Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gyokeres na son barin Arsenal, Liverpool na harin Nmecha
Ɗan wasan Swedin Viktor Gyokeres, na shirin barin Arsenal a watan Janairu, saboda rashin samun damar buga wasanni. (TeamTalk)
Liverpool na son ɗaukar ɗan wasan Borussia Dortmund Felix Nmecha, idan suka gaza yin nasara wajen siyen Alex Scott, daga Bournemouth. (CaughtOffside)
AC Milan na shirin miƙa tayi sabon kwantaragi ga Adrien Rabiothar zuwa 2030, bayan ƙwazon da ɗan wasan ya nuna a farkon kakar wasannin. (Corriere dello Sport - in Italian)
Kociyan Chelsea Xabi Alonso, na son siyo wasu yan wasa biyu da Bercelona Jules Kounde, da Frenkie de Jong, a watan Janairu, don ƙara ƙarfafa tsaron bayan da tsakiyar ƙungiyar. (Football365)
Chelseakuma na son ɗan wasan Borussia Dortmund Mathis Albert, wanda ya bugawa ƙungiyar wasa ɗaya kawai. (FootballTransfers)
Ɗan wasan AS Roma da Brazil Wesley, na ci gaba da jan hankulan Arsenal, da Manchester Unitedda Newcastle. (SportWitness)
Tsohon ɗan wasan bayan BrightonSolly March, na shirin komawa Charlton a matsayin ɗan wasa mai zaman kansa. Ɗan wasan dai ya kasance mai zaman kansa tun bayan da kwantaraginsa ta ƙare a Seagulls a watan Yuli. (Football Insider)
Ɗan wasan IFK Goteborg Oliver Mansson na jan hankalin ArsenaldaChelsea. (TeamTalk)
Arsenal da Manchester United sun fitar da ran ɗaukar ɗan wasan Sporting Maxi Araujo. (Sport Witness)
Chelseasun shiga mataki na gaba kan tattaunwar da suke yi na siyen ɗan wasan MoroccoGessime Yassine, da ke taka leda a Strasbourg. (Ekrem Konur)