Jarumta da tarihin Ebola a fagen damben gargajiya

Dandambe
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Litinin aka yi zana'izar Abdurrazak Abdulmumin da aka fi sani da sula Ebola tsohon dan damben gargajiya da ya wakilci Kudu.

Ya rasu ne ranar Lahadi a babban birnin tarayya Abuja, bayan da ya sha fama da rashin lafiya daga baya ya ce ga garinku nan.

Ebola ya yi fice a fannin damben gargajiya a fadin Najeriya, ya kuma yi zamani a lokacinsa, wanda yake da ƙirar yan dambe gashi dogo ƙaƙƙarfa ga kwarjini da farin jini da barkwanci da iya mu'amala da mutane.

Wane ne Abdurrazak Ebola?

Abdurrazaq Ebola

Asalinsa iyayensa ƴan Sabon Birni ne a jihar Sokoto, waɗanda suka koma jihar Kaduna da zama, a nan ne suka haifi yara bakwai ciki harda Abdurrazak Ebola, sai dai tun yana ƙarami mahaifiyarsa ta rasu.

Abdurrazaƙ ya fara da sana'ar farauta ne, yayin da yayansa Dogon Auta ke buga dambe.

Yayan Ebola yana zuwa dambe, kuma Ebola na binsa, amma Dogon Auta sai yake korarsa baya son ya shiga damben gargajiya.

Sai da ya girma ne ya fara wasan ba tare da sanin yayan nasa ba.

Ebola ya fara ɗaukaka da fara dambe da Jamus, inda ya yi kisa biyu, sai kuma ya yi wasa da Ɗan Shagon Babangida Huntuwa fitaccen ɗan wasa, inda Ebola ya kashe shi daga nan aka fara labari cewar ga wani yaro ƙanin Dogon Auta ya fara dambe ya buge Ɗan Shagon Babangida.

Daga nan aka fara ce masa Bahagon Dogon Auta, hakan ya sa labari ya sauka wajen shugabanin Kudawa, inda suka gayyace shi gidan damben Dei-Dei da ke Abuja.

A can sai ya ci gaba da samun nasara a wasannin da yake bugawa yana buge yan dambe, ganin haka ƙungiyar dambe ta Abuja, ƙarkashin shugaba, Ali Zuma ta fara biyansa kuɗin abinci da wurin kwana, amma sai Aminu mai unguwa ɗaya daga shugaban ƙungiyar ƴan kallo ta Kudawa ya karɓe shi, domin kula da rayuwarsa.

Ta yaya ya samu sunan Ebola a harkar dambe?

Masu dambe

Bayan da Ebola ya ci gaba da dambe a Abuja, sai jarumtarsa ta ci gaba da fitowa, inda yake ta buge yan wasa daga Jamus da Guramaɗa.

Ɓangarorin Jamus da Guramaɗa sun riƙa gayyato ƴan wasansu shahararru zuwa Abuja domin a buge Ebola.

Daga nan aka fara tunanin sunan da za a sauya masa, maimakon Dogon Auta, sai kuma cutar Ebola ta ɓulla, daga nan mai gidansa Aminu mai unguwa ya nemi makaɗin ƴan dambe Autan Mai Turare da cewar ya kamata dogon Auta ya koma amsa Ebola.

Ebola ya ga bayan duk wanda suke zuwa dambe da shi, sannan ya ga bayan duk wani ɗan wasa daga Jamus, kai ɗaukakarsa ta ƙara fitowa ne a jihar Kano, saboda yawan damben da ya buga da wadanda ya kashe.

Wannan jarumtakarsa ta sa aka sa damben mota a jihar Kano a karon farko da aka sa mata damben gwamnan jihar Kano lokacin Abdullahi Umar Ganduje, kuma Ebola ne ya lashe gasar, ita ce motar farko da aka sa a dambe da ya zama zakara.

Jarumtar Ebola tsakanin ƴan dambe

dandambe

A cewar ɗaya daga cikin mai gidan Ebola, Aminu Mai Unguwa kamar yadda ya sanar da BBC, har lokacin da Ebola ya yi ritaya babu wani ɗan dambe daga Jamus da Ebola bai buge ba.

Ya fara lashe mota a damben gwamna da ya buga a Kano, bayan nasara a kan Bahagon Sanin Kurna.

Ya kuma ci mota a kan Bahagon Shagon Yansanda da kuma a kan Garkuwan Cindo a birnin Kebbi, bayan da Garkuwan Cindo bai je damben ba, haka kuma a birnin Kebbi an bashi kyauta mota a Adamawa ma wani mai kaunar Ebola ya bashi kyautar mota.

Bayan nan Ebola ya lashe lambar zinare a damben gargajiya da ya wakilci jihar Kano a wasannin kasa na Sports Festival da aka yi a Abuja.

Ya kuma yi yawan buga gasa a fadin Najeriya ya kuma fafata a wasan dambe na ƙasa da ƙasa. Shi ne dai ya fara cin mota a gasar damben gargajiya.

dandambe

Ebola ya taba aure, amma sun rabu da matar, amma ya mutu ya bar wata matar da ke masa takaba, amma bai taɓa haihuwa ba.

Duniyar damben gargajiya ba za ta taba mantawa da Abdurrazak Abdulmumin da ake kira Ebola ba, saboda jarumtar da ya yi a fagen wasan na gargajiya.