Tsaron Putin: Sirrin matakan kariyar shugaban Rasha

Asalin hoton, getty
Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ziyarci Indiya domin halartar taron koli na ƙasashen BRICS karo na 18, wanda aka gudanar a cibiyar taro ta Bharat Mandapam da ke New Delhi a ranakun 12 da 13 ga Satumba.
Wannan ita ce ziyarar Putin ta biyu a Indiya tun watan Disambar bara, lokacin da ya kai ziyara ta musamman domin tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu, bayan shafe shekaru huɗu bai ziyarci ƙasar ba.
A yayin ziyarar, Putin ya gudanar da tattaunawar ƙasashen biyu da Firaministan Indiya, Narendra Modi, inda suka tattauna batutuwa daban-daban da suka shafi dangantaka tsakanin Rasha da Indiya.
Kakakin fadar Kremlin, Dmitry Peskov, ya ce kafin ziyarar cewa shugabannin biyu za su tattauna wasu batutuwa a ɓoye, saboda abin da ya ce ƙoƙarin wasu ƙasashe ne na kawo cikas ga haɗin gwiwa tsakanin Rasha da Indiya.
Peskov ya ce: "Ba za a iya tattauna wasu batutuwa a bainar jama'a ba saboda akwai ƙasashen da ke ƙoƙarin kawo cikas ga bunƙasar haɗin gwiwa tsakanin Rasha da Indiya. Saboda haka, ana tattauna waɗannan batutuwa cikin sirri, amma cikin ingantacciyar hanya mai amfani."
Ɗaruruwan masu kula da motsi na Putin
Putin wanda ya ke da shekara 73, ya daɗe akan mulki tun daga 2000, abin da ya sa ya zama shugaban Rasha mafi daɗewa a fadar Kremlin baya ga Joseph Stalin. A yanzu yana gudanar da wa'adinsa karo na biyar kenan a matsayin shugaban ƙasa.
'Yan adawa a Rasha ba su da ƙarfin jayayya da shi, kuma idan yana buƙatar ci gaba da mulkin ƙasar zai iya har zuwa shekarar 2036.

Asalin hoton, getty
Dangane da tsaronsa, ɗaruruwan jami'an tsaro na sa ido sosai kan duk wani motsinsa, kuma suna tare da shi sa'o'i 24 a rana.
A cewar wani rahoton BBC, ana shirya abincin Putin cikin tsananin sirri, yayin da mashayinsa da duk abin da zai sha ake bincikawa sosai a ƙarƙashin kulawar manyan masu ba shi shawara.
Putin, wanda ya taɓa aiki a hukumar leƙen asiri ta KGB, ya san irin haɗarin da ke tattare da matsayinsa sosai.
Wane ne ke bai wa Putin tsaro?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daga cikin hukumomin tsaron Rasha akwai wata hukuma ta musamman da ke da alhakin kare shugaban ƙasar da iyalinsa, wato Hukumar Tsaron Shugaban Ƙasa ta Rasha (SBP).
Hukumar tana ƙarƙashin Hukumar Samar da Tsaro ta (FSO) ta Rasha, wadda aka kafa daga tsohuwar hukumar leƙen asiri ta KGB.
Jami'an SBP, waɗanda ke sanye da baƙaƙen kaya kuma ɗauke da na'urorin sadarwa, suna tare da Putin dare da rana kamar inuwa.
A cewar kafar yaɗa labarai mallakar gwamnatin Rasha ta Russia Beyond, jami'an tsaron da ke raka Putin a tafiye-tafiyensa zuwa ƙasashen waje ana rarraba su zuwa rukuni huɗu.
"Layin farko na tsaro shi ne masu gadinsa na musamman."
"Layi na biyu kuma shi ne jami'an tsaron da jama'a ba sa iya gane su cikin sauƙi."
"Layi na uku ana kafa shi ne a kewayen taron jama'a domin hana mutanen da ake zargi da aikata wani abu kusantar shugaban."
"Layi na huɗu, wanda shi ne mafi nisa, ya ƙunshi maharba da ake girke su a saman gine-ginen da ke kewaye da wurin da shugaban yake."

Asalin hoton, getty
Mark Galeotti, wani masani kan harkokin tsaron Rasha kuma darektan kamfanin Mayak Intelligence, wanda ke nazarin batutuwan tsaro a ƙasar, ya ce Putin ba ya son yin tafiye-tafiye da jirgin helikwafta.
Ya ce yawanci yana tafiya ne cikin jerin motocin ayari mai yawa, wanda ya ƙunshi babura, manyan motocin baƙaƙe da kuma wasu motoci masu tsauraran matakan tsaro.
A yayin tafiye-tafiyensa, galibi ana hana jirage marasa matuƙa, wato drones, shawagi a sararin samaniyar yankin, sannan a dakatar da zirga-zirgar sauran ababen hawa.
Rundunar 'musamman' da ke kare shugaban ƙasa
Hukumar Tsaron Shugaban Ƙasa ta Rasha (SBP) tana samun tallafi daga Rundunar Tsaron Ƙasa ta Rasha (Rosgvardiya). Wasu mutane na kiran wannan runduna da "rundunar musamman ta shugaban ƙasa."
Rundunar ba ta cikin Rundunar Sojin Rasha. A hukumance, ayyukanta sun haɗa da kare iyakokin ƙasar, yaƙi da ta'addanci da kuma tabbatar da doka da oda.
Sai dai a aikace, ana cewa ɗaya daga cikin muhimman ayyukanta shi ne kare Putin daga barazana iri-iri.
Stephen Hall, wani masani kan Rasha a Jami'ar Bath da ke Birtaniya, ya ce sanannen abu ne cewa Rundunar Tsaron Ƙasa ta Rasha tana taka muhimmiyar rawa wajen kare Putin, wanda ke cikin wani yanayi na tsauraran matakan tsaro tare da sauran hukumomin tsaron ƙasar.

Asalin hoton, getty
A cikin 'yan shekarun nan, an ƙara yawan jami'an da ke cikin wannan runduna zuwa 400,000.
Hall ya ce wannan adadi ne mai matuƙar yawa, yana mai cewa hatta yawan jami'an tsaron da ke cikin tsarin tsaron shugaban Amurka bai kai wannan adadi ba.
Yadda ake kula da tsaron Putin
Yana da wahala a san dalla-dalla yadda ake aiwatar da matakan tsaron Putin da kuma irin girman matakan da ake ɗauka. Sai dai fadar Kremlin da wasu ƙwararrun harkokin tsaron Rasha sun bayyana wasu bayanai.
A tsarin tsaron Putin, ana ɗaukar matakan kariya mafi tsauri musamman dangane da abincinsa da abin da yake sha.
Galeotti ya ce saboda fargabar yiwuwar sanya masa guba, Putin yana da wani mutum na musamman da ke ɗanɗana abincinsa kafin ya ci, domin tabbatar da cewa abincin ba shi da wata illa.
Ya shaida wa BBC Mundo cewa: "Tsarin ya fi kama da na wani sarki a zamanin da, fiye da na shugaban ƙasa a wannan zamani."

Asalin hoton, getty
Bugu da ƙari, idan Putin ya yi tafiya zuwa wajen Rasha, jami'an tsaronsa suna bincika duk wani abu da zai yi amfani da shi.
Galeotti ya ce: "Duk abin da yake ci ko sha, tawagarsa ce ke kawo masa. Misali, a tarukan hukuma inda ake ba da giya, Putin yana shan wadda tawagarsa ta kawo ne kawai, ba daga wata kwalba dabam ba."
Haramta amfani da wayoyin zamani a fadar shugaban ƙasa
Wani muhimmin mataki a tsarin tsaron Putin shi ne hana amfani da wayoyin zamani a cikin fadar Kremlin.
Putin da kansa ya taɓa cewa ba ya amfani da wayar salula. Ya bayyana hakan ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Rasha, TASS, a shekarar 2020.
Ya ce yana da wata layin waya ta musamman ta aiki, wadda za a iya amfani da ita wajen tuntubarsa idan akwai wanda ke buƙatar yin magana da shi.
Masu ba shi shawara sun tabbatar da hakan. Kakakin Kremlin, Dmitry Peskov, ya sha maimaita cewa Putin ba ya amfani da wayar salula saboda ba shi da lokacin yin hakan.
Sai dai an kuma bayar da wani dalili cewa Putin ba ya amincewa da intanet.
A wani lokaci, ya yi ishara da intanet a matsayin CIA, wato hukumar leƙen asirin Amurka.

Asalin hoton, getty
Ya kuma taɓa roƙon 'yan ƙasar Rasha da su guji binciken bayanai a Google, saboda yana ganin cewa Amurka ce ke tattara duk bayanan da ake samu ta hanyar sa.
Galeotti ya ce Putin ba ya yawan amfani da intanet. An san shi da ƙin amfani da wayoyi, sannan yana mai da hankali sosai kan tsaro, domin a ganinsa wayoyin zamani ba su da isasshen tsaro.
A cewar masana, Putin yana karɓar bayanai a cikin takardun rahotanni, sannan ya gabatar da su ga masu ba shi shawara.
Hall ya ce Putin yana fara ranarsa ne da takaitattun bayanan tsaro guda uku. Na farko ya shafi halin da duniya ke ciki, na biyu ya shafi abubuwan da ke faruwa a cikin Rasha, yayin da na uku ya shafi abubuwan da ke faruwa a matakin ƙoli na shugabancin ƙasar.
Ya ce bayanan da aka gabatar masa su ne mafi muhimmanci a gare shi, kuma su ne ke taimaka masa wajen yanke shawarar matakan da zai ɗauka a wannan rana.
Hall ya ƙara da cewa ya taɓa tattaunawa da jami'an diflomasiyya da kuma wasu jami'an Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, waɗanda suka shaida masa cewa a wasu lokuta idan sun gabatar da bayanan da hukumomin leƙen asirinsu suka ɗauka a matsayin ba daidai ba, Putin yakan yarda da bayanan da jami'an leƙen asirinsa suka kawo masa, maimakon bayanan jami'an diflomasiyyar.



























