Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Upamecano, Caleta-Car, Marcelo, Williams, Costa da Zidane

Babban jami'in Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya ce Liverpool da Chelsea su ne kungiyoyi biyu na gasar Firimiya da ke fafatawa da kungiyarsa a yunkurin daukar dan wasan RB Leipzig dan kasar Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 22. (Mirror)

Marseille ta ki amincewa da tayin Liverpool na euro 23m (£20m) kan dan kasar Croatia Duje Caleta-Car, mai shekara 24. (RMC Sport, via Team Talk)

Kazalika Liverpool ta gaza daukar aron dan wasan Lyon Marcelo bayan kungiyar ta hana dan wasan na Brazil, mai shekara 33, tafiya saboda raunukan da wasu 'yan wasanta suke fama da su. (Sun)

Liverpool ta yi watsi da tayin da Southampton ta yi mata a kurarren lokaci na karbar aron dan wasan Wales Neco Williams, mai shekara 19. (Sky Sports, via 90 Min)

Manchester City ba ta yi yunkurin daukar dan wasan Sifaniya Diego Costa ba duk da rade radin da ake yi cewa tsohon dan wasan Chelsea mai shekara 32 yana shirin tafiya can. (Mail)

Dole kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya yi nasara a gasar Zakarun Turai idan yana son ci gaba da zama kan mukaminsa. (AS)

Dan wasan tsakiyar Scotland Billy Gilmour, mai shekara 19, zai ci gaba da zama a tawagar Thomas Tuchel ta Chelsea a sauran lokacin da ya rage na kakar wasan bana bayan da ya burge kocin lokacin atisaye. (London Evening Standard)

Manchester United ba ta bayyana aniyar daukar dan wasan Roma dan kasar Bosnia-Herzegovina Edin Dzeko, a lokacin musayar 'yan kwallo na watan Janairu ba, duk da shawarar da kafofin watsa labaran Italiya suka ba ta. (Express)

Manchester United ta yi watsi da sha'awar da kungiyoyi irin su Southampton, Newcastle da West Ham suke nunawa ta karbar aron Brandon Williams inda take so dan wasan mai shekara 20 dan kasar Ingila ya ci gaba da murza leda a Old Trafford. (Sun)

Karfin gwiwar da Manchester City ta kara samu kan tsaron gabanta shi ya sa ta sauya ra'ayi a kan barin dan wasan Ingila Taylor Harwood-Bellis, mai shekara 19, ya tafi Blackburn a matsayin aro. (Manchester Evening News)

Manchester United da Liverpoolsuna sanya ido kan dan wasan Aston Villa mai shekara 17 Carney Chukwuemeka.(Times, via Birmingham Mail)