Iran ta ƙara ƙaimi wajen yin kutse ta intanet tun bayan fara yaƙi - Isra'ila

Asalin hoton, Getty Images
Babban jami’in tsaron intanet na Isra’ila ya ce Iran ta ƙara ƙaimi wajen yin kutse ta intanet tun bayan fara yaƙi tsakanin ƙasashen biyu.
Yossi Karadi ya bayyana cewa an samu ƙaruwa a kutsen intanet daga Iran a cikin watannin baya-bayan nan.
A wata hira da ya yi da jaridar Die Welt ta Jamus, Karadi ya ce a watan Yunin 2025, lokacin da Isra’ila ke gudanar da hare-haren soji kan Iran, sun gano kusan kutse ta intanet daga Iran 1,600.
Amma a cikin makonni huɗu na baya-bayan nan na Yunin 2026, adadin ya ƙaru zuwa kusan 4,800.
Ya ƙara da cewa masu yin kusten daga Iran ƙwararru ne sosai inda ya kuma ce dole ne a ɗauki lamarin da muhimmanci.
Karadi ya kuma ce kutsen da Iran take yi ta intanet ɗin na harin muhimman cibiyoyin ƙasa, da ƙananan da matsakaitan kamfanoni kamar na lauyoyi da masu binciken kuɗi, da kuma jama’a baki ɗaya..

















