Me rashin zuwan Tinubu babban taron MDD a Amurka ke nufi?

Tinubu ya je taron UNGA a shekarar 2023 amma bai sake zuwa Amurka ba, inda bai halarci zaman a shekarun 2024, 2025 da 2026 ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tinubu ya je taron UNGA a shekarar 2023 amma bai sake zuwa Amurka ba, inda bai halarci zaman a shekarun 2024, 2025 da 2026 ba
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

A ƙarshen makon nan ne mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya sanar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya umurce shi ya jagoranci tawagar ƙasar zuwa taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) karo na 81 da zai gudana a birnin New York na Amurka.

An shirya gudanar da muhawarar babban taron na UNGA daga ranar 22 zuwa 28 ga Satumban 2026.

Rashin halartar shugaban ya haifar da muhawara tsakanin ƴan adawa a ƙasar da masana kan dalilin da ya sa Tinubu bai halarci babban taron ba, karo na uku a jere.

Tun da Tinubu ya je taron a shekarar 2023 bai sake halarta ba. Shugaban bai halarci zaman a shekarun 2024, 2025 da 2026 ba, inda a kowanne lokaci yake tura mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilce shi.

Wasu na ganin rashin halartar taron sau uku a jere abu ne da ya saɓa ƙa'ida, kuma hakan na iya yin tasiri ga hulɗar Najeriya da ƙasashen duniya.

Ana ganin cewa taron UNGA na ɗaya daga cikin muhimman wuraren da shugabannin ƙasashe ke tattauna batutuwan tsaro, kasuwanci da ci gaba tare da neman jari da haɗin gwiwa da sauran ƙasashe.

Tuni dai ƴan adawa suka fara suka da zargin Tinubu kan rashin halartar taron.

A wata sanarwa da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya fitar, ya yi zargin cewa wataƙila ko tsohuwar shari'ar "ƙwace kadarori" da gwamnatin Amurka ta taɓa gudanarwa kan "wasu kuɗaɗe da ake dangantawa da Tinubu a shekarun 1990 ne," dalilin da ke sanya shugaban ƙasar gujewa ƙasar Amurka".

Sai dai tuni fadar shugaban ƙasar ta yi watsi da wannan zargi.

Me ya hana Tinubu zuwa taron?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Fadar shugaban ƙasa ta ce Shugaba Bola Tinubu ba zai halarci taron UNGA karo na 81 da kansa ba ne saboda yana hutunsa na shekara a ƙasar Faransa.

Jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce rashin halartar shugaban ba yana nufin Najeriya ba ta da wakilci a taron ba, domin tawagar ƙasar za ta ci gaba da shiga dukkan zaman da za a gudanar.

Shi ma babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin ƙasashen waje, Ademola Osodi, ya ce rashin zuwan Tinubu taron ba zai rage tasirin Najeriya a harkokin diflomasiyya ko shugabancinta a nahiyar Afirka ba.

Da yake magana a shirin Sunday Politics na tashar Channels TV, Osodi ya ce shugaban na mayar da hankali kan muhimman batutuwan cikin gida ne, musamman tattalin arziki da tsaro.

Ya ƙara da cewa Najeriya na ci gaba da hulɗa da ƙasashen duniya ta wasu hanyoyin, ba sai ta Majalisar Ɗinkin Duniya kaɗai ba.

"Akwai muhimman batutuwan da suka shafi tattalin arziki da tsaro da shugaban ke mayar da hankali a kansu a gida," in ji Osodi.

Ya kuma ce kasancewar Tinubu ko rashinsa a taron ba zai sauya matsayin Najeriya a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙasashen Afirka ba.

Me rashin halartar Tinubu ke nufi ga Najeriya?

Masana harkokin Diplomasiyya a Najeriya sun fara tsokaci kan damarmakin da ƙasar ke rasawa saboda rashin zuwan shugaba Bola Tinubu babban taron majalisar Dinkin Duniya karo na uku a jere.

Masana na ganin hakan zai iya hana Najeriya wasu damarmaki musamman wajen ganawa da shugabannin ƙasashe domin inganta alaƙa.

Ambasada Aminu Iyawa, tsohon jakadan Najeriya ne a ƙasar Mexico, ya ce duk shugaban da ya san mahimmancin halartar wannan taron ba zai ƙi zuwa da kansa ba sai idan akwai ƙwaƙƙwaran dalili.

"Yawancin mutane sun ɗauka cewa waɗannan jawaban da shugabannin ƙasa ke yi a wajen taron shi ne mafi muhimmanci, a'a ba haka ne ba,".

Ya ce akwai ganawar da shugabannin ke yi a gefen taron, wanda shi ne ya fi amfani ga duk wata ƙasa da ke da wata buƙata musamman ma ƙasashe masu tasowa irin Najeriya.

Masanin ya ce "Najeriya ta yi asara sosai" saboda rashin halartar Shugaba Tinubu a taruka uku da suka gabata. A cewarsa shugabanni sun fi son ganawa da takwarorinsu domin yanke hukunci da ɗaukar mataki nan take wanda wakilci ba zai iya yi ba.

'Damarmakin da Najeriya ke rasawa'

Ambasada Iyawa ya ce Najeriya za ta iya amfani da wannan damar wajen neman sassaucin basussukan da ake bin ta daga Bankin Duniya da IMF, wanda shugabannin da suka ci gaba irin su Amurka, India, Faransa da China ke da ruwa da tsaki.

Ya ce ba lallai a kalli buƙatun da mataimakin shugaban zai gabatar ba, amma in da Tinubu ya je zai iya neman a yafe wasu basukan ko a rage su.

"Ai duk wani shugaba da yake son ƙasarsa ta ci gaba, zai je,... wataƙila shi shugaba Tinubu bai ɗauki wannan taro da muhimmanci ba," in ji shi.

Baya ga batun yafe basussuka da Najeriya za ta iya neman sassauci a kai, akwai batun da Ambasada Iyawa ya ce babbar dama ce ga Najeriya.

Ya ce sakamakon yadda ƙasar kullum take neman masu zuba jari su shiga ƙasar a fannonin harkar mai, zinare da wasu ma'adanan ƙasa, ba lallai ta iya jan hankalin duniya ba idan shugabanta ba ya irin wannan waje da kansa.

"Idan ba shi ya yi magana da su ba, babu wani tasiri da abin zai yi... Idan kana so ƙasar ka ta ci gaba, ta samu daraja, ka yi magana a ji, sai in ga ka ga su," in ji Ambasada Iyawa.

Tuni dai mataimakin shugaban Najeriyar Kashim Shettima ya isa birnin New York a daren ranar Lahadi, inda ake sa ran ƙasar za ta gabatar da jawabinta a ranar Alhamis a taron na UNGA.

Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya

Bayanan hoto, Mataimakin shugaban Najeriyar Kashim Shettima ya isa birnin New York a daren ranar Lahadi, inda ake sa ran ƙasar za ta gabatar da jawabinta a ranar Alhamis a taron na UNGA

'Babu wanda ya hana Tinubu zuwa Amurka'

Fadar Shugaban Ƙasar ta yi watsi da zargin cewa rashin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) da Shugaba Bola Tinubu ya yi karo na uku a jere na da alaƙa da wani takunkumi da aka sanya masa kan tafiyarsa zuwa Amurka.

Ademola Osodi, ya ce irin wannan zargi, batu ne na siyasa kawai, yana mai cewa: "Babu wata matsala ko takunkumi ko kaɗan."

Osodi ya ce ya taɓa raka Tinubu zuwa Amurka lokacin taron Majalisar Ɗinkin Duniya na shekarar 2023, sannan ya tuna wata tafiya da suka yi ta birnin Los Angeles kafin su wuce Yokohama a Japan.

A cewarsa, waɗannan tafiye-tafiye sun nuna cewa shugaban ƙasar na iya shiga Amurka ba tare da wata matsala ba.

"Mun je Amurka kuma ina tare da shi. Wannan magana siyasa ce kawai, ana maimaita ta ne kawai saboda muna lokacin zaɓe," in ji Osodi.

Tuni dai mataimakin shugaban Najeriyar Kashim Shettima ya isa birnin New York a daren ranar Lahadi, inda ake sa ran ƙasar za ta gabatar da jawabinta a ranar Alhamis a taron na UNGA.

Shin ya matsayin Najeriya a taron?

Jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce Najeriya za ta ci gaba da riƙe kujerarta ta musamman da kuma matsayinta a babban zauren na UNGA, duk da cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne zai wakilci Shugaba Tinubu.

A wata sanarwa da ofishin jakadancin Najeriya a New York ya fitar, Ibrahim ya ce fiye da kashi 60 na ƙasashen da za su yi jawabi a taron na bana sun tura wakilcin mataimakansu ne ko ministocin harkokin wajensu.

Ya ce babu wani sabon abu a cikin matakin da ƙasashe ke ɗauka na tura manyan jami'ai su wakilci shugabanninsu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

Jakadan ya ƙara da cewa Shettima tare da Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, za su shiga dukkan muhimman taruka da ganawa na diflomasiyya da ke gudana a taron.

"Mataimakin shugaban ƙasa da ministar harkokin wajen suna da cikakken ikon wakiltar Najeriya da kare muradunta a taron."