Tottenham na son Gakpo, Forest na harin Reijnders

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan tsakiya na Manchester City da Netherlands Tijjani Reijnders, mai shekara 28, shi ne danwasan da Nottingham Forest ke neman lale fam miliyan 55 domin ɗauko shi. (Mail, external)
An yi wa Tottenham tayin ɗanwasan gaba na Amurka Folarin Balogun, mai shekara 25, yayin da tsohon ɗanwasan na Arsenal ke fuskantar rashin tabbas a Monaco. (Sun, external)
Spurs na tattaunawa da Manchester City kan ɗanwasan gaba na Brazil Savinho, mai shekara 22, yayin da kuma take son ɗanwasan gaba na Liverpool da Netherlands Cody Gakpo, mai shekara 27 da ɗanwasan tsakiya na Eintracht Frankfurt Jean-Matteo Bahoya, mai shekara 21. (Athletic - subscription required, external)
Idan har Savinho ya amince ya koma Tottenham, Manchester City za ta shiga farautar ɗanwasan Chelsea da Portugal Pedro Neto wanda tuni ta fara tuntuɓar ɗanwasan mai shekara 26. (Fabrizio Romano, external)
Real Madrid na shirin farfaɗo da tattaunawa da wakilan Vinicius Jr a wannan makon amma ƙungiyar ba ta ta niyyar yin ƙari daga tayin da ta yi wa ɗanwasan na Brazil wanda Arsenal ke farauta. (ESPN, external)
Chelsea na dab da cimma yarjejeniya da Rayo Vallecano kan ɗanwasan baya na Spain mai shekara 28 Pep Chavarria. (Athletic - subscription required, external)
Tottenham na son ɗanwasan gaba na Chelsea Nicolas Jackson amma ba ta taya ɗanwasan na Senegal ba mai shekara 25 wanda Chelsea ta saka wa kudi fam miliyan 65. (Mail, external)
Chelsea na tunanin ɗauko golan Porto da Portugal Diogo Costa, wanda ake alakantawa da Manchester United. (Mirror, external)
Manchester City ta taya golan Marseille da Argentina Geronimo Rulli, mai shekara 34, yayin da ƙungiyoyin biyu ke shirin soma tattaunawa. (Fabrizio Romano, external)
Manchester United na kallon ɗanwasan tsakiya na Nottingham Forest da Ingila Morgan Gibbs-White, mai shekara 26, a matsayin wanda ya fi dacewa ya maye gurbin Bruno Fernandes idan har ɗanwasan na Portugal ya bar Old Trafford. (Mail - subscription required, external)
Manchester United da Chelsea na hamayya kan ɗanwasan Bologna da Colombia Jhon Lucumi, wanda ake alakantawa da ƙungiyoyin Seria A Juventus da Como. (Quotidiano Sportivo - in Italian, external)
Tsohon ɗanwasan gaba na Manchester United Jadon Sancho, mai shekara 26, ya tattauna da wasu manyan ƙungiyoyi a Turai da Saudiyya da Gabas Ta Tsakiya yayin da yake nazari kan zaɓin da ya fi masa. (Sky Sports, external)











