Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wace riba Saudiyya ke samu daga yaƙin Iran da Amurka?
Kamfanin Saudi Aramco ya bayyana cewa ribarsa a zango na biyu na shekarar 2026, a daidai lokacin da ake fama da tashe-tashen hankula a yankin sakamakon yaƙin Iran da kuma babban tangarɗar da aka samu ga zirga-zirgar jiragen ruwa a Tekun Fasha, ta kai mafi ƙololuwa tun shekarar 2022.
Aramco ta samu wannan ribar ne duk da cewa yawan man da Saudiyya ke haƙowa da kuma fitar da shi zuwa ƙasashen waje ya ragu, inda aka karkatar da kaso mai yawa na man ƙasar ta hanyar tekun Maliya.
Ribar Aramco a wannan zango ta wuce dala biliyan 33, wanda ya nuna karin kusan kashi ɗaya bisa uku idan aka kwatanta da irin wannan lokaci a bara.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, ribar da kamfanin ya samu bayan cire haraji da sauran kuɗaɗe ta ƙaru da kashi 44 cikin ɗari.
Waɗannan alƙaluman biyu sun samo asali ne daga hanyoyin lissafin kuɗi daban-daban, amma dukansu suna nuna gagarumar ƙaruwa a ribar Aramco.
Wannan ƙaruwa ta riba, wadda ta zo daidai da lokacin yaƙin Iran, ta haifar da tambayoyi kan ko yadda mafi girman kamfanin mai a duniya ya yi fice a fannin kasuwanci na nuna cewa gwamnatin Saudiyya ta amfana daga wannan yaƙi, da kuma ko bayanan kuɗin Aramco suna nuna ainihin halin da tattalin arzikin Saudiyya yake ciki.
Me ya sa ribar Aramco ta ƙaru duk da raguwar yawan man da take haƙowa?
Yawan man fetur da iskar gas da Aramco ta samar a zangon na biyu na shekarar 2026 ya ragu da kusan kashi 25 cikin ɗari idan aka kwatanta da irin wannan lokaci a bara.
Sai dai farashin man da kamfanin ya sayar ya ƙaru da sama da kashi 60 cikin ɗari.
Kuɗaɗen da aka samu daga hauhawar farashin sun rama tasirin raguwar samar da mai da kuma fitar da shi ƙasashen waje.
Ƙwararriyar tattalin arziki, Carol Nakhle, babbar jami'ar gudanarwa ta kamfanin ba da shawara kan makamashi na Crystol Energy, ta shaida wa BBC Persian cewa ba Aramco kaɗai ba ne ya amfana daga wannan yanayi.
"Aramco, kamar sauran kamfanonin mai da suka ci gaba da fitar da mai zuwa kasuwannin duniya a lokacin yaƙin baya-bayan nan, ta amfana daga hauhawar farashin mai", kamar yadda ta yi ƙarin haske.
Nakhle ta kuma ce ƙarancin kuɗin da Aramco ke kashewa wajen haƙo mai ya kasance muhimmin dalili.
"Ga kamfani mai samar da mai da kuɗi ƙalilan kamar Aramco, hauhawar farashi ba wai kawai tana rage tasirin raguwar samarwa da fitar da mai ba ne, har ma da samar da kuɗaɗen shiga fiye da na baya," in ji ta.
A cikin rahoton kuɗinta, Aramco ta bayyana cewa ƙaruwa a ribarta ya fi samo asali ne daga hauhawar farashin ɗanyen mai, kayayyakin man fetur da kuma kayayyakin sinadarai.
Sashen tace mai da tallace-tallace na Aramco ya amfana daga hauhawar farashin kayayyaki kamar dizal da man jirgin sama, tare da ƙarin ribar da ake samu daga tace mai.
Ribar aiki a wannan sashe ta kusan ninka sau biyu.
Haka kuma, cibiyar matatun mai da masana'antun sinadarai da rumbunan ajiya da harkokin kasuwancin Aramco a cikin Saudiyya da ƙasashen waje sun bai wa kamfanin damar samun ƙarin kuɗaɗen shiga daga hauhawar farashin kayayyaki.
Wannan ƙaruwa a kuɗaɗen shiga ba ta taƙaitu ga Aramco kaɗai ba.
Lokacin da Aramco ta sanar da sakamakon kuɗinta na wannan zangon, kamfanin BP ma ya bayyana cewa ya samu ribar dala biliyan 5.73 a zangon na biyu na shekarar 2026, sama da ninki biyu na ribar da ya samu a irin wannan lokaci a bara, kuma ita ce mafi girman ribarsa ta kowane zango tun shekarar 2022.
Kamfanonin Exxon Mobil, Chevron da Shell ma sun samu ribar da ta fi ta shekarar da ta gabata.
Sai dai, babban kaso na man da Aramco ke fitarwa zuwa ƙasashen waje yawanci yana bi ne ta hanyar da yaƙin ya shafa kai tsaye.
Ta yaya bututun da Saudiyya ta shimfiɗa ya rage mata tsadar fitar da mai?
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka bai wa Aramco damar ci gaba da fitar da man fetur shi ne bututun da ƙasar da shimfiɗa domin fitar da mai da ke yi wa laƙabi da ''East-West Pipeline''.
Wannan bututu yana jigilar mai daga cibiyoyin Abqaiq da ke gabashin Saudiyya zuwa tashar jiragen ruwa ta Yanbu da ke gabar Tekun Maliya.
Carol Nakhle ta shaida wa BBC cewa wannan bututun ya bai wa Saudiyya damar da ta fi wasu maƙwabtanta.
"Saudiyya ta samu damar karkatar da wani kaso mai yawa na ɗanyen man da take fitarwa zuwa ƙasashen waje ta hanyar bututun zuwa Tekun Maliya, wanda ya rage mata dogaro da mashigar Hormuz, duk da cewa hakan bai wadatar ba'', in ji ta.
Ƙasashe kamar Iraki da Kuwait suna da ƙarancin wasu hanyoyin fitar da man fetur, wanda hakan ya sa suka fi fuskantar haɗarin tangardar zirga-zirgar jiragen ruwa.
Bututun, wanda zai iya jigilar kusan ganga miliyan 5 na mai a kowace rana, ya zama babbar hanyar da Aramco ta yi amfani da ita a lokacin yaƙin Iran da rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya.
A cewar wani rahoto da jaridar New York Times ta wallafa, Saudiyya ta karkatar da sama da kashi 70 cikin ɗari na man da take fitarwa zuwa ƙasashen waje ta wannan hanya tun bayan fara yaƙin.
Babban jami'in gudanarwa na Aramco, Amin Al-Nasser, ya ce bayan sanar da sakamakon kuɗaɗen kamfanin, yawan tashoshin fitar da mai daban-daban da kuma jigilar mai ta bututun zuwa tashar Yanbu sun bai wa Aramco damar ci gaba da ayyukanta.
Ya ƙara da cewa kamfanin ya ci gaba da gudanar da ayyukansa.
"Duk da mafi girman tangardar da aka taɓa samu ga samar da mai ta mashigar Hormuz," in ji shi.
Rarraba kadarori da kamfanin ya yi zuwa fannoni daban-daban da kuma tsare-tsaren da ya shafe shekaru da dama yana aiwatarwa sun taimaka masa wajen cimma wannan buri.
Sai dai bututun ba shi da ƙarfin ɗaukar dukkan man da Saudiyya ke fitarwa daga yankin Tekun Fasha kafin fara yaƙin.
Haka kuma, wani ɓangare na ƙarfin bututun ana amfani da shi ne wajen samar da mai ga matatun mai da ke yammacin Saudiyya.