KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 27 ga watan Yunin 2026.

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Ana fargabar gurɓacewar muhalli daga ayyukan haƙo mai a DR Congo

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Human Rights Watch ta yi gargaɗin cewa ayyukan hako mai da kamfanin Perenco ke gudanarwa a yankin Muanda da ke lardin Kongo a tsakiyar Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Kongo na iya zama barazana ga lafiyar al'umma da muhalli.

    Rahoton ya ce hayaƙin da kamfanin ke fitarwa da kuma ƙona tarkacen mai sun gurɓata ingancin iska, yayin da malalar mai daga rijiyoyi da bututun mai ta gurɓata koguna da ƙasa.

    Mazauna yankunan sun ce suna fama da matsalolin numfashi, ciwon ƙirji da tashin zuciya, kuma suna danganta waɗannan matsaloli da ayyukan kamfanin.

    Sai dai Perenco ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa binciken da aka yi na da kura-kurai.

    Kamfanin ya ce ya zuba jari wajen rage gurɓacewar muhalli da kuma tallafa wa ayyukan kiwon lafiya, tare da bayyana cewa ya dakatar da fitar da hayaƙin gas a wurare sama da 200 kuma yana aiki tare da hukumomin Kongo.

    Gwamnatin Kongo, wadda ta ba da umarnin a gudanar da binciken muhalli kan ayyukan kamfanin tun ƙarshen shekarar 2024, har yanzu ba ta fitar da sakamakon binciken ba.

    Human Rights Watch na kira ga gwamnati da ta bayyana sakamakon binciken tare da ɗaukar matakan kare lafiyar jama'a.

    Perenco, wanda shi ne kaɗai kamfanin da ke samar da mai a Kongo, na gudanar da ayyuka a kan tudu da kuma a teku a bakin gaɓar ƙasar mai tsawon kilomita 37.

  2. Najeriya ta yi martani kan kisan ɗan ƙasarta a Afrika ta Kudu

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya, ta hannun ofishin jakadancinta da ke Johannesburg, ta yi allawadai da kisan wani ɗan ƙasarta, Ibeh Chika Simon, wanda ya mutu a yayin wani samamen da 'yansandan Afirka ta Kudu suka kai a Bellville da ke Cape Town a ranar 23 ga Yuli.

    Jakadancin ya ce mutuwar tasa ta faru ne a yanayi mai cike da tambayoyi, yayin da kuma wani ɗan Najeriya, Egwabor Patrick Chuks, ya samu munanan raunuka bayan an harbe shi a wannan samame.

    A wata sanarwa, ofishin jakadancin ya ce ya yi matuƙar kaɗuwa da yadda lamarin ya faru, yana mai zargin jami’an tsaro da amfani da matakan da suka kai ga mutuwar marigayin.

    Haka kuma, ya bayyana lamarin a matsayin wani ɓangare na abin da ya kira ci gaba da kashe-kashen da ba a warware ba da kuma zargin cin zarafin baƙi a Afirka ta Kudu.

    Najeriya ta buƙaci hukumomin ƙasar su gudanar da bincike cikin gaggawa, adalci da gaskiya tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.

    A nata ɓangaren, Kwamitin Ministoci kan Harkokin Hijira na Afirka ta Kudu ya ce ana ci gaba da binciken abin da ya faru.

    Ministar Shari’a Afrika ta Kudu, Mmamoloko Kubayi, ta ce a yayin samamen ƴansandan, wasu mutane sun yi turjiya ga jami’an tsaron yayin da kuma wasu baƙi suka hana su gudanar da aikinsu.

    Ta ce za a bayyana sakamakon binciken idan an kammala shi, tare da ƙara da cewa gwamnati na damuwa da hare-haren sintiri da ake kai wa baƙi, inda aka kama mutum bakwai da ake zargi da hannu a irin waɗannan ayyuka

  3. Kare Lebanon shi ne sharaɗin farko a yarjejeniyar Iran da Amurka - Mojtaba

    ....

    Asalin hoton, Tasnim News Agency

    Kafofin yaɗa labarai na Iran sun wallafa wata wasiƙa da suka ce Mojtaba Khamenei ne ya aike ta a matsayin martani ga wasiƙar shugaban Hezbollah na Lebanon da kuma mubaya’arsa gare shi.

    A cikin wasiƙar, Mojtaba Khamenei ya yabawa Hezbollah, yana mai bayyana ƙungiyar a matsayin jagorar ƙungiyoyin jihadi masu yaƙi da Isra'ila.

    Wasiƙar ta ce Iran ta ɗauki kare Hezbollah a Lebanon a matsayin wata muhimmiyar manufa ta dabarun siyasa, bisa tsarin da Ali Khamenei ya shimfiɗa.

    Haka kuma, ta bayyana cewa kiyaye cikakken ikon ƙasar Lebanon da kuma janyewar Isra'ila gaba ɗaya daga yankunanta ba tare da wani sharadi ba su ne manyan sharuɗɗan yarjejeniyar da ake son amfani da ita wajen kawo ƙarshen yaƙin Iran da Amurka.

    Rahotanni sun ce tun bayan harin da Amurka ta kai kan gidan Ayatollah Ali Khamenei da iyalansa a ranar 29 ga Maris, ba a sake ganin Mojtaba Khamenei ko jin muryarsa ba.

  4. Amurka tana ta mana tayin zaman lafiya amma kare ƙasarmu ne muraddinmu - Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce Amurka na ci gaba da aikewa Iran tayin sasanta rikicin da ke tsakaninsu, amma abin da Tehran ta fi bai wa muhimmanci shi ne kare ikon ƙasarta, martabarta da kuma lafiyar al'ummarta.

    Baghaei ya zargi Amurka da Isra'ila da kai hare-hare kan Iran sau biyu a baya a lokutan da ake gudanar da tattaunawa, yana mai cewa hakan ya nuna cewa an ci amanar diflomasiyya sau da dama.

    Ya kuma ce Amurka ta karya yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma tsakanin ɓangarorin, yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ke zargin Iran da rashin mutunta yarjejeniyoyin da take shiga.

    Bayan kusan kwana biyu da dakatar da hare-haren ramuwar gayya tsakanin Iran da Amurka, rahotanni na nuna yiwuwar komawar ɓangarorin teburin tattaunawa domin lalubo hanyar kawo ƙarshen rikicin.

  5. Assalamu alaikum!

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ke fatan saka kasancewa da ku a wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.