Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutumin da ya kai gawar ƴar'uwarsa banki don nuna shaidar ta mutu
- Marubuci, Rakhi Ghosh and Nikita Yadav
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hindi and BBC News
- Lokacin karatu: Minti 5
Gargaɗi: Wannan labari na ƙunshe da bayanai masu tayar da hankali
Wani mutum a gabashin ƙasar Indiya ya ce wahala da yake sha wajen neman cire kuɗin ƴar'uwarsa da ta mutu daga banki, ta tursasa masa zaƙulo rage-rage ƙasusuwanta domin nuna wa banki shaidar cewa ta mutu da gaske.
Wani bidiyo da aka riƙa yaɗawa daga jihar Odisha, inda mutumin mai suna Jitu Munda, mai shekara 52 ke zama, ya nuna shi ɗauke da ƙwarangal ɗin matar lokacin da yake tafiya kan titi zuwa banki a cikin makon nan.
Bidiyon ya haifar da muhawara tsakanin al'umma.
Mutumin ya ce ya yi hakan ne sanadiyyar takaicin da ya shiga bayan banki ya ƙi ba shi kuɗin marigayiyar, inda suka nace kan dole sai ya gabatar da ƙwaƙƙwarar hujjar cewa ta mutu.
Ƴansanda sun ce mutumin ya zaƙulo gawar matar sannan ya kai ta bankin.
Hukumomin bankin sun musanta cewa sun buƙace shi ya kawo gawar, inda suka ce an buƙace shi ne ya kawo takardun da za su tabbatar cewa matar ta mutu.
Bankin ya ce da alama mutumin ya yi hakan ne saboda ya jahilci matakan da ake bi wajen amsar kuɗaɗen mamaci daga banki, sannan a halin yanzu an riga an miƙa kuɗaɗen.
Haka nan bankin ya musanta wasu daga cikin kalaman Munda.
Lamarin da ya faru a yankin Keonjhar a ranar Litinin ya janyo hankalin mutane sosai a faɗin ƙasar Indiya, inda mutane da dama ke zargin hukumomi da kuma bankin da ƙin taimaka wa mutumin.
Ministan harkokin kuɗaɗen shiga na jihar Odisha, Suresh Pujari ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin, kuma ya ce za a ɗauki mataki a kan shugaban bankin yankin bisa zargin nuna rashin ƙwarewar aiki.
Gwamnatin yankin Keonjhar ta nuna "matuƙar damuwa", inda ta ce tana matuƙar bayar da muhimmanci ga kare haƙƙi da martabar al'umma.
Munda ya shaida wa sashen harshen Indiya na BBC cewa lamarin ya samo asali ne bayan mutuwar yayarsa mai shekara 56 mai suna Kalara, wadda ta mutu a cikin wannan shekarar.
Kafin mutuwarta tana yin wani ƙaramin aiki ne inda ake biyan ta a kullum, daga nan sai ta koma ƙauyensu bayan mutuwar mijinta da ɗansu, in ji Munda.
Ya ƙara da cewa ƴan watanni kafin mutuwarta, sai ta sayar da dabbobin da ta mallaka, inda ta haɗa kuɗi rupee 19,000 (naira 279,937) ta ajiye a asusunta na banki.
Munda ya ce ya ziyarci bankin a lokuta da dama a ƙoƙarin ganin an ba shi kuɗin da marigayiyar ta bari, amma abin ya ci tura.
"A lokacin da manajan bankin ya ƙi sauraro na, ya nace kan cewa dole sai na kawo shaidar cewa ta mutu, sai abin ya ba ni haushi," in ji Munda.
Ya ƙara da cewa "shi ya sa na kawo ƙwarangwal ɗinta domin tabbatar musu da cewa ta mutu."
Bidiyon da aka riƙa yaɗawa ya nuna shi ɗauke da rage-ragen ƙasusuwa da aka nannaɗe da buhu yana kan hanya zuwa bankin, sannan da ya isa ya ajiye ta a ƙofar shiga bankin. Babu tabbas kan ko wane ne ya ɗauki bidiyon.
Bayan yaɗuwar bidiyon ne mutane suka riƙa tsokaci kan tsauraran sharuɗɗan da ake gindayawa kafin iyali ko ƴan'uwa su karɓi kuɗaɗen mamaci bayan mutuwarsa, musamman idan mamacin bai sanya sunan ƴan'uwan a cikin magadansa da za su karɓi kuɗin ba.
Wasu kuma sun riƙa tsokaci kan wahalar da mazauna karkara ke sha wajen hulɗa da banki.
A ƙasar Indiya wajibi ne iyali su gabatar da takardu, kamar shaidar mutuwa da shaidar gado kafin banki ya sakar musu kuɗin da mamaci ya bari - wani mataki da ke ɗaukar dogon lokaci, musamman idan abin ya haɗa da mutanen karkara waɗanda ba su da wayewa kan samun irin waɗannan takardu.
Bayan lamarin da ya faru, bankin mai suna Indian Overseas Bank, wanda shi ne ke kula da bankin da lamarin ya faru da ake kira Odisha Grameen Bank ya ce babu gaskiya a zargin da ake yi cewa ma'aikatan bankin sun buƙaci mutumin ya kawo gawar marigayiyar.
Bankin ya ce an sanar da Munda duk matakan da ake bi wajen karɓar kuɗin, amma ya gaza cika ƙa'idojin.
Haka nan bankin ya ce mutumin ya je bankin ne a cikin wani "birkitaccen yanayi" sannan kuma ya yi ƙoƙarin tayar da hankali, inda daga baya ya wuce, kafin ya sake dawowa ɗauke da ƙasusuwan marigayiyar, lamarin da suka ce ya tayar da hankali.
Shugaban reshen bankin na yankin Sushant Kumar Sethi ya shaida wa BBC Hindi cewa da farko Munda ya shaida musu cewa ƴar'uwar tasa na fama ne da matsalar shanyewar arin jiki shi ya sa ba za ta iya zuwa bankin da kanta ba, inda ma'aikatan bankin suka ce za su je gida su gan ta. Sai daga baya ya ce musu ta mutu.
Sethi ya kuma musanta batun cewa Munda ya je banki sau da yawa kan lamarin, ya ƙara da cewa Munda bai je bankin ba a cikin wata biyu da suka gabata, kuma akwai wasu magadan nata da suka je bankin suna iƙirarin cewa su ne ke da haƙƙin karɓar kuɗin, wanda hakan ya sanya aka buƙaci ganin takardun shaida.
Daga baya ƴansanda da kuma ma'aikatan ƙaramar hukuma sun yi nasarar shawo kan Munda domin mayar da ƙwarangwal ɗin matar maƙabarta, inda suka tabbatar masa cewar za a biya masa buƙatarsa.
Hukumomi sun kuma ba shi tallafin kuɗi rupee 30,000, wato kimanin naira 434,000.
Ya zuwa ranar Laraba, hukumomi sun ce an ba shi takardar shaidar mutuwar ƴar'uwar tasa da duk wasu takardu da ake buƙata, sannan kuma bankin ya ce ya miƙa kuɗin ga iyalan marigayiyar.