Mene ne zaɓen tsakiyar wa'adin mulkin Amurka, kuma me ya sa yake da muhimmanci?

.
    • Marubuci, جیمز فیتزجرالد
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Zaɓen ranar 3 ga Nuwamba, wanda zai iya yin tasiri kan ikon da ake da shi a Majalisar Dokokin Amurka da kuma makomar ci gaba da shugabancin Donald Trump, na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan siyasa da Amurka ke fuskanta.

Mene ne zaɓen tsakiyar wa'adi?

A ranar 3 ga Nuwamba, Amurkawa za su zaɓi membobin Majalisar Dokokin Amurka (Congress), wadda ta ƙunshi ɓangarori biyu: Majalisar Wakilai (House of Representatives) da kuma Majalisar Dattawa (Senate).

Ana gudanar da zaɓen majalisar dokoki duk bayan shekara biyu, kuma idan an yi wannan zaɓe a tsakiyar wa'adin shekara huɗu na shugaban ƙasa, ana kiran sa zaɓen tsakiyar wa'adi.

Ɗaya daga cikin manyan ayyukan Majalisar Dokoki shi ne tsarawa da amincewa da dokokin tarayya da ake aiwatarwa a faɗin ƙasar.

Sakamakon zaɓen tsakiyar wa'adin zai ƙayyade wace jam'iyyar siyasa ce za ta mallaki ikon Majalisar Dokoki, ko dai 'yan Republican ko kuma 'yan Democrat na adawa, da kuma irin sauƙin da shugaban ƙasa zai samu wajen aiwatar da shirye-shiryensa.

Har ila yau, sakamakon wannan zaɓe ana ɗaukarsa a matsayin ma'aunin tantance yadda jama'ar Amurka ke gamsuwa da aikin shugaban ƙasa zuwa wannan mataki na mulkinsa.

Waɗanne mutane ne ake zaɓa?

Za a zaɓi dukkan mambobi 435 na Majalisar Wakilai (House of Representatives). Mambobin wannan majalisa suna da wa'adin mulki na shekaru biyu. A mafi yawan lokuta, dokoki kan fara fitowa ne daga wannan majalisa, inda ake gabatar da su tare da yin muhawara a kansu.

A lokaci guda, za a kuma gudanar da zaɓe kan kujeru 35 daga cikin kujeru 100 na Majalisar Dattawa (Senate). Sanatoci suna da wa'adin shekaru shida. Daga cikin ayyukansu akwai amincewa ko ƙin amincewa da dokokin da suka zo musu daga Majalisar Wakilai.

A wannan rana kuma, masu kaɗa ƙuri'a a sassa da dama na Amurka za su zaɓi jami'an gwamnati na jihohinsu. Zaɓukan gwamnoni a jihohin California, Florida, Georgia da Michigan na daga cikin zaɓen da ake sa ran za a bi diddiginsu sosai.

Waɗanne ne muhimman batutuwan da ake takara a kansu?

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tattalin arzikin Amurka yana ɗaya daga cikin manyan damuwar masu kaɗa ƙuri'a da dama, musamman waɗanda ke fama da tsadar man fetur, kayan abinci, gidaje da kuma ayyukan kiwon lafiya.

Hauhawar farashin kayayyaki (inflation) har yanzu tana sama da matakin da Babban Bankin Amurka ya tsara. Wani ɓangare na wannan matsala na da alaƙa da yaƙin da Amurka da Isra'ila suka fara da Iran a watan Fabrairu.

'Yan Democrat suna cewa manufofin harajin kwastam da Donald Trump ya ɗora kan kayayyakin kasuwanci sun kuma ƙara tsadar rayuwa ga Amurkawa.

Shige da fice ma na daga cikin manyan batutuwan da ake muhawara a kansu. 'Yan Republican suna cewa Trump ya cika ɗaya daga cikin manyan alkawuran yaƙin neman zaɓensa na shekarar 2024 ta hanyar tsaurara matakan tsaron iyakoki da kuma fara wani gagarumin shiri, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce, na yaƙi da shige da ficen ba bisa ƙa'ida ba.

Haka kuma, damuwa kan basirar wucin gadi (AI) ta ƙara karfi a makonnin baya-bayan nan. Manyan 'yan siyasa daga jam'iyyun biyu sun amince cewa akwai buƙatar kafa dokoki da ƙa'idojin da za su tsara amfani da wannan fasaha. A wannan batu, suna da ra'ayi da ya sha bamban da na Trump, wanda ya yi watsi da ra'ayin samar da dokoki don takaita ci gaban fasahar.

Me sakamakon zaɓen zai iya sauyawa?

Majalisar Dokoki (Congress) tana ɗaya daga cikin rassan gwamnati uku na Amurka, tare da Fadar Shugaban Ƙasa da kuma Bangaren Shari'a. Riƙe ikon majalisar na da matuƙar muhimmanci wajen tsara da zartar da dokoki.

A halin yanzu, jam'iyyar Republican ce ke da rinjaye a duka Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa, amma rinjayen nasu ba shi da yawa.

A Majalisar Wakilai, suna da kujeru 218, wanda shi ne mafi ƙarancin adadin kujerun da ake buƙata domin mallakar rinjayen majalisar. Haka kuma, wani ɗan majalisa mai zaman kansa kan yi zaɓe tare da su a mafi yawan lokuta.

A Majalisar Dattawa kuwa, jam'iyyar Republican tana da kujeru 53.

Ikon Majalisar Dattawa zai sauya ne kawai idan 'yan Democrat sun samu aƙalla kujeru 51, domin idan kowace jam'iyya ta samu kujera 50, mataimakin shugaban ƙasa, wanda a halin yanzu ɗan Republican ne, zai kasance yana da ƙuri'ar yanke hukunci.

Idan 'yan adawa na Democrat suka sake samun rinjaye a aƙalla ɗaya daga cikin majalisun biyu, za su iya gabatar da nasu kudurorin dokoki domin a tattauna su kuma a kada ƙuri'a a kansu.

Wa ce jam'iyya ce za ta iya yin nasara?

A baya, masu kaɗa ƙuri'a kan yi abin da ake kira "hukunta jam'iyyar shugaban ƙasa", wato su kaɗa ƙuri'a a kan jam'iyyarsa maimakon su mara mata baya.

Kuri'un jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan sun nuna cewa farin jinin shugaban ƙasar ya ragu. A cewar shafin tattara bayanan ƙididdiga na Silver Bulletin, Trump ya fara wa'adinsa na biyu da goyon bayan jama'a da ya ɗan haura kashi 50 cikin 100, amma zuwa farkon watan Oktoba wannan adadi ya ragu zuwa kusan kashi 37 cikin 100. A lokaci guda kuma, kashi 61 cikin 100 na masu amsa binciken sun nuna rashin gamsuwa da yadda yake gudanar da mulki.

Sai dai ba dukkan kujerun majalisun biyu ne za a yi gasa mai zafi a kansu ba. Wasu kujerun ana kallonsu a matsayin tabbatattun kujerun jam'iyyar Republican ko Democrat.

Abokiyar hulɗar BBC a Amurka, CBS News, ta gano manyan zaɓukan kujerun Majalisar Dattawa guda 10 a jihohi kamar Iowa da New Hampshire, da kuma muhimman zaɓukan Majalisar Wakilai guda 42 a jihohi kamar Arizona da Ohio.

Zaɓen bana ya ƙara zama mai wahalar hasashe saboda takaddamar da ke tsakanin jam'iyyun biyu kan yadda ake zana iyakokin mazabun Majalisar Wakilai.

'Yan Republican sun yi ƙoƙarin tsara taswirorin zaɓe a wasu jihohi ta yadda za su fi amfanar su, yayin da 'yan Democrat ma suka ɗauki irin wannan mataki domin ƙarfafa damarsu ta lashe ƙarin kujeru.

Wane tasiri wannan zaɓe zai yi ga Trump?

Idan 'yan Democrat suka samu rinjaye a Majalisar Wakilai ko Majalisar Dattawa, zai yi wa Trump wuya ya samu amincewar Majalisar Dokoki kan dokokin da yake son aiwatarwa.

Sakamakon haka, wasu daga cikin manufofinsa na cikin gida na iya fuskantar cikas, ko da yake Trump ya samu hanyoyin amfani da ikon shugabancinsa ba tare da cikakken dogaro da jam'iyyarsa ba.

Samun iko a ɗaya daga cikin majalisun biyu zai kuma ba 'yan Democrat damar amfani da kwamitocin majalisa wajen binciken wasu sassa na shugabancin Trump.

Ana iya bincikar zarge-zargen cin hanci da rashawa, sabon babban ɗakin rawa na Fadar White House, da kuma hanyoyin aiki na Hukumar Shige da Fice da Kwastam ta Amurka (ICE).

A cikin jam'iyyar Democrat kuma, akwai tattaunawa kan yiwuwar tsige Trump (impeachment), wato gabatar da tuhume-tuhume a Majalisar Dokoki waɗanda za su iya zama tushen wani shari'ar siyasa, ba ta laifukan aikata manyan laifuka ba.

Amma idan jam'iyyar Republican ta ci gaba da riƙe ikon Majalisar Dokoki, Trump zai iya ci gaba da aiwatar da manufofinsa a sauran wa'adin mulkinsa cikin sauƙi.

Wane tasiri wannan zaɓe zai yi ga zaɓen shekarar 2028?

Sunan shugaban ƙasa ba ya cikin takardar zaɓe a zaɓen tsakiyar wa'adi, duk da cewa Trump ya bukaci 'yan Republican su kaɗa ƙuri'a kamar dai sunansa yana cikin takardar zaɓen, kuma su ɗauki ƙuri'unsu a matsayin amincewa da yadda ya gudanar da mulki zuwa wannan lokaci.

Ko mene ne sakamakon zaɓen, ana sa ran masu sharhi kan harkokin siyasa za su yi amfani da shi wajen tantance yadda masu kaɗa ƙuri'a ke kallon alkiblar da ƙasar ke bi a ƙarƙashin jagorancin Trump.

Trump ba zai iya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a karo na uku ba.

Bayan zaɓen tsakiyar wa'adi, ana sa ran hasashe da tattaunawa za su ƙaru kan wanda zai iya maye gurbinsa a matsayin ɗan takarar jam'iyyar Republican a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2028, da kuma wanda jam'iyyar Democrat za ta tsayar domin fafatawa da shi.