Ko zan rasa raina sai na yaƙi zalunci - Pantami

Yayin da ake ci gaba da samun turjiya daga wasu daga cikin yan jam'iyyar APC da ke neman jam'iyyar ta basu damar tsayawa takarar gwamana a wasu daga cikin jihohin ƙasar, a jihar Gombe lamarin na ci gaba da daukar hankula, musamman tun bayan da gwamnan jihar Muhammad Inuwa ya bayana Dr jamilu Gwamna a matsayin wanda zai gajishi a mastyin gwaman.
Tsohon Ministan Sadarwar Najeriya kana mai neman tsayawa takarar gwamna a jihar Gombe a jam'iyyar APC, Farfesa Isa Ali Pantami, ya sha alwashin daukar duk wani mataki da ke bisa doka wajen kalubalantar yadda aka fitar dan takarar gwamnan jihar na zaben badi, da ya ce ya saba wa ka'ida.
Hakan dai ya biyo bayan da farfesa Pantamin ya mayar da fom ɗinsa na neman takarar gwamnan jihar Gombe a hedikwatar jam'iyyar APC mai mulki da ke Abuja, duk da bayyana Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna a matsayin dan takarar gwamnan jam'iyyar na maslaha, da gwamnan Gomben ya yi.
Ya ce matakin wanda Gwamna Muhammad Inuwa ya jagoranta, ya saɓa wa doka da ƙa'ida, kuma tsagwaron rashin adalci ne, don haka tuni ya samu ƙwarin gwiwa daga Shugaba Bola Tinubu da Shugaban APC Farfesa Nentawe Yilwetda da suka nuna cewa a je a tabbatar da ba a yi kama-karya ba.
Farfesa Ali Isa Pantamin dai ya ce 'idan aka yi adalci a matakin adalci duk wanda ya samu namu ne, amma idan aka yi zalunci har ga Allah za mu ya ƙe zalunci. Abun da na ke faɗa ba fa da baki ba ne, za ka ga yaƙi da zalunci da baka taɓa gani ba irin sa ba a Najeriya,' In ji Fantamin.
Haka kuma ya ce za su yaƙi zalunci ne ta matakan da dokokin najeriya suka tanada, wanda kuma ita ce hanyar da zaa kawo sauyi a tsarin yadda alamura ke tafiya a ƙasar.
Farfesa Pantamin ya jadada cewar akwai wasu daga cikin dattawa a jihar ta Gombe da suka fara tuntuɓarsu don ganin an shawo kan lamarin.
"Idan na adalci ne ƴar tinƙen da aka shirya gudanarwa to albishirinmu jam'iiyar mu za ta yi nasara, idan na zalunci ne hatsari ya afku domin kowa zai rasa, lamarin zai lalace don Allah bai taba goyan bayan zalunci ba. kuma zalunci nan ko ni aka baiwa allah ba zai bar zalunci ba," In ji Farfesa Pantami.
Farfesa Ali Isa Pantamin ya mayar da maratani kan ba tunda wasu ke cewar a matsayin sa na malamin addini, ya kamata a ce ya bi zaɓin da gwamnan na sa ya yi, tare da mara masa baya don ganin an kai ga ci da masalahar al'umma.
"Shiru da ake yi akan zalunci yana ɗaya daga cikin dalilan da suka lalata ƙasar mu, yanzu misali inda komai a Najeirya ya na tafiya dai dai wa daidai, a arewacin Najeriya babu wata mastala ko kaɗan, kuma ba na faɗa da kowa musamman shi wanda aka zaɓa amma ba na goyan bayan zalunci ko kaɗan," in ji tsohon minsitan sadarwar na Najeriya.
Ko Fantami zai Sauya sheƙa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Farfesa Pantami ya shaidawa BBC cewar har yanzu shi dan jam'iyyar APC ne, amma akwai wasu matakai uku da suka ɗauka kan matakan da za su ɗauka na gaba sai dai lokaci da za mu futo su bayyana matakan bai yi ba.
''Sau ɗaya aka taɓa zama da mu, aka tara mu cewa wani tsari mu ka ɗauka, sai gwamna Muhammed Inuwa Yahaya ya ce ya yi alƙawarin zai yi adalci in zai yiwu a yi amfani da tsarin maslaha''
''Na biyu in bai yiwu ba sai ayi zaɓen ƴar tinke kuma a tsarin masalaha sai aka ce a je a fitar da ƙa'idojin da za a bi kuma ba bu wanda ya ga ƙa'idojin a cikinmu''
''Idan za ka yi consensus sai a nemi kwamiti mai zaman kansa wanda ba su da wani karkata ga wani ɗan takara sai a basu wuka da nama''
Dr Pantami ya kuma ce akwai waɗanda aka aika wa goron gayyata yayin da akwai wasu da ba a gayyacesu ba
''An ba mu notice ɗan takaitacce ne, na ƙasa da awa 20, a lokacin da mu ka gani mun kama hanyar tafiya, tafiyar ba ta yiwu ba, ga saƙo a rubuce cewa in dai zaman da za a yi, ci gaba ne na zaman da aka fara ƙwaya ɗaya da aka yi na consensus mu na roƙon a ƙara mana lokaci don nu halarci zaman mu tabbatar an yi''
Duk da irin tasirin da wasu ke yi na irin tasirin kalaman farfesa Ali Isa Fantamin a Najeriya kasnacewar sa ɗaya daga cikin manyan malaman da ke bayar da karatu a Najeriya, an jiyo Pantamin na cewar jam'iyyar ta su ta ɗauko hanyoyin adalci da rashin sa, ba wai a iya gombe ba a Najeriya baki daya.
"Akwai wurare da yawa da aka dauki hanyoyin adalci akwai wadan da kuma an yi zalunci, dukkan bangarorin akwai, don shi ne magana ta gaskiya." a cewar Farfesa Pantami.
Sannan kuma Farfesa Pantami ya shaidawa BBC cewa a shirye yake ya tunkari zaɓen fitar gwanin ta hanyar ƴar tinke.











