United da Liverpool na harin Mitchell, Munich na son Gibbs-White

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Crystal Palace Tyrick Mitchell, na ci gaba da ɗaukar hankalin Manchester United da Liverpool. (Teamtalk)
Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da ke buga La Liga na sa ido kan ɗan wasan Aston Vila Alejandro Garnacho, bayan ƙoƙarin da ya yi a Villa Park, a matsayin ɗan wasan aro daga Chelsea.(Mail plus - subscription required)
Liverpool za ta sake naɗa Julian Ward a matsayin daraktan wasanni. Zai dai koma kan muƙamin ne daga mukamnin da ya ke riƙe a Fenway sporting na techinical darakta don maye gurbin Richard Hughes a kakar 2022-2023. (The Athletic)
Bayern Munich na harin ɗan wasan Nottingham Forest Morgan Gibbs-White, 26. (Talksport)
Arsenal za ta yi amfnai da hutun watan Satumbar nan, don tsayar da matsaya kan ɗan wasan Ingila Declan Rice. (Football Transfers)
Arsenla dai ba ta da wani zaɓi illa ta tsawaita zaman Rice ɗin da watannni 12, sai dai ta na son ya ci gaba da kiyaye manufar ƙungiyar ke da shi ga ɗan wasa da ake ganin na da mahimmanci ga mai horar da ƴan wasan na Arsenal Mikel Arteta. (Guardian)
Liverpool ta yi tsayuwar daka kan ɗauko ɗan wasan Jamus Florian Wirtz, duk da cewar wakilan ƴan wasan na tattunawa da Bayern Munich. (Teamtalk)
Chelsea na sa ido kan ɗan wasan Gambia Adama Jeng, yayin da Bayern Munich, da Benfica, da Sporting da Paris FC su ma ke zawarcin ɗan wasan Samger FC.(Mail plus - subscription required)
AC Milan da Roma sun dage wajen ɗaukar ɗan wasa Endrick a matsayin aro daga Real Madrid idan shugaban ƙungiyarlorentino Perez na son ɗan wasan dan ƙsar Brazil ya bar ƙungiyar. (Calciomercato - in Italian)
Barcelona na sa ido kan ɗan wasan Athletico Paranaense Arthur Dias, da a baya Tottenham nuna sha'awa mai ƙarfi wajen ɗaukarsa. (ESPN Brasil - in Portuguese)
Arsenal ta kusa kamalla cinikin ɗan wasan Brazil Vinicius Jr daga Real Madrid a kakkar wasanin nan, wani yunƙuri da abokan taka ledar ɗan wasan suka ɗauka ya fasa komawa Arsenal. (Cadena SER - in Spanish)


























