Mutanen da suka mutu a Iran da Isra'ila a tsawon yaƙin Amurka da Iran

Janaizar ɗalubai da malamansu da aka kashe a wata makarantar mata a Minab, Iran.
    • Marubuci, Christine Jeavans
    • Marubuci, Matt Murphy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Daga watan Faburairu da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da yaƙi kan Iran, alƙaluman hukumomi sun ce an kashe dubban mutane a Gabas ta Tsakiya, yayin da aka cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin.

Alƙaluman da hukumomi a Iran da Lebanon suka fitar sun ce an kashe mutane sama da 7,300 a ƙasashen biyu daga ranar 28 ga Faburairu.

Daga cikinsu harda ɗaruruwan yara da ma'aikatan kiwon lafiya da dama. Akwai kuma wasu mutanen da dama da aka kashe a sassan yankin.

Sai dai wasu masu sharhi sun ce ba a tattara alƙaluman da kyau ba, kuma ƙwararru sun shaidawa sashin binciken ƙwaƙwaf na BBC Verify cewa rufe intanet da kafofin watsa labarai da gwamnati ta yi, da kuma kasancewar ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a wasu sassan yankin sun kawo cikas ga yadda ake kai rahotannin abubuwan da ake faruwa.

Dr Iain Overton - babban darektan ƙungiyar bayar da agaji ta 'Action on Armed Violence' da ke Birtaniya ya ce faɗan da ake yi a kasashe da dama na yankin na nufin kodai ba za a iya tattara adadin waɗanda suka mutu ba, ko a samu jinkiri wajen tattara wa ko kuma a gaza tantance haƙiƙanin su.

Ya kara da cewa "za a shafe shekaru ana ci gaba da jayayya kan haƙiƙanin yawan waɗanda suka mutu a yaƙin.''

Iran

Alƙaluman da gwamnatin Iran ta fitar sun ce daga tsakiyar watan Afrilu, hare-haren Amurka da Isra'ila sun kashe ƴan Iran aƙalla 3,468 aka kashe, ciki har da mata 499.

A rahoton da ya bayar a ranar 26 ga watan Afirelu, kamfanin dillancin labarai na IRNA ya ruwaito cewa mutanen da aka kashe sun haɗa da fararen hula 1,460 da kuma sojoji 2,008.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amma kamfanin dillancin labarai na Human Rights Activists News Agency (HRANA) mai fafutukar kare hakkin dan adam (HRANA) ya ce adadin waɗanda aka kashe ya zarce haka, yana mai cewa an kashe mutane 3,636.

A cikin wani rahoto da ya fitar a ranar 18 ga Mayu, HRANA ya ce adadinsu ya haɗa da fararen hula 1,701, ciki har da ƙananan yara 307 da sojoji 1,221, da kuma wasu mutane 714 da ba a iya tantance ko su wane ne ba.

Kamfanin ya ce alƙaluman nasa ba cikakku bane saboda samun ƙididdigar waɗanda aka kashe a yankin abu ne mai wahalar gaske ta la'akari da yadda shiga yankin ke da wuya, ga kuma matakin da gwamnati ta ɗauka na katse intanet.

"Hukumomi suna ɓoye bayanai kan mutanen da aka kashe, kuma iyalan su na fuskantar matsin lamba kada su sanar da yadda aka yi ƴan uwan nasu suka mutu,'' in ji mataimakin daraktan kamfanin, Skylar Thompson,

Hukumomin Iran sun zargi Amurka da Isra'ila da kai hari kan kayayyakin more rayuwa a faɗin ƙasar.

Bincike da dama sun gano cewa wani hari da makami mai linzami da Amurka ta kai a ranar farko ta yaƙin ya afka wa wata makaranta a garin Minab, wanda jami'an Iran suka ce ya kashe mutane 168, ciki har da yara 110.

Rundunar sojin Amurka ta ce tana bincike kan harin.

Hoton wani da aka kaiwa hari a Iran.

Asalin hoton, Reuters

Kwanaki bayan nan, mahukunta a Iran sun ce an kashe mutane 20 a wani harin makami mai linzami da ya faɗa ɗakin wasannin motsa jiki, lokacin da wasu ƴanmata ke buga ƙwallon kwando a garin Lamerd.

Amurka ta musanta cewa ita ta kai harin, amma ƙwararru sun shaidawa BBC Verify cewa da aalama an yi amfani da makami mai linzami na Amurka (PrSM) wajen kai harin.

Lebanon

Rikicin Isra'ila da Hezbollah ya fara ne a ranar 2 ga watan Maris lokacin da Hezbollah ta ƙaddamar da harin ramuwar gayya a kan Isra'ila, bayan kisan jagoran addinin Iran. Isra'ila ta mayar da martani da hare-hare ta sama da kuma kutse kudancin Lebanon.

Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce tun daga lokacin mutane 3,912 aka tabbatar hare-haren Isra'ilan sun kashe, cikin su harda mata 366 da ƙananan yara 247.

Babu bayani kan ko mayaƙan Hezbollah nawa aka kashe a rikicin. BBC Verify ya tuntuɓi ma'aikatar lafiyan amma ba ta bayar da amsa ba.

Itama Hezbollah ba ta fitar da yawan mayaƙan da aka kashe mata ba, amma Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce a watan jiya sun kashe mayaƙan Hezbollaa 3,000 aka kashe tun da aka fara yaƙin.

A farkon watan Maris ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce an kashe mutane 41 a wani hari ta sama da Isra'ila ta kai a gabashin Bekaa Valley.

Haka nan kuma ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce a ranar 8 ga watan Afirelu hare-haren Isra'ila sun kashe mutane 361 a cikin minti 10. Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai harin ne kan mayaƙan Hezbollah 250.

Amma ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta musanta haka tana mai cewa duk mutanen da aka kashe fararen hula ne.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe ma'aikatan ta bakwai masu aikin tabbatar da zaman lafiya a Lebanon.

Hayaƙi na tashi bayan harin Isra'ila a birnin Beirut

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Hayaƙi na tashi bayan harin Isra'ila a birnin Beirut

Isra'ila

Hukumomin Isra'ila sun ce an kashe mutane 60 a ƙasar, mafi yawansu sakamakon hare-haren Iran da Hizbullah.

Gwamnatin Isra'ila ta shaidawa BBC cewa daga cikin su akwai fararen hula 29, sai sojoji 31.

21 daga cikinsu an kashe su a hare-haren makamai masu linzami na Iran, a cewar alkaluman gwamnati da aka bayar ga BBC. Wasu 31 kuma sojojin IDF ne suka mutu a fada.

Gwamnati ta ce mutum daya ya mutu a wani harin bam da ba a yi niyya ba.

A watan Maris, ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Human Rights Watch (HRW) ta zargi Tehran da aikata laifukan yaƙi ta hanyar kai hari kan cibiyoyin fararen hula da manyan bindigogi.

Mutuwar da aka yi a sassan Gabas ta Tsakiya

Martanin farko da Iran ta mayar kan hare-haren Amurka da Isra'ila ya faɗa ne kan ƙasashen Larabawa maƙwabtan ta, inda Amurka ke da sansanonin sojin ta.

Sojojin Iran sun harba makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa, waɗanda da yawa daga cikinsu suka kai hari kan wurare daban-daban na fararen hula, ciki har da filayen jirgin sama da cibiyoyin makamashi da tashoshin jiragen ruwa.

BBC Verify ya wallafa hare-haren baya da aka kai kan sansanonin sojoji a ƙasashe takwas da suka haɗa da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Qatar da Kuwait da Iraki da Jordan da Bahrain da kuma Oman.

Taswirar Gabas ta Tsakiya mai nuna ƙasashen Iran da Oman da Qatar da UAE da Saudiyya da Iraqi da Jordan da Israel da Kuwait da Lebanon da kuma Syria.

Samun cikakken bayani kan yawan mutanen da aka kashe da jimillar su abu ne mai wahala saboda ba dukkan ƙasashen ne suke sanar da ƙididdigar waɗanda aka kashe ba.

Sai dai sanarwar da hukumomi suka fitar da kuma rahotannin kafafen yaɗa labarai a lokuta daban-daban sun bayyana kashe-kashe da aka yi a yankin Gulf, ciki harda kisan mutane 13 a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

A Iraki, mutane sama da 100 ne suka mutu, a cewar alƙaluman da Al Jazeera da Agence France Presse suka tattara. Daga cikin waɗannan, an ruwaito cewa aƙalla mutane 80 dakarun sa kai ne na PMF.

Haka nan kuma, ma'aikatar tsaron Amurka, Pentagon ta ce an kashe dakarun Amurka 13 a sansanonin su daban-daban a Gabas ta Tsakiya, inda aka kashe bakwai a harin Iran da kuma wasu shida a harin jirgin sama.

Hukumar Kula da Jiragen Ruwa ta Duniya ta ce matuƙan jirgin ruwa 14 daga ƙasashe daban-daban sun mutu a hare-haren da aka kai kan jiragen ruwa a mashigar Hormuz da wasu wurare a Gabas ta Tsakiya.