Ina Tinubu yake kuma yaushe zai koma Najeriya?

Bola Tinubu
    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shafe kusan wata guda a wajen ƙasar, tun bayan tafiyarsa zuwa Turai a ranar 30 ga Agusta 2026 domin "hutun aiki" na makonni uku. Sai dai bayan wa'adin hutun ya kusa ƙarewa, fadar shugaban ƙasar ta sanar da cewa ya ƙara wasu kwanaki a hutun da yake yi.

A sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga, ya fitar a ranar 21 ga Satumba, ya ce Tinubu zai koma Najeriya a ƙarshen mako. Sai dai hakan bai tabbata ba domin har yanzu bai dawo ba.

Tinubu ya fara hutunsa ne a Birtaniya, daga nan kuma ya wuce Faransa, inda ya gana da shugaba Emmanuel Macron. A cewar fadar shugaban ƙasar, Tinubu na ci gaba da sa ido kan harkokin gwamnati daga ƙasashen waje, yayin da mataimakinsa, Kashim Shettima, ya wakilce shi a wasu ayyukan.

Fadar shugaban ƙasar ta ce an tsawaita zaman shugaban a ƙasashen waje, lamarin da ya jawo muhawara, musamman saboda Shettima shi ma ya bar Najeriya domin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, inda ake ta tambayoyi kan wane ne ke shugabancin ƙasar.

Masu suka na ganin Tinubu ya wuce wa'adin da ya kamata ya tafi hutu ba tare da miƙa mulki ga mataimakinsa ba.

A baya-bayan nan Bayo Onanuga ya fitar da sanarwar cewa duk da shugaban ba ya Najeriya yana cikin ƙoshin lafiya sannan kuma yana iya gudanar da shugabancin ƙasa.

Abin da wasu ke ta tambaya shi ne yaushe zai koma ƙasar, ganin yadda ake ta ɗage daowwarsa, sannan ya matsayin abin da ya yi a dokar ƙasa?

Me kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce idan shugaban ƙasa zai yi tafiya?

Wannan batu na na ci gaba da zaman Shugaba Bola Tinubu a ƙasashen waje, batu da ake ta tafka muhawara a kai.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sashe na 145 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce: "Duk lokacin da shugaban ƙasa zai tafi hutu ko kuma ya kasa gudanar da ayyukan ofishinsa saboda wani dalili, dole ne ya aika da sanarwa a rubuce ga shugaban majalisar dattawa da kuma kakakin majalisar wakilai kan hakan."

"Dokar ta ce mataimakin shugaban ƙasa ne zai ci gaba da gudanar da ayyukan shugaban ƙasa a matsayin muƙaddashi, har sai lokacin da shugaban ya dawo."

Ƙaramin sashe na biyu ya ce idan shugaban ƙasa ya kasa ko ya ƙi aika da sanarwar a cikin kwanaki 21, majalisar dokoki ta ƙasa za ta iya zartar da ƙuduri da rinjayen ƙuri'un mambobin ɗaya daga cikin majalisun biyu, domin bai wa mataimakin shugaban ƙasa umarnin gudanar da ayyukan shugaban ƙasa a matsayin muƙaddashi.

Haka za a ci gaba har sai shugaban ƙasar ya aika da wasiƙa ga shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai, ya sanar da su cewa ya dawo kuma a shirye yake ya ci gaba da gudanar da ayyukansa.

A yanzu dai ba a bayyana a hukumance ko Tinubu ya aika da wannan takarda ba. Wannan ya sa ake ɗiga ayar tambaya kan hurumin abin da Tinubun ya aikata.

Ina Tinubu yake, kuma yaushe zai dawo?

Bola Tinubu a Faransa

Mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga, wanda ya sanar a farko cewa Tinubu zai koma ƙasar cikin ƙarshen mako, ya sake fitar da wata sanarwa a ranar 27 ga Satumba, inda ya ce an sake sauya ranar dawowarsa bayan wani sauyin da aka samu.

Ya ce ana sa ran zai dawo cikin makon nan, ko da yake bai tabbatar da ranar a hukumance ba. Amma wasu rahotanni da kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ce wataƙila ya koma ƙasar a ranar Talata ko Laraba.

Onanuga, ya sanar a ranar 27 ga Satumba cewa Tinubu na cikin ƙoshin lafiya, kuma zai dawo domin halartar bukukuwan cika shekaru 66 da samun 'yancin kan Najeriya.

Saboda haka, ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya kafin bikin ranar 'yancin kai a ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, kuma zai halarci bikin ƙaddamar da wani fim a Legas da aka shirya domin tunawa da marigayi MKO Abiola.

Ganin da aka yi wa Tinubu na ƙarshe shi ne a birnin Paris na Faransa, inda ya gana da shugaban ƙasar, Emmanuel Macron, da ɗan kasuwa Vincent Bolloré. A cewar Onanuga, shugaban ya ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati daga ƙasashen waje, ciki har da ganawa da masu zuba jari.

Daga cikin ayyukan da fadar shugaban ƙasar ta ambata a matsayin misalin ci gaba da aikinsa yayin hutun, Onanuga ya ce Tinubu ya taimaka wajen samar da aikin gina tashar jiragen ruwa a Ogun da gwamnatin jihar ta ƙaddamar, wanda aka kiyasta zai lakume dala biliyan bakwai.

A sanarwar, Onanuga ya ce a wannan zamani na kimiyya da fasaha, ba lallai ne sai shugaban ƙasa ya kasance a Abuja a zahiri domin gudanar da ayyukansa ba.

Abin da ƴan Najeriya ke cewa

Tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cewa zai tafi hutu, aka fara tambayoyi kan ko ya miƙa wa mataimakinsa, Kashim Shettima, ikon gudanar da ayyukan shugaban ƙasa a lokacin da ba ya nan.

Batun ya ƙara ɗaukar hankali bayan da fadar shugaban ƙasa ta sanar da cewa Tinubu ya ƙara wasu kwanaki a hutunsa.

Ƴan siyasa musamman ƴan adawa, na zargin Shugaba Tinubu da karya kundin tsarin mulki. Amma masu magana da yawun shugaban ƙasa, irin su Bayo Onanuga da Daniel Bwala, sun dage cewa bai karya wata doka ba.

Daga cikin waɗanda suka soki matakin Tinubun akwai tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya tambayi ko wane ne ke gudanar da ayyukan shugaban ƙasa yayin da Tinubu da Shettima suke wajen Najeriya.

Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, ya kuma ce lokacin da shugaban ƙasar da mataimakinsa suke ƙasashen waje, Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro da tsadar rayuwa.

Shi ma Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, ya tambayi inda shugaban Najeriya yake, yana mai cewa ya kamata shugaban ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan al'umma a Afirka ya wakilci ƙasar a manyan tarukan ƙasa da ƙasa.

Jam'iyyar ADC ma ta buƙaci fadar shugaban ƙasa da majalisar dokoki ta ƙasa su fayyace wanda ke gudanar da ayyukan shugaban ƙasa a lokacin da Tinubu da Shettima suke ƙasashen waje.

Ita ma jam'iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki ya soki tsawaita hutun Tinubu inda ta ce ƙasa bai kamata ya tafi hutu a lokacin da Najeriya ke fuskantar matsalolin tsaro da tattalin arziki da kuma ƙarin wahalhalun rayuwa ba.