Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 28/00/2026

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. An gano ƙoƙon kai da ƙasusuwan mutum 28 a Abia

    Ƴansanda a Najeriya sun ce suna gudanar da bincike kan aƙalla mutum 28 da aka gano ƙoƙon kansu da ƙasusuwansu daga wasu sansanonin miyagu a dazuka da ke jihar Abia a kudu maso gabashin ƙasar.

    An gano gawarwakin ne yayin wani samame da Rundunar 'Yan Sandan Jihar Abia ta gudanar a yankin Isuochi na karamar hukumar Umunneochi, yankin da ya sha fama da satar mutane da sauran munanan laifuka.

    Kakakin rundunar ƴansandan jihar Maureen Chinaka ta ce ƴansanda sun gano ƙoƙon kawuna da ƙasusuwan mutum 28 daga sansanonin da ke dazukan Umuaku da Nneato.

    Masu bincike na zargin cewa ƙasusuwan na iya kasancewa na mutanen da aka sace, amma ana ci gaba da bincike domin tantance ko su wane ne da kuma yadda suka mutu.

    Jami'ai daga ɓangarori daban-daban na rundunar 'yan sanda ne suka shiga aikin, ciki har da sashen yaki da miyagun laifuka da sashen yaki da satar mutane da sashen yaki da kungiyoyin asiri, da sashen tattara bayanan sirri da sauran rundunoni na musamman.

    'Yan sanda sun ce sun kaddamar da samamen ne bayan samun bayanan sirri kan zargin ayyukan masu aikata laifi a dazukan.

    A cewar kakakin, zuwa yanzu ba a kama kowa ba yayin samamen saboda waɗanda ake zargi sun tsere kafin ƴansanda su isa sansanonin.

    Ƴansanda sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike yayin da kuma aka ƙara sa ido domin gano mutanen da suke tsere.

    Kwamishinan ƴansandan jihar Abia Wilfred Afolabi ya ce samamen wani ɓangare ne na yaƙin da ake na tarwatsa maɓoyar miyagu da kuwa yaƙi da matsalar tsaro a jihar.

    Gano ƙasusuwan na iya ƙara tayar da hankula game da ƙungiyoyin masu satar mutane da ke fakewa a dazukan da ke sassan kudu maso gabashin Najeriya, inda suke sace direbobi, matafiya da mazauna yankunan domin neman kuɗin fansa.

    A shekarun baya-bayan nan, hukumomi sun gano gawarwakin da suka fara ruɓewa a samamen da aka kai kusa da kasuwar shanu da kuma ake zargin suna da alaƙa da ayyukan masu satar mutane.

  2. Iran ta shigar da ƙorafi kan taƙaita zirga-zirgar jiragenta

    Shugaban Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Iran ya ce ƙasar ta aika da ƙorafi a hukumance ga Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (ICAO), kan takunkumin da aka ƙaƙaba wa harkokin sufurin jiragen saman Iran.

    Abouzar Shiroudi ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Iran, IRNA, cewa ƙorafin ya ƙunshi bayanai da ke bayyana matsayar Iran kan taƙaita zirga-zirgar jiragenta.

    Ya kuma ce kai hare-hare kan filayen jiragen sama da jirage babban misali ne na laifukan yaƙi a dokokin ƙasa da ƙasa.

    Ya ƙara da cewa Iran ta kuma gabatar da ƙorafi makamancin wannan ga kotun Hague.

    Tun bayan fara aiwatar da takunkumin Amurka kan kamfanonin jiragen saman Iran a makon da ya gabata, filayen jiragen sama a ƙasashe daban-daban sun soke zirga-zirgar jiragen kamfanonin Iran.

    Iraki da Georgia da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Azerbaijan da Oman, waɗanda suke daga cikin manyan wuraren da 'yan Iran ke zuwa da kuma hanyoyin da suke bi wajen wucewa zuwa Turai da Amurka, sun soke zirga-zirgar jiragen Iran sakamakon matsin lamba daga Amurka.

    Kamfanin dillancin labarai na Fars ya ce kamfanonin jiragen saman Iran na tattaunawa domin samar da sabbin hanyoyin zirga-zirgar jirage.

  3. Kwalara ta halaka 'fursuna shida' a Kano

    Fursunoni shida sun mutu sakamakon ɓarkewar cutar kwalara a wani gidan gyaran hali da ke arewacin Najeriya, a cewar ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da a yanzu suke neman hukumomi su ayyana dokar ta ɓaci kan lamarin.

    An soma ganin alamun ɓarkewar cutar makonni biyu da suka mutu lokacin da wani fursuna a gidan gyaran hali na Kurmawa a jihar Kano ya fara amai da gudawa, kamar yadda hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya ta bayyana.

    Hukumar ta ce gwajin da aka yi ya tabbatar da cewa kwalara ce kuma tuni ta tabbatar da mutuwar fursunoni biyu amma ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama na cewa waɗanda suka mutu sun kai shida a tsukin mako ɗaya.

    A baya-bayan nan ma, mutum 37 sun mutu a jihar Neja bayan an kulle su a ƙaramin ɗaki sakamakon kama su da aka yi bisa zargin haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba.

  4. Ƴanbindiga sun sace fiye da mutum 80 a Neja da Zamfara

    Fiye da mutum 80, akasarinsu mata sun ɓace bayan da ƴanbindiga suka ƙaddamar da hare-hare biyu da ƴanbindiga suka kai a wasu jihohin arewacin Najeriya a ranakun ƙarshen mako.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa a ranar Asabar, ƴanbindiga sun sace aƙalla manoma 47 yayin da suke gona a jihar Neja inda kuma a jiya Lahadi, aka yi garkuwa da mata 40 a jihar Zamfara.

    Ƴanbindiga na yawan kai munanan hare-hare kan ƙauyuka inda suke halaka mutane tare da ƙona gidajensu bayan sun sace musu dukiya.

    Wata majiya a jihar Neja ta ce manoma 47 galibinsu mata, an sace su a gonakinsu da ke Rimi a yankin Mariga na jihar Neja.

    Wani rahoton tsaro da aka shirya wa kungiyoyin jin kai, wanda AFP ta gani, ya tabbatar da faruwar hare-haren amma bai bayyana adadin mutanen da aka sace ba.

    Matan da aka sace jiya Lahadi an yi garkuwa da su ne a Yargada da ke Gusau a jihar Zamfara, a cewar wani rahoton tsaro da aka shirya wa Majalisar Dinkin Duniya, wanda AFP ta gani.

  5. Sojojin Amurka takwas sun ji rauni a harin Iran

    Kafar yaɗa labarai ta NBC ta ambato wasu jami'an gwamnatin Amurka uku na cewa sojojin ruwan ƙasar guda takwas sun ji rauni sakamakon harin makami mai linzami da Iran ta kai kan wani jirgin ruwa a Mashigar Hormuz.

    Majiyoyin uku sun shaida wa NBC cewa sojojin Amurka na cikin jirgin lokacin da Iran ta kai harin a ranar 14 ga Satumba.

    Ba su bayyana irin jirgin da aka kai wa harin ba, amma sun ce ba jirgin yaƙin Amurka ba ne.

    A yayin rikicin baya-bayan nan tsakanin Iran da Amurka, rundunar sojin Amurka da ke kula da yankin Gabas ta Tsakiya, CENTCOM ta ce wasu daga cikin hare-haren da ta kai martani ne ga ƙoƙarin Iran na kai hari kan jiragen ruwan Amurka.

    Sai dai rundunar ta ce babu wani jirgin yaƙin Amurka da ya samu lahani a waɗan nan hare-haren.

    A baya-bayan nan, wani kwamandan dakarun juyin juya halin Iran ya yi iƙirarin cewa dakarun ƙasar sun yi nasarar tarwatsa wani makami a saman wani jirgin Ruwan Amurka.

  6. Shettima ya koma Najeriya bayan taron UNGA

    Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya koma ƙasar bayan da ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a zauren babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da aka yi a New York da ke Amurka.

    Wata sanarwa da mai bai wa Shettima shawara kan yaɗa labarai, Stanley Nkwocha ya fitar ce ta tabbatar da komawar Shettima Najeriya.

    A cewar sanarwar, yayin bulaguron, Shettima ya gabatar da jawabi a taron na UNGA inda a nan Najeriya ta sake jaddada kiranta na kawo sauye-sauye a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya inda kuma ta nemi a bai wa wasu ƙasashen Afirka kujerar dindindin.

    A tsukin lokacin, Shettima ya gana da ƴan Najeriya mazauna ƙetare inda a zaman ya jaddada muhimmancin ƙwarewarsu da kuma alfanun da suke da shi ga ci gaban ƙasa.

    Komawar Shettima Najeriya na zuwa ne a daidai lokacin da Tinubu ya sake tsawaita hutunsa inda fadar shugaban ƙasar ta ce zai koma gida a makon da muke ciki.

  7. 'Ba lallai sai Tinubu yana Abuja ba ne zai yi aikinsa'

    Mai bai wa shugaban Najeriya, Bola Tinubu shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya ce ana sa ran shugaban ƙasar zai koma ƙasar cikin makonnan bayan da ya shafe makonni a Turai inda daga nan yake wanzar da ayyukan gwamnati.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Onanuga ya ce Shugaba Tinubu yana nan cikin ƙoshin lafiya kuma ya kasance yana tafiyar da harkokin gwamnati yayin da yake hutu.

    Ya ce ba lallai sai shugaban ƙasar ya kasance a Abuja ba ne zai iya sauke nauyin da ke kansa na shugabanci ba.

    Ya bayar da misali da taron da Tinubu ya yi da masu hannun jari a Faransa ciki har da rawar da ya ce shugaban ya taka wajen samar da wani shirin tashar jirgin ruwa ta dala biliyan 7 a Ogun wanda gwamnatin jihar ke jagoranta.

    Kalaman Onanuga na zuwa ne yayin da ɓangaren hamayya ke sukar yadda Tinubu ya ɗauki tsawon lokaci ba ya Najeriya da kuma ƙin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.

    Tinubu ya bar Najeriya ne ranar 30 ga watan Agusta domin hutun shekara na tsawon makonni uku inda ya fara zuwa birnin London kafin daga bisani ya je Paris a Faransa.

    Daga baya Fadar shugaban ƙasar ta sanar cewa Tinubu zai tsawaita hutun da ƴan kwanaki inda aka tsara zai dawo a ƙarshen makon da ya gabata.

    Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC Atiku Abubakar, ya ki yadda shugaban ya daɗe a wajen ƙasar ba tare da miƙa ragamar mulki ba.

    Shi ma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya taba sukar matakin Tinubu na yin hutunsa a Turai.

  8. Faɗa na ƙara tsananta a Yemen

    Ana ci gaba da gwabza ƙazamin faɗa a kusa da birnin Taiz a Yemen inda sojojin gwamnati da ke samun goyon bayan Saudiyya ke kokarin daƙile sabon farmakin da mayaƙan Houthi, waɗanda Iran ke mara wa baya, ke kai wa.

    Birnin Taiz yana wani yanki ne a tsakanin yankunan arewa da ke ƙarƙashin ikon ƙungiyar Houthi da kuma yankunan kudanci da ke hannun gwamnati.

    Wakiliyar BBC ta ce majiyoyi daga ɓangaren Houthi sun shaida wa BBC cewa suna shirin kai wani gagarumin farmaki.

    Amma sojojin gwamnati sun ce suna sane da wannan shirin kuma suma sun shirya daƙile shi.

  9. Hukumomi sun tsare mutum biyar kan zargin ta‘addanci a Birtaniya

    Hukumomi a Birtaniya sun tsare wasu mutum biyar bisa zargin aikata laifukan ta'addanci bayan wani lamari da ya auku a kusa da sansanin sojojin saman ƙasar da sojojin Amurka ke amfani da shi don kai hare-hare kan Iran tun watan Maris.

    Shugaba Trump ya ce mutanen sun shirya kai hari ne da zai haifar da mummunar ɓarna.

    Wakilin BBC ya ce mazauna yankin sun bayyana cewa an ƙara tsaurara matakan tsaro a kusa da sansanin sojan saman na Birtaniya.

    An fahimci cewa 'yan sandan da ke yaƙi da ta'addanci suna gudanar da bincike kan ko Iran tana da hannu a wannan lamarin.

  10. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye, BBC Hausa, barkan mu da safiya. Da fatan muna lafiya.

    A yau Litinin, kamar kullum, za mu kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Sai ku kasance tare da mu domin karanta wainar da ake toyawa a duniya. Akwai sauran shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk da X da Instagram inda za ku iya zuwa domin karanta ƙarin labarai da kallon bidiyo.