Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Talata 15/09/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Hoto
  • Cyber Truck
  • Adeyemi Adeniyi
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman Minjibir

  1. Amurka na fama da karancin makamai- Pentagon

    Makaman Amurka

    Asalin hoton, US Navy via Getty Images

    Bayanan hoto, Yakin Iran na daga cikin dalilan karancin manyan makamai a Amurka

    Ma’aikatar tsaron Amurka ta ce yaƙin da ƙasar ke yi da Iran ya jawo ƙarancin wasu makamai da kuma tsaiko wajen sake cike ma’ajiyar makamai. Hakan dai ya ci karo da ikirarin Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya sha musanta cewa ƙasar na fuskantar ƙarancin makamai.

    Wani rahoto daga babban mai sa ido mai zaman kansa na Ma’aikatar Tsaron Amurka, ya ce ƙasar ta kashe sama da dala biliyan ashirin da biyu kan makamai tsakanin watan Fabrairu zuwa Yunin shekarar nan. Rahoton ya ce hakan ya jawo ƙarancin wasu muhimman makamai a ma’ajiyar sojojin ƙasar.

    Sai dai Shugaba Trump ya sha cewa makaman Amurka basu da iyaka, ba za a iya karar da su ba, inda ya karyata rahotannin da ke cewa akwai ƙarancinsu.

    Rahoton sabon binciken ya kuma bayyana cewa akwai matsaloli a masana'antun da ke kera makamai, lamarin da ke kawo tsaiko wajen sake samar da su, sai dai bai bayyana adadin makaman da suka rage a hannun sojojin Amurka ba.

    A yayin yaƙin, sojojin Amurka sun yi amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango, da makaman kariya daga hare-haren ta sama na makamai masu linzami na Iran.

    Wani bincike da cibiyar CSIS ta fitar a ƙarshen watan Yuli ya nuna cewa adadin wasu makamai masu kare sararin samaniya, ya ragu sosai.

    Rahoton ya ce Ma’aikatar Tsaron Amurka na ƙoƙarin sauƙaƙa hanyoyin sayen makamai da kuma rage lokacin da ake ɗauka wajen kera su, domin magance ƙarancin. Yaƙin ya kuma jawo asarar kayan yaƙi da aka kiyasta kudinsu da dala biliyan uku da digo bakwai.

    Jimillar kuɗin da Amurka ta kashe kan yaƙin tsakanin 28 ga Fabrairu zuwa 30 ga Yuni ya kai sama da dala biliyan talatin da uku.

    A farkon yakin Shugaba Trump ya sha cewa yaƙin ba zai dauki lokaci ba, sai dai a baya-bayan nan ya ce akwai yiwuwar yaƙin bai ƙare ba sai bayan zaɓen rabin wa’adin mulki na Amurka da za a gudanar a watan Nuwamba.

    Wasu kuri’un jin ra’ayin jama’a kuma sun nuna cewa yaƙin bai samu karɓuwa sosai tsakanin Amurkawa ba.

  2. Kwalejoji 115 na gwamnatin Najeriya ba su koma karatu ba

    A Najeriya makarantun kwolejin gwamnatin taraya guda 115 a fadin kasa sun kasance a rufe a daidai lokacin da sauran takwarorinsu ke komawa karatu bayan kammala hutun zangon karatu.

    Wannan lamari na zuwa ne bayan kokarin gwamnatin Tarayya ke yi na mika makarantar kwolejin gwamnati ta King’s College da ke Lagos hannun kungiyar tsofafin daliban makarantar, da fita daga hannun gwamnatin.

    Sai dai wannan lamari mai cike da sarkakiya, ya ɗarsa fargaba ga zukatan ma'aikatan nakarantar ta King' College da ke Lagos.

    Ma’aikatan makarantar da kungiyar manyan ma’aikatan gwamantin tarayya da na ma’aikatar illimi ta kasa sun jadada cewa makarantun za su ci gaba da kasance a rufe muddin ba a yi watsi da wannan batu ba.

    A wata sanarwa da ministan ma’aikatar illimi ta kasa Dr Tunji Alausa, ya fitar ya sake jaddada cewa gwamnati ta amince kungiyar tsofaffin daliban ta mallaki makarantar tare da kafa wani kwamiti da zai kula da shirye-shiryen mika ta gare su.

    Kwamitin zai yi aikin watanni 6, da duba abubuwan da suka dace ayi wajen gudanar da makarantar da zamanantar da ita da gudanarwa ba tare da wata matsala ba.

  3. NDLEA ta lalata dakin gwaje-gwaje na Meth, da cafke ɗan Mexico

    Kankarar sinadarin Meth

    Asalin hoton, Australian Federal Police

    Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta sake tarwatsa wani dakin gwaje-gwaje na methamphetamine a wata masana tare da cafke wani dan kasar Mexico mai safarar miyagun kwayoyi da ke yunkurin tserewa daga kasar ta filin jirgin saman Legas.

    Shugaban hukumar Birgediya-Janar Buba Marwa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka aikewa manema labarai ta hannun daraktan yaɗa labaran hukumar Femi Babafemi,,kan ci gaban da hukumar ta kara samu na kamawa da kama masu safarar da hada muggan kwayoyi a kasar.

    Marwa ya kara da cewa samamen da suka kai ya kara fito da matsalar da ake fama da ita a kasar ta samar da muggan kwayoyi da ƴan kasa da na kasashen waje ke kafa wuraren sarrafa su.

    Ya kara da cewa, a samamen da jami'ansu suka kai, sun gano an boye masana'antun ne a cikin wani daji a ƙauyen Tapa da ke karamar hukumar Ibarapa ta Arewa a jihar Oyo, inda gwaje-gwajen da aka yi a wurin suka tabbatar da yawan sinadarin methamphetamine da aka sarrafa.

    Wannan nasarar ta biyo bayan binciken kwakwaf na tsawon watanni da NDLEA ta gudanar, kan wata babbar kungiyar masu aikata laifuka, bayan jerin dakunan gwaje-gwajen miyagun kwayoyi da aka gano a sassan kasar daban-daban na Najeriyar.

  4. Ƴan gudun hijirar Yemen 200,000 sun tsallaka Djibouti -MDD

    Yan gudun hijirar Yemen

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Yawancin ƴan gudun hijirar sun dogara da dan abin da hukumomi da kungiyoyin agaji ke tallafa mu su da shi

    Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum 200,000 sun rasa muhallansu a sabon rikin da ya barke tsakanin ƴan tawayen Houthi na Yemen da Iran ke marawa baya da gwamnatin kasar Saudiyya ke marawa baya.

    Wasu dubbai sun tsallaka iyakar Yemen da kasar Djibouti da ke gabashin Afurka ta mafani da mashigar Bab el-Mandeb, inda jami'ai ke nuna damuwar karin ayyukan jin kai.

    Kazamin fadan da ake gwabzawa a Yemen na kara jefa iyalai cikin mawuyacin hali da barin gidajensu. Dakarun Saudiyya sun kaddamar da hare-hare ta sama kan 'yan tawayen Houthi, a matsayin martani kan hare-haren da suka kai wasu 'yankunan ƙasar.

    Jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun ce hare-haren da aka kai sun lalata hanyoyin da kafar sadarwa da ababen more rayuwa, lamarin da ke tarnaki wajen kai agaji ga mabukata.

    Yawancin wadanda sukai gudun hijira mata ne da kananan yara cikin mawuyacin hali, amma sun dan samu nutsuwa bayan tsallakawa tudun mun tsira.

    Ƴan tawayen Houthi dai na kara dannawa tekun maliya, da karbe ikon tsuburin Perim da ke kusa da mahigar Bab el‑Mandeb, wadda babbar hanya ce ga jiragen 'yan kasuwa zuwa yankin Asiya.

  5. An dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a Netherlands

    An dakatar da zirga-zairgar jiragen ƙasa a sassa da dama na Netherlands, bayan da hukumomi suka yi zargin cewa an lalata wasu layukan dogo a ɓoye.

    Lamarin ya kawo tsaiko a zirga-zirga jiragen kasa a tsakiya da gabashin ƙasar. Hakan na zuwa ne sa'o'i kadan gabannin buɗe majalisar dokokin ƙasar a hukumance.

    Kamfanin da ke kula da jiragen ƙasa na Netherlands, ya ce an gano wasu abubuwa da aka ɗaura a kan hanyar jiragen kasa a wurare daban-daban, musamman a yankunan karkara.

    Ya kuma ce anyi amfani da fasahar zamani wajen daukar hotunan waɗannan abubuwa a inda hanyar ta nuna ta cika duk da cewa babu wani jirgin ƙasa a wurin. Har yanzu ba a gano wanda ake zargi da aikata hakan ko kuma dalilin yin hakan ba, sai dai rundunar ƴansandan ƙasar ta ce tana gudanar da bincike.

    Manyan birane da kuma hanyoyin zuwa babban filin jirgin saman ƙasar sun fuskanci tsaiko da cunkuso, lamarin da ya shafi ababen hawa a kan tituna, saboda an tilasta rufe wasu tashoshin jiragen ƙasa.

  6. Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro a makarantu

    Dalibai na daukar karatu

    Asalin hoton, OTHERS

    Hukumomin Najeriya sun ce sun tsaurara matakan tsaro da sanya ido a sansanonin horar da masu yi wa kasa hidima NYSC, da makarantu da wuraren ibada, sakamakon bayanan sirri da ke nuni da cewa kungiyoyin ‘yan bindiga na shirin kai hare-hare a fadin kasar.

    Cikin wata sanarwa da rundunar ƴansandan Najeriya ta aike wa rundunonina ta a faɗin ƙasar, ta yi gargaɗin samun ƙaruwar haɗin kai tsakanin gungun ƴanta'adda da masu aikata muggan laifuka domin kai hare-haren haɗin gwiwa a daidai lokacin da ɗalibai ke komawa makaranta a zango na 2026/2027.

    Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa rahotannin sirri sun nuna yadda gungun mahara ke zirga-zirga daga jihar Katsina da ke arewa maso yamma, zuwa jihar Kaduna mai makwabtaka, zuwa jihar Filato da ke arewa ta tsakiya.

    Rahotannin sun kuma yi gargaɗin cewa mayaƙan da ake zargi na ƙungiyar ISWAP da abokan hulɗarsu na cikin gida na gudanar da bincike da leƙen asiri a kan wuraren da za su iya kai wa hari.

    Gwamonin sauran jihohin ƙasar ciki har da waɗanda ke fama da matsalar tsaro sun ɗauki matakin kariya da shirin ko-ta-kwana.

    Hukumomi a jihar Oyo ta sami nasarar cafke mutane 5 da ake zargi da ta’addanci, waɗanda a yanzu haka ke hannun ƴansanda bayan harin da suka kai wani sansanin soji da ke a wajen birnin jihar.

    Wannan gargaɗin na zuwa ne kwana guda bayan jami'an tsaro a Jihar Oyo sun fitar da bayanan sirri kan shirin mayaka na kafa sansanoni a Jihar Osun domin kawo cikas ga zaben 2027 da ke tafe.

    Wasu maharan na daban sun kai hari sansanin sojoji na Operation Burst da ke hanyar Igbeti zuwa Igboho a yankin Oorelope da Olorunsogo, inda suka ƙone motar jami'an tsaro ta sintiri da wanmi bangare na ginin sansanin.

    Sai dai babu wanda ya rasu ko jikkata a harin ba amma an yi nasarar cafke mutum biyar da ake zargi da kai harin.

  7. Rufe mashigar ruwan Bab al-Mandeb zai haifar da mummunan bala'i - Qatar

    Qatar ta bayyana damuwa kan ƙalubalen da ke tattare da rufe mashigin ruwan Bab al-Mandeb.

    Wani jami’i a ma’aikatar harkoki wajen Qatar, Ibrahim al-Hashemi, ya faɗa wa manema labarai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa wahalar da duniya ta shiga sakamakon rufe Mashigar Hormuz ya kai maƙura a don haka bai kamata a ƙara matsalar ba da rufe Bab al-Mandeb.

    Rufe hanyar zuwa Tekun Maliya ta kudanci zai zama bala’i ga duniya baki ɗaya inda kuma y ace “tuni ma muka fara ganin matsalolin…A don haka, Qatar na ƙara jaddada bin maslahar diflomasiyya da kuma tattaunawa."

    A makon da ya gabata ne mayaƙan Houthi suka ƙwace iko da gaɓar gabashin Tekun Maliya da kuma mashigar Bab al-Mandeb.

  8. Kusan mutum miliyan 20 sun shiga halin yunwa a Sudan - WFP

    Al'ummar Sudan

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an jin ƙai sun ce kusan mutum miliyan 20 na faɗa wa ƙangin yunwa a Sudan yayin da yaƙi tsakanin sojoji da dakarun RSF ya shiga shekara ta huɗu ana gwabza shi.

    Bayan ziyarar da ya kai ƙasar, shugaban hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Carl Skau ya ce Sudan na ci gaba da zama ƙasar da yanayin jin ƙai ya yi muni.

    Ya ce mutum miliyan 14 ne suka rasa matsugunni yayin da rikici ke ƙamari a yankunan Blue Nile da tsakiyar Kordofan.

    Mr Skau ya kuma yi gargaɗi cewa wataƙila a samu raguwar kayan jin ƙai cikin makonni masu zuwa saboda ƙarancin kuɗi.

  9. Kwararar ƴan gudun hijira daga Yemen zuwa Djibouti ya zo da ba zata - MDD

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana kwararar ƴan gudun hijira da ke tserewa yaƙi a Yemen zuwa Djibouti a matsayin abin da ba a zata ba - inda fiye da mutum 2,000 ke tsallakawa tekun Maliya tun Alhamis ɗin makon jiya.

    Wakiliyar Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya a Djibouti ta ce rabin ƴan gudun hijirar da suka isa ƙasar yara ne.

    Jiragen ruwa ɗauke da ƴan gudun hijirar daga Yemen na ci gaba da isa birnin Obock. Wasu daga cikinsu masu tsaron teku ne suka kuɓutar da su bayan da mai ya ƙare musu a tafiyar kilomita 20 ta tsallakawa ƙasar daga Yemen.

    UNICEF ta ce akasarin mutanen da suka isa Djibouti yara ne, kuma sun galabaita sai dai hankalinsu ya ɗan kwanta kasancewar sun tserewa yaƙin.

    Jami'ai sun yi gargaɗi cewa adadin ƴan gudun hijirar na iya ƙaruwa idan aka ci gaba da gwabza faɗan, lamarin da zai ƙara dagula lamarin jin ƙai a Djibouti.

    Tuni dai ƙasar ta karɓi baƙuncin dubban mutanen da suka rasa matsugunni ciki har da masu neman mafaka.

  10. Za mu mayar da martani kan hare-haren Houthi - Saudiyya

    Saudiyya ta ce za ta mayar da martani cikin gaggawa kan hare-haren da mayaƙan Houthi ke kai mata.

    Hare-haren na baya-bayan nan da mayaƙan na Houthi ke kai wa da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa sun jikkata mutane 13 a Saudiyya.

    Bayan ayyana takunkumin jiragen ruwa a teku, sai mayaƙan Houthi suka fara kai hare-hare kan jiragen ruwan Saudiyya a Tekun Maliya.

    A makon da ya gabata ne suka ƙwace iko da gaɓar gabashin Tekun Maliya da kuma mashigar Bab al-Mandeb, wadda muhimmancinta ke ƙaruwa yayin da ake fuskantar cikas a mashigar Hormuz.

    A halin da ake ciki kuma, an sanar da cewa za a gudanar da wani taron gaggawa na Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya kan batun Bab al-Mandeb a birnin New York a yau, bisa buƙatar da Faransa ta gabatar.

  11. Mutum 44 sun mutu sanadin cutar mashaƙo a Zamfara

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar Lafiya a Zamfara ta ce mutum 367 ne suka kamu da cutar mashaƙo kuma wasu fiye da 320 sun warke bayan sun samu kulawa.

    Daraktan kula da lafiyar al'umma a ma'aikatar, Dakta Yusuf Haske ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau lokacin da yake ƙarin bayani game da halin da ake ciki a jihar game da cutar. Ya kuma ce cutar ta halaka mutum 44.

    Dakta Haske ya bayyana cewa an ɗauki samfur ɗin mutanen inda aka gwada su a ɗakin gwaje-gwaje sannan kuma an sake tabbatar da cewa cutar mashaƙon ce bayan da aka sake duba samfur ɗin a wata cibiya da ke Abuja.

    A cewar shi, bayan tabbatar da lamari ne, ma'aikatar lafiya ta jihar bisa umarnin gwamna Dauda Lawal ta ayyana samun ɓarkewar cutar a jihar.

  12. Amurka ta tabbatar da girke makamin yaƙi a sararin samaniya

    NASA

    Asalin hoton, Thomas Traasdahl/Ritzau Scanpix/AFP via Getty Images

    A karon farko, Amurka ta tabbatar da cewa ta girke wani makamin yaƙi a sararin samaniya da ke zaga duniya.

    Sakataren Rundunar Sojin Sama ta Amurka, Troy Meink, ya ce girke makamin ya zama wajibi domin kare ƙasar daga duk wata barazana daga abokan gaba.

    Sai dai kuma bai bayyana irin ƙwarewar da makamin yake da ita ba, ko kuma lokacin da aka girke shi a sararin samaniyar ba.

    A baya, manyan jami'ai a rundunar sojin Amurka sun sha bayyana cewa suna shirin ƙarfafa ƙarfin sojin ƙasar a sararin samaniya, suna masu nuni da irin shirye-shiryen Rasha da China na inganta hanyoyin da za su iya kai hari ko kuma tarwatsa ayyukan tauraron ɗan adam na Amurka idan rikici ya ɓarke nan gaba.

  13. Gwamnatin Sokoto ta rufe masallacin Sheikh Musa Lukuwa

    Sheikh Musa Lukuwa

    Asalin hoton, Sheikh Musa Ayyuba Lukuwa Sokoto/FB

    Gwamnatin Jihar Sokoto ta sanar da rufe masallacin Juma’a na Musa Lukuwa har sai yadda hali ya yi bayan tashin hankalin da ya faru a makon da ya gabata inda wani matashi ya daɓawa malamin wuƙa.

    Cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar, gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne domin bayar da damar yin bincike kan harin da aka kai tare da kisa.

    Sanarwar ta kuma ce gwamnati ta kafa kwamitin malamai domin gudanar da bincike kan musabbabin rikicin inda kuma ake sa ran kwamitin zai bai wa gwamnati shawarwari kan matakan da suka dace a ɗauka.

    Gwamnatin ta kuma nesata kanta daga duk wani al'amari na fakewa da addini don yin ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

    Sanarwar ta yi kira ga al’ummar jihar da su guji furta kalamai masu tayar da hankali da ka iya tunzura jama’a da kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kan al'ummar jihar.

    Malam Musa Ayuba Lukuwa malamin addinin Musulunci ne a jihar Sokoto da ke bin fahimtar Ahlussunnah Wal Jama'a.

    Yana daga cikin malamai masu yawan janyo taƙaddama musamman dangane da al'amura masu sarƙaƙiya.

  14. Ana ci gaba da yaƙi tsakanin Houthi da Saudiyya

    Ana ci gaba da gwabza faɗa tsakanin 'yan tawayen Houthi a Yemen da kuma Saudiyya, inda ɓangarorin biyu ke bayar da rahoton ƙarin asarar rayuka da jikkatar da aka samu.

    Ƙawancen sojojin da Saudiyya ke jagoranta, wanda ke marawa gwamnatin Yemen baya, ya ce mutum 13 fararen hula sun jikkata sakamakon hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙi da mayakan Houthi suka kai kan biranen Khamis Mushait, da Abha da kuma Taif da ke kudancin Saudiyya.

    A Yemen kuma, kafar yaɗa labaran 'yan Houthi ta ruwaito cewa mutum uku sun mutu a hare-haren sama da rundunar ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta ta kai a lardin Taiz da ke kudu maso yammacin ƙasar.

    Tun da farko a ranar Litinin, mayakan na Houthi sun kai hari kan sansanin sojin sama na Sarki Khalid da ke kudancin Saudiyya.

    Wakilin BBC ya ce ƙara ta'azzarar da rikicin ke yi ya ƙara sanya damuwa a kan batun samar da makamashi da kuma batun tsaron jiragen ruwa.

  15. Ba ma yaƙi da Saudiyya - Iran

    Massoud Pezeshkian

    Asalin hoton, SPUTNIK/KREMLIN/EPA/Shutterstock

    Shugaban Iran, Massoud Pezeshkian ya ce ƙasarsa ba yaƙi take da Saudiyya ba inda ya ce ƙasashen Gabas ta Tsakiya ba su fahimci dalilan hare-haren da Iran ɗin ke kai wa sansanonin sojojin Amurka a yankin ba.

    A hirar da ya yi da kafar yaɗa labarai ta India Today yayin da ya halarci taron BRICS, Mr Pezeshkian y ace “ba ma yaƙi da Saudiyya sannan suma ƴan Houthi suna da nasu matsalolin. Ya kamata duka ƙasashen yankin su zauna domin tattauna hanyoyin samar da zaman lafiya da tsaro. Babu wani dalili na yaƙar junanmu.”

    Shugaban na Iran ya kuma jaddada cewa “matsalar it ace Amurka ta kafa sansanin soji a ƙasashen Larabawa. Suna kai mana hare-hare daga sansanonin.”

    “Ba zai yiwu a ci gaba da kai mana hare-hare daga wuri guda ba a kullum”, kamar yadda Mr Pezeshkian ya bayyana.

  16. Karatu don nishaɗi na da alaƙa da ingantacciyar lafiyar ƙwaƙwalwa - Bincike

    Karatu

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu bincike a Birtaniya sun gano cewa yin karatu don nishaɗi na da alaƙa da samun ingantacciyar lafiyar ƙwaƙwalwa, da rage damuwa da kuma rage yiwuwar kamuwa da cutar mantuwa.

    A cikin wani sabon nazari da suka yi bayan tattara hujjoji da dama ciki har da takardun bincike, da sakamakon binciken jin ra’ayin jama’a da kuma hotunan binciken ƙwaƙwalwa, masana kimiyyar daga Jami’ar Cambridge sun bayyana cewa yin karatu akai-akai, ko da kuwa wane irin littafi ne, na iya samar da fa’idojin lafiya a kowanne mataki na rayuwa.

    Ɗaya daga cikin sakamakon binciken, wanda ya shafi matasa sama da dubu goma, ya nuna cewa waɗanda suka fara karatu don nishaɗi tun suna ƙanana, sun fi kwakwalwa sosai da mayar da hankali a kan karatu.

    Binciken ya kuma nuna cewa irin waɗannan matasa sun fi samun nasara a makaranta, idan aka kwatanta da takwarorinsu da ba sa yawan karatu don nishaɗi.

  17. Isra'ila ta sanar da mutuwar kwamandan sojin Hamas a Gaza

    Hamas

    Asalin hoton, Ayman Majed Harb Alhisi/Anadolu via Getty Images

    Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da mutuwar wani kwamandan sojin Hamas a Gaza.

    Ita ma kafar yaɗa labarai ta Falasɗinu ta tabbatar da mutuwar Ahmed al-Batash, da aka fi sani da "Abu Osama".

    Kafar yaɗa labaran ta ce harin da aka kai ta sama ya shafi motarsa.

    An tsara cewa Mohammed bin Salman zai gana da Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi nan da sa'oi masu zuwa.

    Lamarin na zuwa ne yayin da ƴan Houthi suka yi iƙirarin ci gaba da kai hare-hare kan wasu cibiyoyi a Saudiyya.

    Mohsen Rezaei, Sakataren babban Majalisar tsaron Iran ya sake nanata cewa Tehran ba za ta tattauna da Amurka ba har sai an biya buƙatun da aka gabatar a yarjejeniyar fahimta da aka gabatar.

  18. Maraba

    Barkan ku da zuwa shafin Kai Tsaye na BBC Hausa da ke kawo muku labarai na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sauran sassan duniya.

    Sai ku kasance tare da mu a wannan rana ta Talata don sanin halin da ƙasashen duniya ke ciki.

    Sunana Nabeela Mukhtar Uba kuma zan kasance da ku har zuwa anjima da abokan aiki za su karɓi ragama.

    Kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin samun ƙarin labarai har ma da kallon bidiyo.