Su wane ne Ahlul Baiti, kuma mece ce darajarsu a Musulunci?

Hubbaren Annabi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Batun Ahlul Baiti na daga cikin abubuwan da ake samun saɓani a addinin Musulunci tsakanin mazhabobin Sunni da Shi'a.

Ahlul Baiti kalma ce ta Larabci da take nufin ''Iyalan Gida'' a ma'ana da harshe.

To amma a Musulunce tana nufin makusantan iyalan Manzon Allah, waɗanda mabiya addinin musulunci ke girmamamawa da darajawa.

Addinin Musulunci ya koyar da nuna soyayya da girmamawa ga Ahlul Baiti kamar yadda ya zo a ayoyin Al'qur'ani da hadisai da dama.

To sai dai akwai saɓani mai yawa tsakanin mazhabobin Shi'a da Sunna kan su wane ne ainihin Ahlul Baity.

Su wane ne Ahlul Baiti a mazhabin Sunna?

Dakta Abubakar Sani Birnin Kudu, babban Limaman Juma'a na masarautar Dutse a jihar jigawa, kuma Malami a Jami'ar Tarayya da ke Dutse ya ce a mazhabin sunna Alhul Bayti na nufin iyalai da dangin Annabi S.A.W waɗanda suka yi imani a cikinsu.

Ya ce a mazhabin sunna idan aka ce ahlul baity ana nufin ɓangarori guda uku, la'akari da nassosin qur'ani da hadisi

  • Bani Hashim da Bn Muɗɗalib (Masu imanin cikinsu)

Ya kafa hujja da hadisin Sahih Muslim da a ciki ya ruwaito Manzan Allah S.A.W lokacin da yake maganar zakka, inda ya ce ''zakka ba ta halasta ba ga Muhammad (S.A.W) da iyalansa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dokta Abubakar Sani Birnin Kudu ya ce Annabi ya fassara wannan hadisi a aikace lokacin da wasu sahabbai ƴan'uwansa biyu, Abdulmuɗɗalin ibn Haris ibn Rabi'a da kuma Abdullahi bn Abbas suka je wajensa domin ya ba su daga dukiyar zakka domin su yi aure.

Sai Annabi ya ce musu ai ''iyalan Muhammadu ba sa cin sadaqa'', da wannan nassi wannan suka shiga cikin ahlin Baiti, kamar yadda ya yi arin haske.

  • Matan Annabi

Dangane da nassin matan Annabi kuwa, Dokta Abubakar Sani ya ce ayar al'qur'ani ce ta 33 cikin suratul Ahzab ta sauka domin tabbatar musu da matsayin.

"Abin sani kawai, Allah yana nufin ya

tafiyarda kazanta mafi kusa gare ku,

ya ku mutanen gidan Annabi (Ahlul Baiti),

kuma ya tsarkake ku, tsarkakewa."

Malamin ya ce idan aka bi siyaƙin na tun farkon ayar da bayan duk ana magana ne a kan matan Annabi.

''Sannan idan Annabi ya zo layya yakan ce ''Ya Allah ya karɓa daga Annani da iyalan Annabi''.

Dokta Abubakar Sani ya sake kawo wani nassin lokacin da wani Khalifa mai suna Khalid ibn Sa'id ya aika wa Aisha naman sadaka, sai ta mayar ta ce iyalan Muhammadu ba sa cin sadaqa.

''La'akari da wannan matan Annabi sun shiga cikin Ahlil Baiti'', in ji malamin.

  • Ƴaƴan Annabi

Game da ƴaƴan Annabi kuwa, Dokta Birnin Kudu ya ce akwai hadisin kisa'i da Aisha ta ruwaito, in da a ciki aka ce wata rana Annabi ya kira yarsa Fatima da mijinta Aliyu bin Abi Ɗalib da ƴaƴansu Hasan da Hussaini, inda ya lulluɓe su da wani gwado, inda yake cewa ''Waɗannan su ne iyalan gidana''.

''To wannan ne wasu malamai ke ganin nassin shigar da su cikin ahlil baiti, amma hakan yana nufin su ne kaɗai cikin ahlul baiti ba'', in ji shehin malamin.

Hoton hubbaren Annabi

Asalin hoton, Getty Images

Su wane ne Ahlul baiti a wajen ƴan Shi'a?

Sheikh Bashir Lawan shugaban Sashen Da'awa da Tabliq na Mu'assar Rasulul A'azam na mazhabin Shi'a a Najeriya ya ce a Mazhabar Shi'a ba kowa ba ne cikin iyalai da dangin Annabi ke cikin matsayin Ahlin Baiti.

Ya ƙara da cewa waɗanda suke ɗauka a cikin Ahlul Baitu sun haɗa da:

  • Annabi (S.A.W)
  • Fatima Bintu Muhammad
  • Imamai 12

Imamai 12 sun haɗa da:

  • Ali bin Abi Dalib (Imam Ali)
  • Hassan bin Ali (Imam Hassan)
  • Hussaini bin Ali (Iman Hussaini)
  • Ali bin Hussaini ( Imam Sajjad)
  • Muhammad bin Ali (Imam Baqir)
  • Jafar bin Muhammad (Imam Sadiq)
  • Musa bin Ja'afar (Imam Kazim)
  • Ali bin Musa (Imam Rida)
  • Muhammad bin Ali (Imam Jawad)
  • Ali bin Muhammad (Imam Hadi)
  • Hassan bin Ali (Imam Askari)
  • Muhammad bin Hassan (Imam Mahdi)

''Waɗannan su muke ɗauka a matsayin Ahlil Baiti, a mazhabar Shi'a'', kamar yadda ya bayyana.

Sheikh Bashir ya ce Imami na 12, wato Imam Mahdi tuni aka haife shi kuma ya faku, zai kuma bayyana a ƙarshen zamani.

Ya ƙara da cewa duk wanda ba ya cikin waɗannan to ba Ahlil Baiti ba ne a mazhabin Shi'a.

''Idan ɗa ne ga Fatima, to ana ɗaukarsa a matsayin sharifi, amma ba Ahlil Baiti ba'', in ji shi.

Me ya sa Shi'a ta cire matan Annabi?

Sheikh Lawan ya ce mabiya Shi'a sun cire matan Annabi daga cikin Ahlul-Baiti ne saboda yadda suka fahimci fassarar aya ta 33 cikin Suratul Ahzab da ta yi magana a kan Ahlul baity.

"Abin sani kawai, Allah yana nufin ya

tafiyarda kazanta mafi kusa gare ku,

ya ku mutanen gidan Annabi (Ahlul Baiti),

kuma ya tsarkake ku, tsarkakewa."

Malam Lawan ya ce duk da cewa malaman musulunci sun yi ijma'i da wannan aya cewa tana magana ne a kan matan Annabi, amma kuma wasu malaman sun fayyace ma'annatar cikin littafansu.

''Misali Imam Suwiɗi cikin littafinsa na tafsiri ya kawo ruwayoyi da yawa dangane da wannan aya'', in ji malamin.

Ya ce a cikin littafin tafisirin na Imam Suwiɗi ya kawo wata ruwaya daga ɗaya daga cikin matan Annabi, Nana Ummussalama wadda ta ce bayan saukar ayar Annabi (S.A.W) ya fassarata a aikace.

''Nana Ummussalama ta ce lokacin da wannan ayar ta sauka a cikin ɗakinta, (duk da cewa ta sauka a lokuta da yawa), sai Manzon Allah ya fassarata a aikace'', kamar yadda malamin ya yi ƙarin haske.

''Daga saukar ayar sai Annabi ya ce ta kira masa ƴarsa Fatima da ƴaƴanta Hassan da Hussaini, duk sai ya lulluɓe su da wani bargo sai ya ce Allah waɗanann su ne iyalan gidan nawa, Allah ka kare su daga datti ka tsarkake su tsarkakewa da sauran addu'o'in albarka gare su''.

Sheikh Lawan ya ƙara da cewa a nan Annabi bai haɗa da Ummussalama ba, wadda take matarsa.

''Ummussalama ta ce da ta ga haka sai ta yi ƙoƙarin shiga buɗe bargon domin ta shiga, nan take sai annabi ya janye bargon daga hannunta, sai ta ce ya manzon Allah ni ba na cikin iyalan gidanka?''.

Sai annabi ya ce mata ba kya cikin wannan dai, amma kina cikin alkairi.

Kan hakan ne Sheikh Lawan ya ce da wannan suke kafa hujja wajen ware matan annabi daga kasancewa cikin Ahlul Baiti.

Masallacin Annabi

Asalin hoton, Getty Images

Shin Ahlil Baiti Ma'asumai ne?

Duka mazhabobin musulunci sun yi imani da cewa Ahlil Bayti na da matsayi da daraja mai girma a musulunci.

A mazhabin Shi'a, Sheikh Lawan ya ce ana ɗaukar Ahlil bayti a matsayin ma'asumai (waɗanda ba sa kuskure ko saɓo).

Amma mazhabin Sunna ba ta ɗaukar Ahlil Bayti a matsayin ''Ma'asumai'', kamar yadda Dokta Birnin Kudu ya yi ƙarin haske.

''A wannan al'ummar ta Manzon Allah S.A.W, babu Ma'asumi sai shi Annabi Muhammadu S.A.W, shi kaɗai ne ma'asumi'', in ji shi.

Ya ce ayar suratul Ahzab da ta ce ''an tsakake su tsarkake wa, tsarki ne na Iradar Allah, ba nassi ne kan an aiwatar da abu ba'', kamar yadda ya yi karin haske.

Mene ne bambancin Ahlil Bayti da Sharifai?

Sheikh Lawan ya ce sharifai su ne zuri'ar Ahlul Baiti, waɗanda nasabarsu ke tuƙewa zuwa ga Ahlul Baiti.

"Su ba ma ɗaukarsu a matsayin Ahlul Baiti, maimakon haka muna kiransu sharifai ko sada, su ake kira Sharu ko Sidi'', kamar yadda ya bayyana.

Shi ma Dokta Birnin Kudu ya ce Sharifai su ne duk mutanen da ke da alaƙa ta jini da nasaba zuwa ga Annabi S.A.W su ake kira Sharifai.

Ya ci gaba da cewa duk mutumin da a yanzu ya iya tabbatar da nasabarsa zuwa da Annabi S.A.W to ya zama Ahlil Baiti, kuma Sharifi.

''A yanzu Ahlil Baiti da Sharifi duk abu ɗaya ne, babu bambanci'', in ji shi.