Shin yawan kallon bidiyo da yawa na illa ga ƙwaƙwalwar matasa?

dhallinyaro

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wataƙila ka taɓa ɗaukar wayarka domin kallon ɗan gajeren bidiyo kafin kwanciya barci, ko kuma a lokacin da kake da ɗan hutu. Kafin ku ankara sai ka ga ka ɗauki dogon lokaci kana kallon bidiyo ɗaya bayan ɗaya, sai bayan ka ɗago idonka daga wayar, sai ka fahimci cewa ka shafe sa'o'i ba tare da ka sani ba.

Wannan ɗabi'a ta zama dalilin da ya sa mutane da dama ke amfani da gajerun bidiyoyi a kafafen sada zumunta kamar TikTok, Instagram, YouTube Shorts da Facebook.

Sai dai abin tambayar a yanzu ba wai tsawon lokacin da matasa ke shafewa a gaban allon waya kawai ba ne. Tambayar ita ce ko yadda suke kallon bidiyo daga ɗaya zuwa wani, da kuma yadda aka tsara waɗannan manhajoji, na iya shafar yadda matasa ke mayar da hankali, tunani da kuma riƙe bayanan da suke gani.

What happens when the scenes don't stop?

taleefan

Asalin hoton, Getty Images

Wani sabon nazarin kimiyya da ya duba bincike 42 da aka yi, akan mutane 46,900 da ke da matsakaicin shekaru tsakanin kai 16-17, ya nuna alaƙa tsakanin yawan kallon gajerun bidiyoyi da wasu matsalolin da suka shafi tunani da ɗabi'a.

Binciken, wanda Springer Nature ta wallafa a watan Yuni mai taken "Can endless browsing be controlled?", ya gano cewa yawan kallon gajerun bidiyoyi, wanda a wasu lokuta kan ɗauki mutum sa'o'i yana kallo, na da alaƙa da abubuwa kamar haka:

  • Ƙaruwar rashin iya mayar da hankali.
  • Raguwar nazarin ƙwaƙwalwa da iya sarrafa tunani.
  • Yawan samun damuwa, baƙin ciki
  • Alamomin da ke nuna yiwuwar kamuwa da wannan ɗabi'a

Sai dai binciken bai ce waɗannan sakamakon na nufin cewa kallon gajerun bidiyoyi ne ke haddasa matsalar ƙwaƙwalwa ko rage tsawon lokacin da mutum zai iya mayar da hankali ba.

Dalilin haka shi ne mafi yawan binciken da aka duba sun maida hankali ne kan duka ɓangarorin a taƙaitaccen lokaci.

Saboda haka, ana buƙatar ƙarin bincike mai zurfi da kuma na dogon lokaci domin gano ainihin alaƙar da ke tsakanin yawan kallon gajerun bidiyoyi da waɗannan matsaloli.

Daɗewa ana kallo

Bara bulsho

Asalin hoton, Getty Images

Bincike ya nuna cewa yawan jin sauti da kallon bidiyo fiye da ƙima a shekarun farko na rayuwa na iya yin tasiri kan ɗabi'a da kuma tsarin ƙwaƙwalwar ɗan Adam.

Wannan bincike ya ƙara nuna yiwuwar tasirin da ya shafi halittar jiki a matakai biyu masu muhimmanci na ci gaban ɗan Adam, wato lokacin ƙuruciya da kuma lokacin samartaka.

Masu binciken sun kuma mayar da hankali kan wasu abubuwa uku da masu ƙirƙirar kafafen sada zumunta ke amfani da su wajen bambanta manhajojinsu.

  • Na farko shi ne bayanan masu amfani da manhajojin da abin da suke kallo
  • Ci gaba da kallon irin waɗannan bayanai ba tare bda son ya ƙare ba
  • Yanayin yadda mai kallo ke saurin wuce wani bidiyo

Algoritm na zaɓar bidiyoyi ga mutum ɗaya bayan ɗaya masu alaƙa, lamarin da ka iya ƙara tsawon lokacin da mutum ke shafe wa yana kallo ba tare da ya shirya yin hakan ba.

Shin ya kamata iyaye su damu?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shaidun da ake da su a yanzu ba su tabbatar a fili cewa yawan kallon gajerun bidiyoyi na tsawon lokaci na haddasa wata illa ta dindindin ga ƙwaƙwalwa ko kuma matsalar riƙe bayanai ba.

Sai dai binciken ya nuna wani muhimmin abu, inda ya nuna cewa yawan amfani da waɗannan bidiyoyi na da alaƙa da matsaloli daban-daban da suka shafi tunani, duk da cewa har yanzu ana buƙatar ƙarin bincike mai zurfi kan batun.

Wani babban malamin jami'a Van Bavel ya yi imanin cewa waɗannan sakamakon na nuna wani babban al'amari da ya kamata iyaye su ɗauka da muhimmanci, musamman idan amfani da manhajojin ya koma kallon bidiyo ba ƙaƙƙautawa na tsawon sa'o'i.

Sai dai binciken ya nuna cewa akwai wasu abubuwa da za su iya taimakawa wajen rage haɗarin, ciki har da samun yanayi mai kyau, tsarin amfani da na'urorin zamani, da kuma samun kyakkyawar fahimta da wayewa kan yadda ake amfani da fasahar zamani.

A ƙarshe, wataƙila tambayar da ta fi muhimmanci ba ita ce ko gajerun bidiyoyi kansu ba su da kyau ba, sai dai yadda ake amfani da su, yawan lokacin da matasa ke shafewa suna kallonsu, lokacin da suke kallonsu, abubuwan da suke maye gurbinsu da su, da kuma ko yadda aka tsara waɗannan manhajoji na sa mai amfani ya ci gaba da kallo ba tare da samun wata alama ta fili da ke nuna inda zai tsaya ba.

Babbar tambayar ita ce: Shin saurin kallon bidiyo ɗaya bayan ɗaya na iya sauya yadda ƙwaƙwalwa da mayar da hankali ke aiki? Har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike domin samun amsar wannan tambayar.