Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waɗanne ƴan wasan Afirka ne za su haska a gasar cin Kofin Duniya?
- Marubuci, Ahmad Bawage
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
An ɗauki tsawon lokaci ana dama wa da ɓangaren kwallon kafa a Afirka, musamman ma lokacin gasar cin Kofin Duniya, inda ƴan wasa irinsu Roger Milla, Jay-Jay Okocha, Samuel Eto'o da kuma Asamoah Gyan suka assasa sunayensu a tarihi.
A baya-bayan nan kuma, tawagar Moroko ta nuna bajinta da kuma iya taka leda abin da ya kai ta har wasan kusa da karshe a gasar cin Kofin Duniya na 2022 a Qatar.
Yayin da gasar Kofin Duniya ta bana da za a yi a Amurka wadda ita ce mafi girma a tarihi da ƙasashe 48 za su fafata, ciki har da ƙasashen Afrika goma ke karatowa – hankali ya koma kan ƴan wasan da za su baje-kolinsu a gasar da ke tafe.
A wannan maƙala, mun yi duba kan wasu ƴan wasan Afirka da za su fi haskawa a gasar a Amurka.
Mohamed Salah – Masar
Mohamed Salah ya shafe shekara tara a Liverpool, inda ya shiga sahun ƴan wasan ƙungiyar mafi hazaka a tarihi.
Ya lashe Champions League a 2019 da kuma gasar Premier biyu – Ya kuma lashe kyautar ɗan wasan da ya fi zura kwallaye har sau huɗu.
Iya cin kwallo da kuma sarrafa ta cikin salo mai ban sha'awa na cikin abubuwan da suka mamaye rayuwarsa ta kwallon kafa.
Tasirinsa ya zarce har zuwa tawagar ƙasarsa ta Masar, inda ɗan wasan mai shekara 33 ke jagorantar ƙasar a kowane lokaci da kuma zura kwallaye.
Zai kasance ɗan wasan da Masar za su fi saka fatansu a kansa wajen samun nasara a gasar ta Kofin Duniya a Amurka.
Brahim Diaz – Moroko
Duk da cewa bai samu damar buga gasar Kofin Duniya ta 2022 ba, Diaz wanda asalin haifaffen Sifaniya, ya zama cikin ƴan wasa da tawagar Moroko ta Atlas Lions ke alfahari da su.
Ya taka rawar gani sosai a gasar cin Kofin Afirka da aka yi a Moroko, inda ya zura kwallaye biyar.
Kuma ya ci gaba da nuna ƙwarewa da iya taka leda a ƙungiyarsa ta Real Madrid, inda yake haska wa kowane lokaci ya samu dama.
Yana ɗaya daga cikin ƴan wasan Afirka da ake ganin tauraruwarsu za ta haska a Amurka a watan Yuni.
Lyle Foster – Afirka ta Kudu
Foster ɗan wasa ne mai ƙarfin gaske wanda ke takurawa ƴan wasa, ya kuma iya shiga yadi na 18 yadda ya kamata da sarrafa kwallo.
Ɗan wasan na ƙungiyar Burnley ya iya zura kwallo a raga kuma ba ya wasa da dama.
Ɗan wasan mai shekara 25, wanda ya fara bug kwallo a ƙungiyar Orlando Pirates, ya zama ɗan wasan gaba da Afirka ta Kudu ta fi ji da shi a yanzu.
Sadio Mane – Senegal
Duk da barinsa ɓangaren kwallon kafar Turai, tasirin Mane a tawagar Senegal bai ragu ba ko kaɗan.
Ɗan wasan ƙungiyar Al Nassr ya zama jagora a Senegal, inda ya zura kwallaye biyar a lokacin wasannin neman gurbi, abin da ya taimaka wa tawagar Lions of Teranga zuwa gasar kofin duniya karo na huɗu – kuma na uku a jere.
Mane mai shekara 34, ya ci gaba da haska wa a ƙungiyarsa, inda ya ci kwallo da kuma taimaka a ci har sau 19 a dukkan wasanni a kakar bana.
Amad Diallo - Côte d'Ivoire
Ɗan wasan gaban mai shekara 23, ya iya amfani da damarsa wajen zuwa kwallaye masu ƙayatarwa – kuma yawancin kwallayensa na jawo nasara a ƙungiya da kuma ƙasarsa.
Ya zura kwallaye uku a gasar cin Kofin Afirka na 2025 da aka yi a Moroko a watan Janairu, duk da cewa tawagar Elephants ta fice daga gasar a matakin kwata-fainal.
Amad ya zama ɗan wasa mai muhimmanci ga Manchester United, inda yake zura kwallo da taimakawa a ci da kuma ƙoƙari wajen tsare gida.
Hannibal Mejbri – Tunisia
Ɗan wasan na tsakiya Mejbri ya zama na daban saboda ƙwarewa wajen iya sarrafa kwallo da kuma riƙe kwallo lokacin matsi yadda ya kamata.
Ga kuma bayar da kwallo ga ƴan wasan gaba cikin sauki.
Mejberi ɗan shekara 23 ya zama ɗan wasa mai muhimmanci ga tawagar Tunisiya.
Ya taɓa buga wa Faransa a matakin matasa, kafin ya komawa Tunisiya kacokan a 2021.
Antoine Semenyo – Ghana
Komawar Semenyo zuwa Manchester City daga Bournemouth a watan Janairu ya canza shi zuwa wani ɗan wasa na daban a fagen kwallo.
Ɗan wasan mai shekara 26 yana buga wa kowane ɓangare a gaba, wanda abu ne da ya ƙara nuna ƙwarewarsa da kuma muhimmancinsa ga ƙungiyarsa.
Hakan ya sa Semenyo zama ɗaya daga cikin ƴan wasan gaban tawagar Black Stars mafi ƙwazo.
Ghana na fatan zai taimaka musu a gasar kofin duniya da za a yi a Amurka.
Amine Gouiri – Aljeriya
Ɗan wasa Gouiri ya bayyana cewa bai damu da sai ya ci kwallo ba, abin da kawai yake so shi ne taimaka wa abokan wasansa wajen samun nasara.
Duk da haka, ya taimaka wajen cin kwallaye da kuma bayar a ci ga ƙungiyarsa ta Marseille a kakar bana.
Duk da cewa ya buga wa Faransa a matakin matasa, Gouiri ya zaɓi komawa tawagar Desert Foxes domin buga kwallo.
A cikin shekara biyu da rabi, ya ci kwallo kuma ya taimaka an ci har sau 12 a wasanni 21 da ya buga wa Aljeriya.
Wannan ne ya sa ake ganin zai haska sosai a Amurka.