KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 05/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 05/06/2026.

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Mohammed, Usman Minjibir

  1. 'Iran ta yi harbin gargaɗi kan jiragen Amurka'

    Mojtaba

    Asalin hoton, ISNA

    Iran ta ce ta harba makamai masu linzami domin yin gargaɗi ga jiragen yaƙin ruwa na Amurka a gaɓar ruwan Oman, inda ta ce jiragen na Amurka na hantarar tankokin mai da ke ratsawa da kuma jiragen ƴan kasuwa.

    Sai dai Amurka ta musanta hakan, wadda tun farko ta ce ta tare wani jirgin ruwa da aka ƙaƙaba wa takunkumi, da kuma wani jirgin wanda bai ɗauke da tutar kowace ƙasa a tekun Indiya.

    Wani saƙo da aka wallafa ya ce Amurka za ta ci gaba da tare duk wani jirgin ruwa da ke taimaka wa Iran.

    A ranar Alhamis, masu lura da sufurin jiragen ruwa sun ce sun lura da cewa jiragen ruwa mallakin Iran da dama sun ratsa ta Mashigar Hormuz dun da iƙirarin toshe tashoshin ruwan Iran da Amurka ta ce tana yi.

  2. Matatar Dangote ta ƙara yawan man fetur da take tacewa a rana

    Dangote

    Asalin hoton, X/Dangote Refinery

    Matatar man fetur ta Dangote ta ƙara yawan man fetur da take tacewa zuwa ganga 700,000 a rana, a wani tacewa ta gwaji da hukumomi suka yi, wanda hakan wani muhimmin mataki ne ga ayyukan matatar wadda ke ƙoƙarin tabbatar da kanta a matsayin mafi girma a duniya.

    Wannan na nufin matatar ta ƙara man da take tacewa daga ganga 650,000 a rana.

    Mataimakin shugaban sashen man fetur da gas na kamfanin Dangote, Devakumar Edwin ya bayyana cewa ƙara yawan man da matatar ke tacewa na daga cikin shirin matatar na nunka yawan ɗanyen man da take tacewa zuwa ganga miliyan 1.4 a rana cikin shekara biyu da rabi.

    Matatar Dangote ta samu karɓuwa tun bayan fara aikinta, inda a yanzu take taka rawa wajen samar da man jiragen sama a ƙasashe da dama.

    Sai dai matatar na ci gaba da fuskantar ƙalubale a cikin gida, inda take kokawa kan wasu matakan hukumomin Najeriya, musamman game da bai wa wasu kamfanonin damar shigar da tataccen man fetur daga waje.

  3. Wani samfurin AI ya fara fanɗare wa ɗan'adam

    AI

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin Anthropic, daya daga cikin manyan kamfanonin da ke samar da fasahohin ƙirƙirarriyar basira (AI), ya yi gargadin cewa wasu daga cikin fasahohin da ya samar sun nuna alamun cewa za su iya fanɗare wa umarnin ɗan'adam da kuma ikon lura da su, lamarin da ya sa ya ba da umarnin gaggauta dakatar da samar da su a fadin duniya baki daya.

    Kamfanin na Amurka, ya ce bayanan da ya tattara sun nuna cewa AI na ƙara saurin inganta kansa cikin sauri, yayin da rawar da ɗan'adam ke iya takawa kansa a kowane mataki ke ci gaba da raguwa.

    Anthropic ya ce mafita ɗaya ita ce kamfanonin AI a ƙasashe daban-daban su rage saurin ci gaban wannan fasaha a lokaci guda, karkashin dokoki da kowa zai iya tabbatar da ana bin su.

    Kamfanin ya kara da cewa hakan zai ba jama'a da hukumomi damar daidaita tsarin zamantakewa da tattalin arziki da sauye-sauyen da fasahar ke haifarwa.

  4. Zelensky na son ganawa da Putin don kawo ƙarshen yaƙi

    Shugaban Rasha Volodymir Zelensky

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensk, ya wallafa wata buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga takwara aikinsa na Rasha, Vladimir Putin, inda ya gayyace shi zuwa ganawar ido-da-ido domin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi.

    Wasiƙar, wadda aka wallafa a shafin intanet na shugaban Ukraine, ta ce a daidai lokacin da hankalin Amurka ya karkata gaba ɗaya kan rikicin Iran, ba zai dace a ci gaba da jiran lokacin da yaƙin Turai zai sake zama babban abin da Amurka za ta mayar da hankali a kai ba.

    Zelensky ya kuma ce ƴan Rasha sun fara gajiya da hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da Ukraine ke kaiwa, da kuma matsalar hauhawar farashin kaya da ƙarancin man fetur, don haka a shirye suke su ga an samar da zaman lafiya.

    Sa'o'i kaɗan bayan fitar da wasikar, fadar mulkin Kremlin ta Rasha, ta yi martani da cewa ana maraba da Mista Zelensky a birnin Moscow, idan har da gaske yana son ganawa ne da shugaba Putin.

  5. Barka da warhaka!

    Babban masallacin Abuja

    Asalin hoton, Getty Images

    Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye wanda ke kawo muku labaran duk abubuwan da ke faruwa game da yaƙin Iran da kuma muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da saurarn sassan duniya a wannan rana ta Juma'a - ta-bawa, ranar samu.

    Za ku iya yin tsokaci a shafukanmun na sada zumunta: facebook, X, instagram, YouTube sai kuma zaurenmu na WhatssApp.