An garzaya da Sir Alex asibiti daga Old Trafford

Asalin hoton, Getty Images
An garzaya da tsohon kocin Manchester United Sir Alex Ferguson zuwa asibiti daga filin wasa na Old Trafford bayan rashin lafiyar da ta kamashi gabanin fara wasan Premier tsakanin Man United da Liverpool a ranar Litinin.
Wasu majiyoyi sun ce mataki ne irin na rigakafi da aka ɗauka kan tsohon kocin mai shekara 84, ba wai wani yanayi ba ya shiga na gaggawa.
Ferguson wanda ya jagoranci Manchester United na tsawon shekaru 27 lokacin da ƙungiyar ta haskaka, yana yawan zuwa kallon wasan ƙungiyar ya zauna a inda aka keɓe masa.
Babu dai wani bayani kan halin da jikinsa yake tun bayan garzayawa da shi asibitin da aka yi wanda daga nan aka kwantar da shi.
Ferguson ya samu zubar jini a ƙwaƙwalwarsa a 2018, wanda hakan ya haifar masa da mummunar rashin lafiya. Ya bayyana halin da yake ciki game da rashin lafiyar tasa da sauƙin da yake samu dalla-dalla shekaru uku baya.
An ga Sir Alex a filin wasan tare da wasu baƙi a ranar Lahadin awanni gabanin fara wasan.
Dr Aseem Malhotra wani kwararran likitan zuciya ya wallafa a shafinsa na X cewa "Babbar dama a gare ni mafarkina ya zama gaske na samu dogon lokaci da Sir Alex gabanin wasan Liverpool a Old Trafford a yau."
Jami'an Manchester United na fatan kocin zai warware nan ba da jimawa ba, ya kuma koma gida.









