Yaushe za a yi jana'izar Ayatollah Khamenei?

Khamenei

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Sayyed Ali Khamenei jagoran addinin Musulunci na ƙasar Iran ya rasu a ofishinsa a ranar 28 ga Fabareru, a harin farko da Isra'ila da Amurka suka kai kan Iran.

Baya ga kisan jagoran, akwai wasu iyalansa da dama da aka kashe a harin da suka haɗa da surukarsa, Zahra Haddad Adel, wadda ita ce matar Mojtaba Khamenei, sabon Jagoran addinin na yanzu, da surukinsa Misbah-ul-Hada Bagheri Kani, mijin ƴarsa Hoda Khamenei da jikarsa mai wata 14, Zahra Mohammadi Golpayegani, ƴa ga ɗansa Bashar Khamenei.

Ita ma mai ɗakin Khamenei Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh, wadda ta rasu kwana uku bayan harin,ta ji mummunan rauni a harin wanda ya jefa ta cikin mayuwacin hali.

Hare-haren na Amurka da Isra'ila sun janyo mutuwar manyan jagororin ƙasar, to amma tuni aka yi jana'izar da dama daga cikinsu.

Khamenei

Asalin hoton, Getty Images

Tambayar da jama'a ke yawan yi shi ne yaushe ne za a yi jana'izar Sayyed Ali Khamenei fiye da watanni biyu da kisan nasa?

Sai dai kuma a makon da ya gabata ne aka gudanar da tarukan tunawa da jagoran addinin a birnin Tehran

A lokacin yaƙin, an dage jana'izar zuwa lokacin da ya dace, amma ba a bayyana wata rana ba duk da cewa bayan tsagaita wuta an fara maganar shirye-shiryen jana'izar.

A baya, Mohsen Mahmoudi, shugaban kwamitin da ke yaɗa addinin Musulunci na lardin Tehran, ya ce jana'izar Khamenei za ta zama ta musamman.

"Za ta zama wani babban taro na duniya da za a rubuta a tarihin duniyar Musulunci da Iran. A halin yanzu muna karɓar rajista da sanarwar shirin halarta daga ƙasashe daban-daban, kamar Iraki."

'Za a binne Khamenei a Mashhad a Muharram'

Khamenei

Asalin hoton, Getty Images

A cewar mataimakin shugaban harkokin al'adu da zamantakewa na Hukumar Birnin Tehran, jana'izar Ali Khamenei, tsohon shugaban Jamhuriyar Musulunci, za a "iya yi a ƙarshen watan Dhul-Hijja da farkon watan Muharram," wato kusan cikin makonni biyu da ke tafe.

Mohammad Amin Tavakolizadeh ya bayyana haka a taron kwamiti na 52 na harkokin zamantakewa da al'adu na manyan biranen Iran cewa rundunar juyin juya hali ita ce ke kula da shirya wannan taron jana'iza, kuma an tsara jama'a za su gudanar da faretin bangirma na tsawon kwanaki uku domin wannan lamari.

Malam Tavakolizadeh ya ce bayan taron bankwana, za a gudanar da sallar jana'iza da sauran al'adun jana'iza, wanda zai ɗauki aƙalla sa'o'i 24 a Tehran.

"Muna shirin karɓar mutane sama da miliyan 15 zuwa 20 a babban birnin ƙasar."

Jana'iza a Tehran, Qom da Mashhad

Khamenei

Asalin hoton, Getty Images

A cewarsa, bayan Tehran, an tabbatar da cewa za a gudanar da jana'izar a biranen Qom da Mashhad, kuma larduna daban-daban sun nemi su karɓi jana'izar.

Ya kuma ce za a binne Ayatollah Ali Khamenei a harabar hubbaren Imam Reza da ke Mashhad, "bisa wasiyya da shawarwarin iyalansa."

Mataimakin magajin garin Tehran ya ce ana sa ran jami'ai da "masu zaman makoki" daga Pakistan, Afghanistan, India, Bangladesh, Kashmir, da sauran yankunan duniyar Musulmi ta gabas za su je Mashhad.

Har ila yau, ya ce biranen da ke kan hanyar da za a bi a lokacin jana'izar za su tarbi gawar tare da gudanar da tarukan girmamawa na aƙalla kwana ɗaya, ciki har da Qom, Karaj, Saveh, Garmsar, da Semnan.

A cewarsa, an gabatar da buƙata ga ƙabilu, al'umma da kuma majalisar dokokin ƙasar Iraki domin a gudanar da jana'izar a can ma, amma jami'an gwamnatin ƙasar na nazarin batun.

Wane ne Ayatollah Khamenei?

Khamenei

Asalin hoton, Getty Images

Ayatollah Ali Khamenei shi ne jagoran addini na Iran na biyu bayan juyin-juya halin ƙasar da aka yi a shekarar 1979, kuma tun a shekarar 1989 yake riƙe da muƙamin.

Matasan ƙasar yawanci sun taso ne suna ganin sa a matsayin jagoran addininsu.

Yana riƙe ne da madafun iko mai ƙarfin gaske - yana da ikon hawa kujerar na-ƙi a kan duk wani matakin ƙasar, sannan yana da ikon zaɓa ko naɗa wanda yake so a wata kujerar mulkin ƙasar.

Shi ne jagoran askarawan ƙasar, ciki har da dakarun juyin juya-halin ƙasar wato Iranian Revolutionary Guard Corps (IRGC).

Tarihin Khamenei

Khamenei

Asalin hoton, Getty Images

An haife shi ne a garin Mashhad, birni na biyu mafi girma a Iran a shekarar 1939.

Shi ne na biyu a wurin mahaifansa masu ƴaƴa takwas, kuma mahaifinsa ya kasance malamin Shi'a.

Ya fara karatu ne da koyon karatun Ƙur'ani tun yana ƙarami, inda ya zama malami yana da shekara 11.

Duk da cewa yana daga cikin masu bayar da fatawa kan al'amura, a yanzu haka za a iya cewa aikinsa ya fi tasiri a siyasance.

Khamenei mutum ne da Allah ya yi wa baiwar iya tsara magana sosai, kuma ya kasance kan gaba wajen sukar gwamnatin Shah ta Iran, sarkin da aka hamɓarar a juyin juya-halin ƙasar.

Yawancin rayuwar Khamenei ta kasance a ƙarƙashin ƙasa ne ko a gidan yari. Sau shida ana kama shi a zamanin mulkin Shah, inda ya fuskanci uƙuba.

An ce yana son rubutacciyar waƙa da lambu. Khamenei ya samu matsala a hannunsa na dama a wani yunƙurin kashe shi da ya tsallake a shekarun 1980s.

Khamenei a matsayin jagora

Khamenei

Asalin hoton, Getty Images

Shekara ɗaya bayan juyin juya-hali a 1979, sai Ayatollah Ruhollah Khomeini ya naɗa shi babban limamin Juma'a na birnin Tehran.

Daga baya sai aka zaɓe shi a matayin shugaban ƙasa a 1981, kafin shugabannin addinin ƙasar suka zaɓe shi a shekarar 1989 domin ya maye gurbin Ayatollah Khomeini, wanda ya rasu yana da shekara 86.

Iyalan Khamenei

Khamenei

Asalin hoton, Getty Images

Shi da maiɗakinsa, Mansoureh Khojasteh Baqerzadeh suna da yara shida - maza huɗu da mata biyu, ciki har Mojtaba Khamenei wanda ya gaji mahaifinsa.

Ba kasafai ake ganin iyalan Khamenei ba, kuma babu takamaimen bayani game da rayuwarsu.

Babu bayanai sosai game da ƴaƴansa mata biyu.

Bushra da Hoda ne ƙanana a cikin yaran, kuma duk an haife su ne bayan juyin juya-hali na 1979.