kowanne bangare.

Jiragen suna dauke da manyan bindigori masu cin nisan zango da kuma makamai masu linzami.

Mafi yawan su dai jiragen ruwan yaki ne da rundunar sojin Iran ta kera, amma akwai tsirarun na fararen hula da rundunar ta karba daga hannun masunta.

Jiragen suna d saukin kerawa da kuma gyarawa, in ji Can Kasapoglu, wani mai bincike a cibiyar Hudson da ke Washington.

Wannan ya bai wa Iran damar kai hari kan jiragen ruwan soji da na jigilar kaya cikin sauki, tare da je fa tattalin arzikin duniya cikin hatsari,'' in ji Kasapoglu.

Kwararru sun ce burin Iran shi ne tilastawa Washington ta watsar da yakin da ta ke yi da Tehran da kuma samun kariya daga masu irin wannan tunani a nan gaba.

Saboda rashin girman su, jiragen suna da wuyar hangowa daga nesa, don haka sai an matsa kusa da su, ko kuma an yi amfani da wasu kananan jiragen ruwa ko jirage masu saukar ungulu kafin a gano su.

Har yanzu ba a tantance girman jiragen ba saboda ana boye su ne a cikin koguna ko karkashin kasa a gabar tekun kudancin Irn.

Amma na yi kiyasin cewa yawan su ya kai 500 ko sama da 1,000.

Gwamnatin Iran tana yawan gudanar da atisayin sojin ruwa, ciki harda wadanda take baje kolin bajinta da wadannan jirage.

'Yakin sunkurun cikin teku'

Masu sharhi sun bayyana salon da Iran ke amfani da shi a matsayin yakin sunkuru na kan teku.

Yayin da rundunar sojin ruwan Amurka ta yi nasarar tarwatsa manyan jiragen ruwan yakin Iran wadanda suka bayyana a kan teku, rundunar juyin juya halin Iran na taka tsantsan don gudun yakin gaba da gaba da dakarun Amurka, in ji Golkar.

Ya ce ''Iran na ta kokarin kaucewa duk wani yanayin fito na fito da Amurka, don haka ta dauki salon sunkuru ta hanyar amfani da kananan jiragen ruwa masu gudun gaske,''

A bisa wannan yanayi, Iran na iya maye gurbin jiragen da suka lalace a cikin sauki yayin da Amurka da kawayenta ke tura manyan jiragen ruwa da na sama domin kare jiragen jigila daga harin Iran.

Ko salon Iran na yin kyau?

Jigilar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz ta samu koma baya tun bayan fara yakin.

Masu sanya ido kan hada hada a mashigar sun ce alkalumansu sun nuna cewa jiragen ruwa 10 ke wucewa ta mashigar kowacce rana, wato kashi 8 cikin 100 kenan, inda kafin yakin ake samun akalla jiragen ruwa 60 masu wucewa ta Hormuz.

Rundunar sojin Birtaniya mai sanya ido kan harkokin sufuri a mashigar ta ce an samu raguwar hada-hada a Hormuz da kashi 90 cikin 100 idan aka kwatanta da yadda abin yake kafin yaki.

An dan samu farfadowar harkoki a mashigar bayan sanar da tsagaita wuta tsakanin Amurka da Isra'ila a bangare guda da kuma Iran a dayan bangaren, amma yan kwanaki bayan sanarwar sai aka koma gidan jiya bayan Amurka ta sanar da kafa shinge domin hana shiga da fita Iran.

An kuma ci gaba da kai hare-hare kan mashigar.

Hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa jiragen ruwa akalla 1,500 da ma'aikata 20,00 ne rufe mashigar Hormuz ya shafa.

Raguwar man da ake jigila ta mashigar Hormuz ya janyo krancin mai da kuma tsadar shi a sassan duniya.