Harin da Iran ta kai wa jirgin dakon kaya a Mashigar Hormuz babban kuskure ne - Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Iran da karya yarjejeniyar tsagaita wuta, bayan harin da aka kai kan wani jirgin dakon kaya a mashigar Hormuz a ranar Juma'a.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Mista Trump ya ɗora wa Iran alhakin harin, inda ya ce: "Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta harba aƙalla jirage marasa matuƙa huɗu masu kai harin kunar baƙin wake kan jiragen ruwa da ke wucewa ta mashigin Hormuz."
Ya ƙara da cewa "ɗaya daga cikin jiragen marasa matuƙi ya bugi saman wani babban jirgin dakon kaya mai tsadar gaske. Ya ce duk da harin ya taɓa jirgin, amma ya ci gaba da tafiyarsa."
Mista Trump ya kuma ce "sojojin Amurka sun harbo ƙarin wasu jirage marasa matuƙa uku."
A ƙarshen saƙonsa, shugaban na Amurkar ya ce: "Babu shakka wannan babban kuskure ne da ya karya yarjejeniyar tsagaita wutar da muka cimma."
Tun da farko hukumomi Amurka sun shaida wa kafafen yaɗa labarai cewa Iran ce ke da alhakin harin, sai dai har yanzu Tehran ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan zargin.