Yadda ƴan bindiga suka sace limamai 6 a Zamfara

Asalin hoton, Udochukwu Orji/FB
Ana can ana ci gaba da neman wasu malaman addinin musulunci da ƴan fashin daji suka yi garkuwa da su a Talatar Mafara da ke jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya.
Ƴansanda a sun ce wasu ƴanbindiga sun sace limamai shida a ranar Asabar, lokacin da suka halarci wani taron addu'a na neman nasarar Shugaba Bola Tinubu, wanda ke neman wa'adi na biyu a babban zaɓen da za a gudanar a watan Janairu.
Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari kuma shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar ya shirya.
Sai dai a wata sanarwa da rundunar sojin ta Fansar Yamma ta fitar, ta ce bincikensu ya tabbatar da cewa ba a gidan Abdulaziz Yari, wanda shi ne ya shirya taron, aka sace malaman ba.
"Mun dai samu labarin cewa an sace wasu mutane matafiya da suka taso daga yankin dajin Sububu zuwa Talata Mafara daga Bakura, kuma jami'anmu da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro suna ƙoƙarin ceto," in ji sanarwar.
Bayanan da BBC ta tattara daga mutanen gari da hukumomi sun sun nuna cewa malaman na tsaka da tafiya ne yan bindigar suka tare motarsu, sannan suka buɗe musu wuta kafin su suka yi awon gaba da su.
Yadda ƴan bindigar suka sace malaman
Wani mutumin garin da ya nemi a sakaya sunansu ya ce direban da ya tunkari inda ƴan bindigar suka kafa shinge ne kamar na bincike na sojoji da ake da su a hanyar, kuma bai lura da su ba sai da ya je kusa ta yadda ba zai iya sauya akalar motar ba.
"Sai da ya zo dab inda suke, ya yi baya suka buɗe mishi wuta, [suna cewa] ya tsaya... Babu halin ya gudu," in ji shi.
Mutumin ya shaida wa BBC cewa sau tari ƴan bindigar sukan yi shiga ce irin ta jami'an tsaro su tare hanya, ta yadda za su yi amfani da wannan dama su kai wa matafiya hari.
Akwai shingayen binciken jami'an tsaro da dama a kan hanyoin Zamfara da ƴan bindiga da dama suka addaba.
"Za su da kakin sojoji su tsaya a hanya, idan direba bai ankara ba, zai yi tunanin shingen binciken sojoji ne."
Ya ce babu irin cutarwar da ba su yi wa matafiya idan suka samu dama a kan hanyar, inda suke harbe wasu da jikkata da dama.
Matakin da jami'an tsaro suka ɗauka
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Jihar Zamfara dai na ɗaya daga cikin jihohin da suke fama da wannan matsala ta satar mutane domin neman kuɗin fansa, duk da yake hukumomi na cewa suna iya bakin ƙoƙarinsu wajn ganin sun daƙile abubuwan da ke faruwa.
Kakakin rundunar ƴansanda jihar Zamfara DSP Yazid Abubakar ya shaida wa BBC cewa tuni jamia'an tsaro suka bazama domin ceto mutanen 6 da aka sace.
"A rahoton da muka samu mutum shida ne aka ɗauka, ba mu sani ba ko akwai wasu mutanen daban," in ji DSP Yazid.
Ya ce suna roƙon al'umma da zarar sun ga wani bayanin da zai taimaka wajen cetor mutanen su ba su.
Bayanai na cewa akwai ɗimbin mutane da suka shafe tsawon lokaci a wajen ƴan bindiga baya ga waɗanda aka kashe a wasu wurare daban-daban.
Sace mutane domin neman kuɗin fansa ya zama babbar hanyar samun kuɗaɗen shiga ga ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da dama a Najeriya, ciki har da masu iƙirarin jihadi da kuma ƙungiyoyin ƴanbindiga waɗanda ba su da wata manufa ta aƙida, waɗanda ke neman kuɗin fansa kafin su saki mutanen da suka yi garkuwa da su.
Rashin tsaro da kuma halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki na daga cikin manyan batutuwan da suka mamaye yaƙin neman zaɓen da ake gudanarwa a yanzu.
Wane ne Sanata Abdulaziz Yari?

Asalin hoton, Udochukwu Orji/FB
Sanata Abdulaziz Yari mai wakiltar Zamfara ta Yamma ne aka sanar a matsayin Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen takarar shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu.
Sanarwar da kakakin shugaban Najeriyar, Bayo Onanuga ya fitar, ta lissafo wasu jiga-jigan ƴan siyasa daga arewaci da kudancin ƙasar da za su yi a kwamitoci daban-daban a shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.
Sanator Abdul'aziz Yari jigo ne kuma fitaccen ɗan siyasa a Najeriya, wanda a halin yanzu yake matsayin Sanata mai wakiltar shiyyar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawan Najeriya.
Shi tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne na tsawon wa'adi biyu (daga 2011 zuwa 2019) kuma tsohon Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF).
An haife shi a 1968 a ƙaramar hukumar Talata Mafara da ke Jihar Zamfara
Ya fara shiga harkokin siyasa ne gadan-gadan tun farkon Jamhuriya ta Huɗu a shekarar 1999.
Ya yi aiki a matsayin Sakataren jam'iyyar ANPP na Jihar Zamfara, sannan daga baya ya zama Shugaban Jam'iyyar ANPP na Jiha.
A shekarar 2007, an zaɓe shi a matsayin Ɗan Majalisar Wakilai ta tarayya mai wakiltar mazaɓar Anka/Talata Mafara, inda har ya riƙe shugabancin Kwamitin Kashe Kuɗi na majalisar.
A zaɓen shekarar 2011, ya doke tsohon gwamna Mahmud Shinkafi a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar ANPP.
Ya sake lashe zaɓe a shekarar 2015 a ƙarƙashin sabuwar jam'iyyar APC.











