Man United ta musanta shirin sakin Diallo, Liverpool ta matsa a kan Alonso

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta yi watsi da maganganun da ake yi cewa za ta bar dan wasanta na gaba na gefe Amad Diallo, dan Ivory Coast, mai shekara 23 ya bar kungiyar a bazaran nan. (Teamtalk)
Liverpool ta tattauna da Real Madrid a kan dan takaitaccen aikin da Xabi Alonso ya yi da kungiyar ta Sifaniya, a shirin da kungiyar ta Firimiya ke yi na duba yuwuwar bai wa tsohon dan wasan nata na tsakiya aikin kociya. (AS )
Everton na tattaunawa da John Stones a kan yuwuwar komawar dan bayan na Ingila mai shekara 31, kungiyar idan ya bar Manchester City a bazaran nan. (Football Insider)
Newcastle ta kusa rike matashin dan wasan tsakiya na Ingila Lewis Miley mai shekara 20 na tsawon lokaci inda take dab da cimma yarjejeniya da shi ta kwantiragi na tsawon shekaru. (Sun)
Yanzu dai ta tabbata cewa kungiyoyin Firimiya na - Arsenal, da Liverpool, da kuma Manchester United suna da damar samun dan bayan Italiya Andrea Cambiaso, bayan da Juventus ta ce za ta iya sakin dan wasan mai shekara 26 a bazaran na. (Teamtalk)
Har yanzu Atletico Madrid tana son sayen dan wasan tsakiya na Wolves, Joao Gomes, amma kuma ta ce ba za ta biya sama da yuro miliyan 40 ba a kan dan Brazil din mai shekara 25.(Marca)
Dan wasan tsakiya na Scotland Bailey Rice, mai shekara 19, na shirin barin Rangers a bazaran nan kuma Aston Villa na daga kungiyoyin Firmiya da suke son sayenshi. (Football Insider)
Ipswich Town na tattara sunayen masu horarwa ko da kociyanta Kieran McKenna zai samu aikin horad da wata kungiya a gasar Firmiya a bazaran nan. (Sun)











