Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 21/09/2026

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.
  • Abin da ya janyo mutuwar matasa 37 a Neja - Bago
  • Aisha Aliyu Ja'afar
  • Tsadar farashin mai
  • Yadda sheikh Lukuwa
  • Hoto
  • Cyber Truck
  • Adeyemi Adeniyi
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman Minjibir da Imam Saleh

  1. 'Adadin sojojin Amurka da suka mutu a yaƙin Iran ya fi wanda ta sanar'

    hayaƙi

    Asalin hoton, UGC via Reuters

    Rahoton jaridar The Washington Post ya ce adadin sojojin Amurka da suka mutu a yaƙin Iran ya fi adadin da Ma'aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) ta bayyana a hukumance da aƙalla mutum huɗu.

    Jaridar ta ambato jami'an Amurka, a ranar Juma'a na cewa adadin sojojin Amurkan da suka mutu a yaƙin ya fi alƙaluman da Pentagon ta fitar a hukumance.

    Bisa ga rahoton, wanda ya dogara da bayanan wasu jami'ai biyar da ke da masaniya kan yawan waɗanda suka mutu daga Ma'aikatar Yaƙi ta Amurka, aƙalla sojoji 22 ne suka rasa rayukansu a yaƙin da Iran, adadin da ya fi wanda Pentagon ta bayyana a hukumance.

  2. Shugaban Yemen ya nemi taimakon Trump kan mayakan Houthi

    Mayaƙan Houthi

    Asalin hoton, Getty Images

    Majiyoyi da dama na cewa shugaban ƙasar Yemen da ƙasasshen yamma ke mara wa baya ya nemi taimakon shugaba Donald Trump na Amurka, daidai lokacin da tashin hankali ke ƙaruwa tsakanin dakarun gwamnati da ƴan tawayen Houthi.

    Majiyar ta ce Mr Trump bai yi alƙawarin taimaka wa shugaba Rashad al-Alimi da soji ba a tattaunawar da suka yi ta wayar tarho a jiya Lahadi.

    Gwamnatin Yemen da Saudiyya ke mara wa baya na iko da wasu yankuna na ƙasar, yayin da kaso mafi girma ke ƙarƙashin ikon ƴan tawayen na Houthi.

    Haka kuma Washington ba ta bi wa Saudiyya tabbacin taimaka ma ta a yaƙin da ke tsakanin ta Houthi, da ya ƙazance cikin kwanakin da suka gabata.

  3. Kafafen yaɗa labaran Amurka da dama sun daina ɗaukar rahotonnin White House

    Yawancin Kafafen yaɗa labaran Amurka sun janye daga ɗaukar rahotanni daga fadar White House, bayan uku daga cikinsu wato , CNN da Politico da MS NOW, sun shigar da ƙara gaban kotu kan gwamnatin Shugaba Donald Trump, bayan da aka hana ƴanjaridarsu shiga fadar White House domin ɗauko rahoto.

    A ranar Juma'a ne Shugaba Trump ya sanar da haramcin, yana zargin kafafen da wallafa abin da ya kira ƙagaggun labarai da ƙarairayi game da gwamnatinsa.

    Kafafen yada labarai na shirin ƙalubalantar matakin a gaban shari'a kan abin da suka kira tauye hakkin su na gudanar da aiki yadda ya dace kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba su dama, sannan ba gwamnati ce ke zaɓar abin da ƴan jarida za su bayar da rahoto a kai ba.

  4. Masu zanga-zangar adawa da matsalar tsaro sun toshe hanya a Neja

    UMAR BAGO

    Asalin hoton, UMAR BAGO

    Bayanan hoto, GWAMNAN NAIJA UMAR BAGO

    Mazauna ƙananan hukumomin Borgu da Agwara na Jihar Neja sun toshe hanyar Mokwa zuwa New Bussa a ranar Litinin, domin nuna adawa da hare-haren ta’addanci da ake ci gaba da kai wa al’ummominsu.

    Ƙungiyar Matasan Borgu Youth Federation ce ta jagoranci zanga-zangar, inda mambobin wasu ƙungiyoyi daban-daban da ke Masarautar Borgu, ciki har da mambobin Ƙungiyar Ma’aikatan Sufurin Hanya ta Ƙasar (NURTW), suka shiga cikin zanga-zangar.

    Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa masu zanga-zangar sun toshe hanyar ne a mahaɗar Bussa, wadda ke ɗaya daga cikin hanyoyin shiga Masarautar Borgu, tun da misalin ƙarfe 5:30 na asuba, duk da ruwan sama da ake yi.

    Rahotanni sun ce matafiya da ke tafiya zuwa New Bussa da Agwara daga yankin Mokwa sun makale a hanya.

    Shugaban Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja, Mohammed Nasir Abdullahi, ya shaida wa jaridar cewa an tura isassun jami’an tsaro zuwa ƙaramar hukumar domin hana sake kai hare-haren ta’addanci kan al’ummomin yankin.

    Ya ce tura jami’an tsaron ya biyo bayan roƙon da gwamnatin Jihar Neja ta yi wa Gwamnatin Tarayya, bayan da ’yan ta’adda suka kai hari kan wasu masallatan Juma’a a Dekara, Gbezhin, Sabon-Gida da Kpenya a ranar 21 ga Agusta, 2026, inda suka yi garkuwa da adadin masu ibadar da ba a bayyana ba.

  5. Ƴansanda sun kama mutum uku kan kisan mata a Afirka ta Kudu

    ..

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    An tsare mutum uku da ake zargi da hannu a kisan wata mata a wani yanki da ke gabashin Johannesburg a Afirka ta Kudu, inda a baya-bayan nan ake samun ƙaruwar cin zarafin mata a ƙasar.

    Ƴansanda sun bayyana kamen a matsayin wata babbar nasara ga binciken da hukumomi ke gudanarwa.

    Muƙaddashin babbar jami'in ɗansanda Leftanar Janar Puleng Dimpane ta ce jami'ai suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da adalci.

    Mutanen da aka kama za su bayyana gaban kotu yau Litinin.

    Afirka ta Kudu na ɗaya daga cikin ƙasashe a duniya da aka fi samun cin zarafin mata.

  6. Ƙokarin ganin an sake zaɓen Tinubu ne babban abin da na sanya a gaba - Wike

    .

    Asalin hoton, NYESOM WIKE

    Bayanan hoto, MINISTAN BABBAN BIRNIN NAJERIYA ABUJA, NYESOM WIKE

    Ministan Babban Birnin Najeriya Abuja, Nyesom Wike, ya sake jaddada cewa babban abin da ya fi ba wa muhimmanci a fagen siyasa a yanzu shi ne ganin Shugaba Bola Tinubu ya sake lashe zaben shugaban kasa a zaɓen 2027.

    Wike ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja, yayin da yake zantawa da manema labarai bayan duba wasu ayyukan tituna da ake ci gaba da gudanarwa a babban birnin tarayyar ƙasar.

    Ministan ya kuma yi watsi da zargin cewa an kafa gamayyar siyasar nan ta Rainbow Coalition, wadda yake da alaka da ita ne domin tarwatsa jam'iyyun siyasar da ake da su.

    Ya bayyana zargin a matsayin "maras tushe", yana mai cewa an kafa gamayyar ne domin hada mutane daga jam'iyyun siyasa daban-daban wadanda ke goyon bayan gwamnatin Shugaba Tinubu.

  7. Jihohin Najeriya da za su iya fuskantar ambaliyar ruwa a wannan mako

    xxx

    Hukumar kula da madatsun ruwa ta Najeriya (NiHSA) ta yi gargadin cewa za a iya samun ambaliyar ruwa a yankunan da ke bakin ruwa a jihohi 15 na ƙasar tsakanin ranar 19 zuwa 25 ga watan Satumban 2026.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun shugaban hukumar - Umar Mohammed - a cikin ƙarshen mako, ta bayyana cewa dubban matsugunai da makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya da kasuwanni da gonaki da wuraren ibada duk suna cikin haɗarin ambaliyar.

    A ranar Litinin 21 ga watan Satumba, jihar Legas wadda ke cikin jihohin da ake sa ran za su fuskanci ambaliyar ta gargadi mutanen da ke zaune a wuraren da ke cikin hadarin fuskantar ambaliyar ruwa su bar yankunan nasu zuwa tudun mun-tsira.

    Bayanin da hukumar NiHSA ta fitar ya nuna cewa jihohi 15 da za su iya fuskantar ambaliyar ruwan a wannan mako su ne:

    • Imo
    • Cross River
    • Delta
    • Ebonyi
    • Benue
    • Anambra
    • Akwa Ibom
    • Edo
    • Enugu
    • Bayelsa
    • Kogi
    • Abia
    • Taraba
    • Rivers
    • Lagos
  8. Shugaban Iran zai je New York yayin da Trump ya ce a shirye yake ya gana da shi

    Shugaban Iran

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Iran zai je birnin New York a ranar Talata domin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Sa’o’i kaɗan da suka gabata, Donald Trump ya ce a shirye yake ya gana da Masoud Pezeshkian, yana mai gargadin cewa idan ba a cimma yarjejeniya ba, Iran na iya fuskantar durƙushewar tattalin arzikinta ko kuma gagarumar barna.

    Ziyarar Masoud Pezeshkian zuwa shalkwatar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke New York ta janyo ce-ce-ku-ce.

    Wasu jiga-jigan masu ra’ayin mazan jiya, da ma wasu ’yan siyasa masu fafutuka da ke da alaƙa da wannan ɓangare ko kuma masu rajin kawo sauyi, sun nuna shakku kan ziyarar.

    Wasu masu sukar ziyarar sun ce, tun da aka ƙi ba wa tawagar kafafen watsa labarai ta shugaban Iran biza, ba zai yiwu a bayar da sahihan rahotannin ziyararsa ba.

    Bugu da ƙari, wasu masu ra’ayin mazan jiya na ganin cewa, la’akari da halin da ake ciki na yaƙi, halartar Iran na iya zama alamar cewa a shirye take ta shiga tattaunawa, lamarin da ka iya sanya ƙasar cikin raunin diflomasiyya.

    Sun kuma yi imanin cewa Fadar White House na iya kallon ziyarar a matsayin wani mataki na shirye-shiryen neman Iran ta yi rangwame.

    Sai dai masu goyon bayan gwamnati sun ce rashin halartar Iran babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya zai amfani Amurka ne, kuma yana da muhimmanci a ci gaba da samar da damar diflomasiyya.

  9. Rikicin Houthi na ci gaba da tilasta wa ƴan Yemen tserewa zuwa Afrika

    .
    Bayanan hoto, Ƴan gudun hijirar Yemen a Dijibouti

    Sabon rikicin da ya barke tsakanin 'yan tawayen Houthi na Yemen, da Iran ke marawa baya, da Saudiyya ya kara tsananta, lamarin da ya tilasta wa mutane da dama tserewa zuwa Djibouti.

    Dubban 'yan gudun hijira sun tsallaka Tekun Maliya mai cike da hadari, inda mafi yawansu suka isa garin Obock da ke arewacin Djibouti.

    Masu aiko da rahotanni sun shaida wa BBC cewa suna cikin tsoro da fargaba sakamakon hare-haren makamai masu linzami da bangarorin biyu ke kai wa juna.

    A kwanakin nan, jiragen yakin Saudiyya na ci gaba da kai wa mayakan Houthi hare-hare, yayin da mayakan ke mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan babban birnin Saudiyya, Riyadh, da tashar ruwan Yanbu.

  10. An kai wa jirgin dakon mai hari a mashigin Hormuz

    Jirgin ruwa

    Asalin hoton, Oman Maritime Security Centre

    Hukumar Kula da Tsaron Harkokin Jiragen Ruwa da kasuwancin teku ta Birtaniya (UKMTO) ta ce an kai hari kan wani jirgin dakon mai da wani makami mai linzami da ba a tantance ba, yayin da yake wucewa ta mashigin Hormuz.

    A cewar jami’an tsaro, biyu daga cikin ma’aikatan jirgin sun samu ƙananan raunuka, amma duk da haka jirgin ya ci gaba da tafiyarsa zuwa tashar jirgin ruwa da ya nufa.

    Ya zuwa yanzu, babu rahoton wata illa ga muhalli sakamakon harin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin harin da kuma waɗanda ke da hannu a ciki.

    UKMTO ta sake gargadin jiragen ruwa da ke wucewa ta yankin mashigin da su yi taka-tsantsan, tare da bayar da rahoton duk wani abu da ba a saba gani ba ga hukumomin tsaro.

  11. Sojoji sun ceto mutum 23 daga hannun ƴanbindiga a Sokoto

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojn da ke aiki ƙarƙashin rundunar Fansan Yamma a arewa maso yammacin Najeriya sun kuɓutar da mutum 23 da aka yi garkuwa da su inda kuma suka daƙile wasu hare-haren ta'addanci da kuma kama mutum huɗu da ake zargin ƴan ƙungiyar Lakurawa ne a wani samame na daban a sassan jihar Sokoto.

    Jami'in yaɗa labaran rundunar, Letanar Kanar Aliyu Danja ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da suka fitar yau Litinin.

    An kai samamen ne jiya Lahadi inda kuma aka yi nasarar ƙwato shanu shida da ake zargin ƴanbindiga sun sace.

    A ƙaramar hukumar Wurno, sojoji sun mayar da martani kan wani hari da aka kai kan Sabon Gari inda ƴanbindiga suka mamaye ƙauyen tare da buɗewa mazauna yankin wuta, lamarin da ya tilasta musu tserewa.

    Sojojin sun yi musayar wuta da maharan inda suka tilastawa maharan janyewa daga yankin, sun kuma ceto mutum shida da aka sace.

  12. Mutum 11 sun mutu bayan ruftawar mahaƙar zinare a Sudan

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an ceto sun duƙufa aikin gano mutanen da suke maƙale a ƙarƙashin ƙasa sakamakon ruftawar da wata mahaƙar ma'adanai ta yi har mutum 11 suka mutu, wasu aƙalla 30 kuma suka ji rauni a jihar Red Sea da ke Sudan.

    A cewar masu haƙar ma'adanan kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana, ibtila'in ya faru ne ranar Asabar da daddare.

    Zuwa yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka maƙale a ƙarƙashin ƙasa ba.

    Hukumar kula da ma'adanai a Sudan ta tabbatar da faruwar al'amarin sai dai ba ta fito ta bayyana adadin waɗanda abin ya rutsa da su ba.

    Wannan ne karo na biyu da ake samun ibtila'in da ya shafi mahaƙar zinare a Sudan cikin mako guda a jihar Red Sea bayan mutuwar wasu aƙalla 82 a jihar West Kordofan.

  13. Tinubu ya taya mai ɗakinsa murnar cika shekara 66 a duniya

    Tinubu da Oluremi

    Asalin hoton, Tinubu/X

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya taya mai ɗakinsa, Oluremi murnar zagayowar ranar haihuwarta inda take cika shekara 66 a duniya.

    Ya bayyana ta a matsayin babbar aminiyarsa kuma abokiyar shawara.

    Cikin wani saƙon taya murna mai ratsa zuciya kuma cike da kalaman soyayya, Shugaba Tinubu ya jinjinawa Oluremi bisa kasancewa tare da shi da haƙuri da kuma ƙarfafa masa gwiwa.

    A cewarsa, nauyin da ke kan wuyansa, a mafi yawan lokuta suna sauka ne a kafaɗun Oluremi yayin da take saurin fahimtar abubuwan da ke zuciyarsa ko da bai furta su ba.

    Tinubu ya ce "a yanayi na ƙalubale, na rashin sanin abin da gobe za ta haifar, kin kasance tare da ni kuma muna addu'a tare."

    Ya bayyana Oluremi a matsayin wadda ta fahimce shi sosai kuma sau da yawa tana saurin gane yana buƙatar shawara kafin ma na nema.

    Tinubu ya kuma yaba da sadaukarwarta ga iyalanta inda ya ce ƴaƴansu da jikokinsu sun taso ƙarƙashin inuwar addu'ointa kuma sun gaji kyawawan ɗabi'unta.

  14. ‘Mun sha fitsarinmu da gumin jikinmu saboda wahala’

    Bayanan bidiyo, ‘Mun sha fitsarinmu da gumin jikinmu saboda wahala’

    BBC ta samu damar shiga ɗakin da aka tsare matasa fiye da 30 da suka rasa rayukansu a hannun hukumar tsaro ta NSCDC.

    Wani da ya tsira ya bayyana mana irin mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.

    Gwamnati ta ce tana gudanar da bincike domin gano abin da ya yi sanadiyyar mutuwar matasan.

    Lamarin ya sa hukumomi dakatar da jami'ai 20 na hukumar bisa abin da ya faru a ranar Alhamis.

    Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana sunayensu a cikin wata sanarwa, inda ya bayyana matakan da gwamnatin tarayya ta fara ɗauka kan lamarin.

  15. Shettima ya isa New York don halartar taron UNGA

    ...

    Asalin hoton, Stanley Nkwocha/X

    Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya isa birnin New York da ke Amurka don wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da jagorantar tawagar Najeriya a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.

    Wannan ne karo na uku da Shettima yake wakiltar Tinubu a babban taron na UNGA.

    Mai bai wa mataimakin shugaban Najeriya shawara kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, a sanarwar da ya fitar a shafinsa na X, ya ce abubuwan da Najeriya za ta mayar da hankali a kai yayin taron za su kasance bisa muradun ƙasar, goyon bayanta ga haɗin gwiwar ƙasashe da kiraye-kirayen da Shugaba Tinubu ke yi na sake fasalin cibiyoyin duniya don su yi daidai da yanayin tattalin arziki da yawan al'umma na wannan zamani.

    "Saƙonmu a New York a bayyane yake. Najeriya ta yadda da haɗin gwiwa da ƙasashe amma dole ne masu gwamnati su zama wakilan kowa kuma masu adalci," in ji Shettima.

    Maitaimakin shugaban Najeriyar ya isa New York ne tare da gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara da ƙaramar ministar kasafi, Dr Doris Uzoka-Anite da sauran manyan jami'an gwamnati.

    A birnin na New York kuma, Shettima ya samu tarba daga gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ministar harkokin waje, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu da ministar harkokin mata, Hajiya Imaan Sulaiman Ibrahim da sauran manyan jami'an gwamnati da na diflomasiyya.

    A babban taron na UNGA, Shettima zai gabatar da jawabi inda zai bayyana matsayar Najeriya kan muhimman batutuwan da suka shafi duniya musamman kan zaman lafiya da kuma tsaro, ci gaba da bunƙasar tattalin arziki da kuma haɗin gwiwar ƙasashen duniya.

    ...

    Asalin hoton, Stanley Nkwocha/X

    ...

    Asalin hoton, Stanley Nkwocha/X

  16. Za mu bai wa duniya mamaki idan Amurka ta sake kai mana hari - Iran

    Rundunar juyin juya halin Iran ta yi gargaɗi cewa idan har Amurka ta kuskura ta kai wa ƙasar hari, Iran za ta yi amfani da sabbin makamai tare da faɗaɗa yaƙin zuwa wasu yankunan da ba a kai wa hari ba.

    Kakakin IRCG, Hossein Mohebi ya ce idan dai har Amurka ta yi gangancin sake kai hari a Iran, to Iran ɗin kuwa za ta bai wa duniya mamaki.

    A cewarsa, Iran ta ƙera makamai tare da bunƙasa wasu dabarun yaƙi waɗanda ba ta yi amfani da sub a a yaƙin da ake a yanzu.

    Ya kira makaman a matsayin „makaman dabarun yaƙi” waɗanda Iran za ta yi amfani da su “idan buƙatar hakan ta taso” kuma “duniya za ta ga abin da zai faru”.

  17. Amurka da China sun tattauna kan matsalolin AI

    Scott Bessent da He Lifeng

    Asalin hoton, Treasury Secretary Scott Bessent/X

    Sakataren Baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya ce Amurka da China sun tattauna wani shiri na haɗin gwiwa wajen faɗakarwa akan matsalolin da suka shafi ƙirƙirarriyar basirar AI.

    Mista Bessent ya bayyana cewa, ƙarƙashin wannan shiri, ƙasashen biyu za su iya sanar da juna idan aka samu wani lamari da ya shafi AI wanda zai iya zama barazana ga tsaron ƙasarsu.

    Ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da Mataimakin Firaministan China, He Lifeng, a birnin New York.

    Tattaunawar sharar fage ce ga ganawar da ake sa ran shugabannin Amurka da China za su yi a mako mai zuwa a Fadar White House.

    Ko da yake babu wata sanarwa daga gwamnatin China game da tattaunawar, a baya dai shugaba Xi Jinping na China ya yi kira da a samar da wani tsari na ƙasa da ƙasa da zai rinka sanya idanu a kan harkokin ƙirƙirarriyar basira ta AI.

  18. An miƙa mutum 18 ga Amurka kan zargin hannu a kisan Shugaba Moise

    Haiti ta kasance tana fuskantar matsalar ƴan daba tun bayan kisan gillar da aka yi wa Shugaba Jovenel Moise

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Bayanan hoto, Haiti ta kasance tana fuskantar matsalar ƴan daba tun bayan kisan gillar da aka yi wa Shugaba Jovenel Moise

    Jami’an Amurka sun ce an tafi da mutane 18 da ake zargi da hannu a kisan tsohon shugaban ƙasar Haiti, Jovenel Moïse, shekaru biyar bayan kisan nasa zuwa jihar Florida domin fuskantar shari’a.

    Wakilin BBC ya ce an miƙa wasu tsoffin sojojin Colombia 17 da kuma wani babban jami'in gwamnatin Haiti ga gwamnatin Florida domin su fuskanci tuhuma kan kisan tsohon shugaban ƙasar na Haiti.

    Ana zargin waɗannan mutanen da hannu a kisan tsohon shugaban ƙasar Jovenel Moïse, wanda aka harbe har lahira a gidansa da ke birnin Port-au-Prince a shekarar 2021.

    An harbe Mista Moïse har lahira a gidansa da ke birnin Port-au-Prince ne wanda wata ƙungiyar masu ɗauke da makamai, yawancinsu waɗanda ake zargin ‘yan Kolombiya ne suka aikata.

  19. 'Za a rushe gini sama da 250 da hare-haren Isra'ila suka lalata a Gaza'

    Falasɗinawa suna aiki a ɗaya daga cikin gine-ginen da hare-haren Isra'ila suka lalata a Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Falasɗinawa suna aiki a ɗaya daga cikin gine-ginen da hare-haren Isra'ila suka lalata a Gaza

    Jami’ai a Gaza sun sanar da shirye-shiryen kwashe mutane tare da rusa fiye da gine-gine 250 da hare-haren da Isra’ila ta kai suka lalata, saboda fargabar cewa za su iya ruftawa a kowanne lokaci.

    An ɗauki matakin sakamakon yawaitar rushewar gine-ginen da suka lalace ciki har da wani gini da ya rufta a ranar Laraba, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa 21.

    Sai dai hukumomin sun yi gargaɗin cewa shirin na fuskantar manyan ƙalubale, ciki har da ƙarancin manyan injinan aikin gini saboda killace yankin da Isra’ila ta yi, da kuma rashin isasshen fili da za a tsugunnar da waɗanda suka rasa matsugunansu.

    Wakiliyar BBC ta ce ma’aikatar kula da gidaje ta Gaza ta bayyana kusan gine-gine 3,000 a matsayin masu matuƙar haɗari, saboda irin ɓarnar da suka yi fama da ita a yaƙin da ake yi tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hamas.

  20. Salam Alaikum!

    Masu bin mu a wannan shafi na Kai Tsaye da BBC Hausa ke kawo muku a kowace rana, barka da warhaka.

    Da fatan mun wayi gari lafiya. Kamar kodayaushe, a yau ma za mu ci gaba da kawo maku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a duniya - musamman a Najeriya da ƙasashe maƙwabta.

    Za ku iya garzayawa shafukanmu na sada zumunta – Fesbuk da X da kuma Instagram inda a nan ma muka wallafa ƙarin labarai da bidiyo.

    Sai ku kasance tare da mu.