EU ta yi Allah-wadai da harin da Isra'ilawa suka kai wa jami’an diflomasiyyar Turai
Tarayyar Turai (EU) ta yi kakkausar suka kan harin da wasu Isra’ilawa suka kai wa jami’an diflomasiyyar Turai a Yankin Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ke mamaye da shi.
A cikin wata sanarwa, Hukumar Kula da Harkokin Wajen Tarayyar Turai ta ce: “Tarayyar Turai ta yi Allah-wadai da hare-haren baya-bayan nan da 'yan kama waje zauna suka kai a Yammacin Kogin Jordan, ciki har da hare-haren da aka kai wa jami’an diflomasiyyar Turai.”
Sanarwar ta jaddada muhimmancin hukunta masu hannu a ayyukan tashin hankali tare da dakile ci gaba da kai hare-hare da cin zarafin Falasɗinawa da kuma ‘yan jarida, musamman a lokacin girbin zaitun.
A ƙarshe, Tarayyar Turai ta yi kira ga Isra’ila da ta mutunta dokokin ƙasa da ƙasa da haƙƙin bil’adama gaba ɗaya, tare da dakatar da gina matsugunan Yahudawa a yankunan da ake takaddama a kansu.
A ranar Asabar, shaidu sun ce wasu Isra’ilawa sun kai hari kan ayarin motocin jami’an diflomasiyyar Turai a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, sannan suka kai hari kan magajin garin wani birni na Faransa wanda ke ziyarar yankin.
A gefe guda kuma, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya yi gargadin a ranar Juma’a game da yiyuwar barkewar wata babbar matsala a Yammacin Kogin Jordan bayan wani ɗan jaridar mai daukar hoto ɗan Amurka ya samu raunuka sakamakon wani hari na tashin hankali.
Lamarin ya kara nuna damuwar ƙasashen duniya kan ƙaruwar tashin hankali a Yammacin Kogin Jordan, inda hare-hare tsakanin isra’ilawa 'yan kama waje zauna da Falasɗinawa ke ci gaba da tayar da hankali a yankin.