Wane mataki Najeriya ke ciki wajen aiwatar da kasafin kuɗin 2026?

...

Asalin hoton, PRESIDENCY

    • Marubuci, Bashir Zubairu Ahmad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC News Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wata Cibiyar da ke Neman Tabbatar da Adalcin Ga Jama'a (CSJ) ta buƙaci Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fara aiwatar da kasafin kuɗin manyan ayyuka na shekarar 2026 nan take, tana mai gargaɗin cewa ci gaba da jinkirta hakan ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulki da dokar kula da kuɗaɗen Jama'a da kuma dokar kasafin kuɗi.

Ƙungiyar ta kuma aika wa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Tajudeen Abbas kwafin wasiƙar, wadda a cikinta CSJ ta buƙaci ministan kuɗi ya fito fili ya bayyana dalilin da ya sa ake ci gaba da samun jinkiri wajen sakin kuɗaɗen gudanar da ayyukan raya ƙasa, tana mai kafa hujja da sashe na 48 (1) na dokar kula da kuɗaɗen jama'a, wanda ke buƙatar a gudanar da harkokin kuɗin gwamnati cikin gaskiya da kuma bayyana bayanai cikin lokaci.

Cibiyar ta kuma buƙaci a gaggauta sakin dukkan kuɗaɗen da suka rage da ake buƙata domin kammala aiwatar da kasafin kuɗin manyan ayyuka na shekarar 2025, tare da hanzarta aiwatar da na shekarar 2026.

Me wasiƙar ta ƙunsa?

Kamar yadda jaridar Vanguard ta samu kwafin wasiƙar ta kuma wallafa, wasikar ta bayyana cewa:

''Wani muhimmin sashe na dokokin kasafin kuɗin shekara-shekara, wanda aka sake bayyana shi a cikin dokar dasafin kuɗin 2026 bisa tanadin dokar shekarar kasafin kuɗi da kuma fassarar sashe na 318 na kundin tsarin Mulkin Najeriya, sun tanadi cewa kuɗaɗen da aka ware a kasafi an samar da su ne domin soma amfani da su daga ranar 1 ga Janairu zuwa ranar 31 ga Disamba na kowace shekara''.

Haka kuma, ba za a sake sakin wani ɓangare na kuɗin da aka ware daga Asusun Kuɗaɗen Gwamnati bayan ƙarshen shekarar kuɗi ba.

"Ci gaba da tsawaita kalandar kasafin kuɗi domin aiwatar matakan kashe kuɗaɗen manyan ayyuka ba al'amari ne da ya dace ba, domin yana jefa rashin tabbas da jinkiri cikin yadda ake tafiyar da harkokin kuɗin gwamnati."

A cewar ƙungiyar, bayanan da ake da su sun nuna cewa har yanzu ba a saki tare da tabbatar da samun dukkan kuɗaɗen kasafin manyan ayyuka na shekarar 2025 da aka ɗauko zuwa wannan shekara ba.

Mafi yawan ma'aikatu, hukumomi da sassan gwamnati (MDAs) sun karɓi ƙasa da kashi 50 cikin 100 na kuɗaɗen da ake buƙata domin aiwatar da sauran ayyukan raya ƙasa.

Ta ƙara da cewa, har yanzu ba a saki ko sisin kwabo ba domin aiwatar da kasafin kuɗin manyan ayyuka na gwamnatin tarayya na shekarar 2026, duk da cewa shekara ta yi nisa.

CSJ ta kuma soki majalisar dokoki ta ƙasa, tana zarginta da gaza sauke nauyin da Kundin Tsarin Mulki ya ɗora mata na sa ido kan ayyukan gwamnati, musamman wajen tilasta wa ɓangaren zartarwa aiwatar da dokokin kasafin kuɗin da Majalisar ta amince da su.

A wane mataki kasafin 2026 yake?

Dakta Murtala Abdullahi Ƙwara malami ne a Sashen nazarin kimiyyar tattalin arziki a Jami'ar Umaru Musa 'Yar Adu'a ya ce, "Abinda muka sani shi ne majalisa ta yi zama akan kasafin na sekarar 2026 kuma shugaban ƙasa ya rattaba masa hannu, wannan shi kadai zamu iya sani a ciki.

Kuma har yanzu ba a yi amfani da shi wannan kasafi ba, musamman wurin aiwatar da manyan ayyuka kamar asibiti da makarantu da sauran su.

''To wannan shi ne halin da kasafin kuɗin Najeriya yake ciki, sannan duk da an amince da shi amma har yanzu ba a aiwatar da shi ba", in ji shi.

Me ya sa ake samun jinkirin aiwatarwa?

Masani tattalin arzikin, ya ce, "shi wannan samun jinkiri ba a iya cewa ga dalilin da ya kawo shi, tunda su mahukunta ba su fito suka yi cikakken bayanin yadda za a fahimta cewa suna samun wata matsala ko rashin samun kuɗin ko wani abu makamancin haka ba.

Sannan gwamnatin ta samu rara ta kuɗi saboda ba ta biyan tallafin mai a yanzu".

Sai dai masanin ya ce ga dukan alamu ana iya danganta hakan da wata buƙata tasu kawai, suna da tsarinsu da irin nasu dalilai da ya sa ba su aiwatar da kasafin, inda ya ce "a Najeriya dukan gwamnatocin da suka gabata ba a taɓa samun wadda ta ƙi aiwatar da kasafin kuɗi ba sai wannan ta shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma su ma 'yan majalisa sun ƙi su fito su yi bayani saboda haƙƙin al'umma ne, in ji Dakta Murtala Abdullahi Ƙwara..

Mece ce illar hakan?

Masana tattalin arzikin sun ce rashin aiwatar da kasafi zai haifar da babban giɓi tare da mayar da ƙasa baya.

Dakta Murtala Ƙwara ya ce, na farko dai zai tsayar da tattalin arziki, wanda zai ƙara yawaitar talauci da tsananin rayuwa ga jama'a.

''Zai kuma iya haifar da rashin aminci tsakanin 'yan ƙasa da ma baƙi daga waje da za su iya saka jari a Najeriya, abin da zai ƙara rage masu saka jari kenan".

A cewarsa, cin hanci da rashawa zai ƙaru saboda abin da ya kamata a ce an yi domin kuɗaɗe su zagaya a cikin al'umma an rasa hakan kasancewar duk manyan ayukka an tsaida su, kuma wata sila ce ta ƙaruwar miyagun laifuka.

...

Asalin hoton, PRESIDENCY

Tasirin kasafin kuɗi ga ƙasa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A taƙaice, kasafi shi ne taswirar kuɗin gwamnati gabaɗaya, yana nuna inda gwamnati za ta samo kuɗi da inda za ta kashe su a cikin shekara.

Daga cikin abubuwan da suka dogara ga kasafin kuɗi sun haɗa da samar da hanyoyi da makarantu da asibitoci da ruwan sha da wutar lantarki da titunan mota da layin dogo da sauransu.

Idan gwamnati ta aiwatar da kasafin kuɗi za a samar da wasu daga muhimman ayyukka, alal misali gina hanya, da za a ɗauki ma'aikata tamkar lebarori da injiniyoyi da direbobi, abin da zai sa masu sana'a da 'yan kwangila su kuma su kashe kuɗin a kasuwanni kuma hakan zai bunƙasa tattalin arziki.

Kamar dai yadda Cibiyar da ke Neman Tabbatar da Adalci Ga Jama'a ta (CSJ) ta yi hasashe, Mafi yawan ma'aikatu, hukumomi da sassan gwamnati (MDAs) sun karɓi ƙasa da kashi 50 cikin 100 na kuɗaɗen da ake buƙata domin aiwatar da sauran ayyukan raya ƙasa.

Masana tattalin arziki ma na tababar idan adadin ya kai haka.

Hasalima dai, a cewar Dakta Murtala Ƙwara, "wasu ma na iƙirarin cewa kashi 30 kadai aka yi amfani da shi, kuma abin da wannan ke bayar da mamaki shi ne, an yi amfani da kasafin kuɗin 2025 a wannan shekara ta 2026, wato tsawaita kasafi, kuma doka ba ta yarda da shi ba".

A ta bakin masana tattalin arziki dai, irin wannan jan ƙafa da ƙin aiwatar da kasafi ba tare da yin cikakken bayani ba, zai taka rawa wajen taɓarɓarewar abubuwa da dama a kowace ƙasa, musamman lalacewar aikin gwamnati da ƙaruwar talauci sakamakon rashin zagayawar kuɗi tsakanin jama'a da kuma ƙaruwar cin hanci da rashawa.