Morocco da Senegal na jiran hukucin kotu kan kofin Afcon

Sadio Mane ɗauke da kofin Afcon
Bayanan hoto, Sadio Mane ne ya lashe kyautar ɗan wsan da ya fi taka rawa a gasar Afcon ta 2025
    • Marubuci, Ian Williams
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Kowa ya san cewa wasan ƙwallon ƙafa ya kamata ya ɗauki minti 90, amma wasan ƙarshe na gasar Kofin Nahiyar Afirka ta 2025 (AFCON) ya shafe watanni 10 ana taƙaddama a kansa.

Yanzu dai, a ƙarshe za a ayyana ko Moroko ko kuma Senegal zakarar gasar. Sai dai wannan lokacin farin ciki ba zai zo ne a filin wasa ba, sai a kotu.

A ranar Talata da rana, babbar kotun warware rikice-rikicen wasanni ta duniya (CAS), za ta yanke hukunci kan ƙarar da Senegal ta ɗaukaka kan matakin da aka ɗauka na ƙwace mata kofin da ta lashe a watan Janairu bayan ta doke mai masaukin baki, Moroko, a Rabat.

An saurari shari'ar ne a farkon watan Oktoba, kuma yanzu jiran sakamakon ake yi.

To amma ta yaya aka kai wannan mataki?

Me ya faru a wasan ƙarshe na Afcon?

A gaban magoya baya 66,000 da suka cika filin wasa na Prince Moulay Abdellah, suna, Moroko ta nemi lashe kofin AFCON na farko tun bayan shekarar 1976.

Sai dai wasan ƙarshe ya rikiɗe zuwa rudani a ƙarshen ƙarin lokacin.

Yayin da ake 0-0, Senegal ta yi zaton cewa Ismaila Sarr ya zura ƙwallon da za ta tabbatar mata da nasara a mintunan ƙarshe. Amma sai kwatsam alƙalin wasa Jean Jacques Ndala busa 'foul' ya bai wa Moroko bugun tazara.

Takaddamar ta ƙara kamari a minti na 98 lokacin da Ndala ya bai wa Moroko bugun fenariti da taimakon na'urar VAR.

Rikici ya ɓarke a gefen fili da kuma wuraren zaman magoya baya. Kocin Senegal, Pape Thiaw, ya buƙaci wasu daga cikin 'yan wasansa da jami'an tawagar su bar fice daga filin, yayin da wasu magoya baya suka yi arangama da jami'an tsaro bayan doka da oda sun ɗan lalace na wani lokaci.

Daga bisani dai an ci gaba da wasan, kuma a minti na 124 Moroko ta samu babbar damar bai wa Morocco nasara. Sai dai Brahim Diaz ya kasa cin gajiyar bugun fenaritin da ya samu, inda ya yi ƙoƙarin zura ƙwallon ta salon "Panenka", amma golan Senegal Edouard Mendy ya kama ta cikin sauƙi.

Daga nan ne Pape Gueye ya zura ƙwallon da ta bai wa Senegal nasara da ci 1-0 a ƙarin lokaci, lamarin da ya sa ta ɗaga kofin AFCON karo na biyu a tarihinta.

Ko kuma aƙalla, hakan ne abin da suka yi zaton ya faru.

Me ya sa aka sauya sakamakon?

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Moroko (FMRF) ta yi gaggawar shigar da ƙorafi ga Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF), tana mai cewa Senegal ta saɓa wa dokokin gasar.

Sashe na 82 a dokokin gasar, wanda ke cikin babi mai taken "Janyewa daga Gasar", ya tanadi cewa: "Idan, saboda kowanne dalili, wata ƙungiya ta ƙi ci gaba da wasa ko kuma ta bar filin wasa kafin ƙarshen wasan ba tare da izinin alkalin wasa ba", za a ɗauke ta a matsayin wadda ta yi rashin nasara kuma za a fitar da ita daga gasar da ake ciki.

A watan Maris, kwamitin ɗaukaka ƙara na CAF ya amince da hujjar Moroko, inda ya yanke hukuncin cewa Senegal ta yi rashin nasara saboda barin fili, tare da bai wa Moroko nasara da ci 3-0.

Duk da cewa akwai lokuta a baya da CAF ta sauya sakamakon wasanni a neman gurbin gasar AFCON da kuma Kofin Duniya, wasu mutane, ciki har da wani tsohon babban jami'in CAF, sun yi jayayya cewa alƙalin wasa ne kaɗai ke da ikon dakatar da wasa idan wata ƙungiya ta fice daga fili.

Hukumar ƙwallon ƙafar Moroko ta bayyana cewa abin da take nema shi ne a aiwatar da dokokin gasar yadda ya kamata. Amma ita kuwa Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Senegal ta bayyana hukuncin a matsayin "wanda bai dace ba da wanda ba a taɓa gani ba kuma ba za a amince da shi ba", sannan ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Sasantawa ta Wasanni (CAS).

Magoya bayan Senegal na rikici da jami'an tsaro
Bayanan hoto, Magoya bayan Senegal na rikici da jami'an tsaro

Menene Kotun Sasantawa ta Wasanni (CAS)?

An kafa Kotun Sasantawa ta Wasanni (CAS) a shekarar 1984, kuma hedkwatarta na birnin Lausanne da ke ƙasar Switzerland. An ƙirƙire ta ne a matsayin wata hukuma mai zaman kanta ta shari'a domin sasanta rikice-rikicen wasanni, musamman yayin da harkokin wasanni suka ƙara tashe da kuma yawaitar shari'o'in da suka shafe su.

Ga hukumomin wasanni da suka amince da ikon CAS, ana ɗaukarta a matsayin babbar kotun ƙarshe wajen yanke hukunci a harkokin wasanni. Wannan na nufin cewa hukuncinta yakan kasance na ƙarshe, sai dai a wasu lokuta kaɗan idan babbar kotun ƙasar Switzerland ta soke shi saboda wasu ƙalilan daga cikin matsalolin da suka shafi tsarin shari'a.

A duk shekara ana shigar da fiye da ƙorafe-ƙorafe 900 a gaban CAS daga sama da wasanni iri 50. Waɗannan shari'o'i sun haɗa da rikice-rikice kan kwantiragin aiki da musayar 'yan wasa da amfani da abubuwan ƙara kuzari da aka haramta (doping) da cin hanci da rashawa da haƙƙin watsa shirye-shirye na talabijin da kuma, kamar a wannan shari'ar, yadda ake gudanar da gasannin.

An saurari ƙarar da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Senegal ta ɗaukaka ne a wani zaman sirri da aka yi ranar 8 ga Oktoba, inda kwamitin alƙalai uku da CAS ta zaɓa suka saurari shari'ar.

Ɗan Faransa Gerald Simon, wanda ya kafa Cibiyar Binciken Dokokin Wasanni a Jami'ar Burgundy kuma ya shafe shekara 23 yana cikin membobin CAS, ne ya jagoranci kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da farfesan dokokin ƙasa da ƙasa ɗan Italiya Luigi Fumagalli, da kuma lauya kuma farfesa a fannin shari'a a Jami'ar Zurich, Ulrich Haas, wanda ke aiki daga birnin Hamburg na Jamus.

Idan har alƙalan uku sun kasa cimma matsaya guda kan shari'ar, shugaban kwamitin, Gerald Simon, ne zai yanke hukunci na ƙarshe.

Mene ne illolin da za su iya biyo baya a nan gaba?

Duk da cewa kwamitin ɗaukaka ƙara na CAF yana da cikakken 'yanci wajen yanke hukunci, soke hukuncinsa zai zama wani babban koma baya ga martabar hukumar ƙwallon ƙafar Afirka, wadda ta sha suka sosai saboda matakin da ta ɗauka na bai wa Moroko kofin bayan an kammala gasar.

Shugaban CAF, Patrice Motsepe, ya bayyana a watan Maris cewa hukumar za ta "amince" kuma ta "girmama" duk hukuncin da CAS ta yanke. Don haka idan hukuncin ya ce Senegal ta yi nasara, hakan na iya nufin za a sake duba ko gyara wasu dokokin AFCON.

Sai dai ficewar Senegal daga fili ta riga ta haifar da sauyi a dokokin ƙwallon ƙafa.

A watan Afrilu, Hukumar Kafa Dokokin Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (IFAB) ta ce:

"Alƙali na iya bai wa kowane ɗan wasa jan kati idan ya bar filin wasa don nuna rashin amincewa da hukuncin alƙali."

Haka kuma ta ƙara da cewa: "Sabuwar dokar za ta kuma shafi duk wani jami'in ƙungiya da ya ingiza 'yan wasa su bar filin wasa. A ka'ida, ƙungiyar da ta janyo dakatar da wasa za ta rasa wasan."

Kocin Senegal, Pape Thiaw, ya rasa aikinsa bayan ficewar ƙasar daga Gasar Kofin Duniya a zagayen 'yan wasa 32 a wannan bazarar. Haka kuma Walid Regragui, wanda ya jagoranci Moroko a wasan ƙarshe na watan Janairu, an kore shi daga aikinsa a watan Maris.

Kowane hukunci aka yanke, da alama zaman ɗar-ɗar tsakanin hukumomin ƙwallon ƙafar ƙasashen biyu zai ci gaba.

Manyan jami'an Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Moroko (FMRF) sun yi fushi matuƙa da abin da suka kira halayen Senegal, suna masu cewa hotunan da aka watsa a duniya sun ɓata sunan AFCON na farko da Moroko ta shirya tun shekarar 1988. Gasar da aka kashe kuɗi masu yawa tare da ɗaukar shekaru ana shirya ta.

A gefe guda, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Senegal (FSF) da gwamnatin ƙasar sun yi zargin cewa Moroko tana da rinjaye fiye da kima a harkokin ƙwallon ƙafar Afirka.

Akwai kuma wasu abubuwan da suka ɓata wa Senegal rai. Daga ciki akwai yadda aka riƙa haska fitilun laser a idanun 'yan wasanta, da kuma yadda wasu yara masu riƙe ƙwallaye suka matsar da tawul ɗin mai tsaron raga Edouard Mendy.

Lamarin ya kai ga abin mamaki lokacin da ajiyan mai tsaron gida, Yehvann Diouf, ya yi ƙoƙarin shiga tsakani, amma masu riƙe ƙwallaye uku suka kayar da shi ƙasa.

Yayin da AFCON na gaba zai gudana a watan Yuni da Yulin shekara mai zuwa, yiwuwar sake haɗuwar manyan ƙungiyoyin biyu mafi ƙarfi a Afirka na daga cikin abubuwan da za su ja hankalin masu sha'awar ƙwallon ƙafa.

Duk da cewa abin da ya faru a wasan ƙarshe na bana ya haifar da sabuwar hamayya mai zafi tsakanin ƙasashen biyu, kusan kowa ya amince cewa irin waɗannan manyan rikice-rikice ya kamata a warware su a filin wasa, ba a cikin kotu ba.