Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fifa Club World Cup: 'Yan wasan da za su buga wa Bayern Munich gasar
Robert Lewandowski da Manuel Neuer da kuma Thomas Müller suna daga cikin 'yan wasa 23 da Bayern Munich ta ce za su buga mata kofin Zakarun nahiyoyi FIFA Club World Cup.
A Qatar za a buga gasar da ya kamata a yi a 2020, wadda aka soke zuwa bana, sakamakon kalubalen da cutar korona da ta haddasa.
Bayern mai kofin Champions League da na Bundesliga da ta lashe a bara na fatan cin kofin zakarun nahiyoyin duniya da za a fara daga 4 zuwa 11 ga watan Fabrairu.
Idan har ta yi nasara zai zama kofi na shida da ta lashe a wata 12 - Barcelona ce ke da wannan bajintar a Turai a 2009.
Kawo yanzu Bayern Munich tana da kofin Bundesliga da na DFB Cup da na UEFA Champions League da UEFA Super Cup da kuma DFL Supercup da ta mallaka a kakar bara.
Da yake ita ce mai rike da kofin Champions League na Turai za ta fafata ne a karawar daf da karshe da duk wadda ta yi nasara tsakanin Al-Duhail ta Dubai ko kuma Al Ahly mai rike da kofin nahiyar Afirka ranar 8 ga watan Fabrairu.
Da zarar Munich ta kai karawar karshe, za ta fafata da duk wadda ta yi nasara tsakanin Palmeiras ko kuma Tigres/Ulsan Hyundai ranar 11 ga watan Fabrairu.
Wannan kofin zai zama na hudu na duniya idan Bayern ta lashe shi, bayan da ta ci Intercontinental Cup a shekarar 1976 da kuma 2001.
'Yan wasa 23 da za su buga wa Bayern Munich Fifa World Club Cup:
Masu tsaron raga: Manuel Neuer da Alexander Nubel da kuma Ron-Thorben Hoffmann.
Masu tsaron baya: Niklas Sule da Benjamin Pavard da Javi Martinez da Jerome Boateng da Bouna Sarr da Lucas Hernandez da kuma David Alaba.
Masu buga tsakiya: Joshua Kimmich da Leon Goretzka da Marc Roca da Corentin Tolisso da Kingsley Coman da kuma Jamal Musiala.
Masu cin kwallaye: Serge Gnabry da Robert Lewandowski da Leroy Sane da Douglas Costa da Eric Maxim Choupo-Moting da Alphonso Davies da kuma Thomas Muller.