Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa daga 26 ga Afirilu zuwa 1 ga watan Mayun 2026

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga Lahadi 26 ga watan Afirilu zuwa Juma'a 1 ga watan Mayun 2026.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. An kafa tarihi!, PSG 5-4 Bayern Munich

    Wannan ne wasan kusa da na ƙarshe na gasar Champions League da aka fi zura ƙwallo a tarihi.

    Ya yi daidai da wasan Rangers da Eintrancht Frankfurt a zamanin da ake buga gasar European Cup, inda aka tashi wasan Rangers 3-6 Eintracht Frankfurt a kakar wasa ta 1959-60

  2. AN TASHI WASA: PSG 5-4 Bayern Munich, PSG 5-4 Bayern Munich

    An tashi wasa PSG na gaba da ƙwallo ɗaya.

    Akwai sauran kallo a falle na biyu!

    Wannan ne karon farko da PSG ta doke Bayern Munich tun daga 7 ga watan Afrilun 2021.

    Magoya bayan Bayern Munich sun miƙe tsaye domin jinjina wa ƴan wasansu waɗanda suka yunƙuro bayan an danna su ƙasa.

    Daga 5-2 suka yunƙura aka tashi 5-4.

  3. , PSG 5-4 Bayern Munich

    Bayern na dannawa, tana son ta samu ƙwallo ta biyar kafin a tashi.

    Bayern ta cire Aleksandar Pavlovic ta sako Nicolas Jackson.

  4. An ƙara minti huɗu, PSG 5-4 Bayern Munich

  5. , PSG 5-4 Bayern Munich (Minti 89)

    Achraf Hakimi ya ja ƙwallo da gudu sai kuma kawai ya tsaya ya riƙe cinyarsa.

    Wannan ba abu ne da PSG za ta ji daɗi ba.

  6. PSG ta yi canjin ƴan wasa, PSG 5-4 Bayern Munich (Minti 85)

    An sako Lucas Hernandez da Senny Mayulu, an cire Khvicha Kvaratskhelia da Nuno Mendes.

  7. An shiga minti 10 na ƙarshe!, PSG 5-4 Bayern Munich (Minti na 81)

    Mene ne kuma za mu gani kafin a tashi wannan wasa?

  8. Hakimi ya samu kati, PSG 5-4 Bayern Munich (Minti na 80)

    Shi ma Achraf Hakimi ya kamu katin gargaɗi.

  9. Canjin ɗan wasa, PSG 5-4 Bayern Munich (Minti na 79)

    Bayern ta cire Jamal Musiala ta sako Leon Goretzka.

  10. Katin gargaɗi, PSG 5-4 Bayern Munich (Minti na 78)

    Michael Olise na ta wahalar da ƴan PSG har ta kai ga Fabian Ruiz ya samu katin gargaɗi.

  11. , PSG 5-4 Bayern Munich

    Abin ba a cewa komai, wannan wasa sai wanda ya gani.

  12. ƘWALLO A RAGA: PSG 5-4 Bayern Munich, Luis Diaz (Minti na 68)

    Da farko ba a bayar da ƙwallon ba amma daga baya an ce ta ciyu.

    Liuz Diaz daga gefe ya jefa ƙayatacciyar ƙwallo ta gefen ƙarfen raga bayan samun fasin daga Harry Kane.

    Yanzu wasa 5-4!!

  13. , PSG 5-3 Bayern Munich

    An zura ƙwallo TAKWAS, ga shi kuma akwai sauran mintuna 25 kafin a kammala wasa.

  14. ƘWALLO A RAGA: PSG 5-3 Bayern Munich, Dayot Upamecano (Minti na 65)

    An saka wata ƙwallo!

  15. Canjin ɗan wasa, PSG 5-2 Bayern Munich

    PSG ta cire Warren Zaire-Emery ta sako Fabian Ruiz.

  16. ƘWALLO A RAGA: PSG 5-2 Bayern Munich, Ousmane Dembele (Minti na 59)

    Wasa ya ƙare!

    Bayern na dannawa gaba amma da alama abin da PSG ke so kenan.

    Desire Doue ya jefa wa Ousmane Dembele ƙwallo daga nesa, ya wuce mai tsaron baya Dayot Upamecano ya jefa ƙwallo a raga.

  17. ƘWALLO A RAGA: PSG 4-2 Bayern Munich, Khvicha Kvaratskhelia (Minti na 56)

    PSG suna da kyau!

    An mayar wa Neuer da ƙwallo amma ba yadda ya dace ba, sai kawai ya buga ƙwallon waje amma sai ta faɗa ƙafar Achraf Hakimi, shi kuma ya tura ƙwallo zuwa ƙafar Khvicha Kvaratskhelia inda shi kuma nan take ya ƙarasa da ita cikin raga.

  18. Bayern ba ta nuna gajiyawa, PSG 3-2 Bayern Munich

    Bayern na nuna dagiya. Sun tsare baya kuma suna danna PSG.

  19. PSG ta kai kora, PSG 3-2 Bayern Munich )Minti na 53)

    Ousmane Dembele ya kai kora mai kyau inda hakan ya jefa Manuel Neuer cikin razani.

  20. , PSG 3-2 Bayern Munich

    Za mu ga yadda za ta kaya a wannan yanayi bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

    PSG za ta iya tunanin ita ce za ta samu nasara, ita kuma Bayern za ta yi ƙoƙarin ganin an tashi tana sa ran zuwa wasan ƙarshe.