An kama surukar da ake zargi da taimakawa wajen kashe matar ɗanta

Asalin hoton, Courtesy Twisha's family
- Marubuci, Cherylann Mollan
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 2
Babbar hukumar binciken laifuka ta kasar Indiya ta kama wata suruka, wadda ake zargi da hannu a kisan matar ɗanta, lamarin da ya haifar da muhawarori kan zargin kisan kai.
Iyayen matar da aka kashe, Twisha Sharma da ƴan'uwanta sun yi zargin cewa mijinta, Samarth Singh, wanda lauya, tare da mahaifiyarsa Giribala Singh - wadda alƙaliya ce da ta yi ritaya, su ne suka azabtar da ita a kan kudin sadaki, kuma har suka kashe ta, sai dai sun musanta zargin.
Matar wadda ƴar fim ce kuma mai tallar kayan ƙawa ƴar shekara 33 sun yi auren ne na tsawon wata biyar kacal, kafin aka ga gawarta a cikin gidan nata da ke birnin Bhopal na jihar Madhya Pradesh a ranar 12 ga watan Mayu.
A ranar Alhamis, Cibiyar Binciken Manyan Laifuka ta Indiya ta kama surukar, Giribala Singh bayan ta yi mata tambayoyi na tsawon sa'o'i.
Tun farko babbar kotun Madhya Pradesh ta soke yunƙurin neman belin surukar, bayan gano cewa kotun da ke sauraron shari'ar ta yi watsi da wasu shaidu da bayanan wadanda suka shaida abin da ya faru.
Bayan mutuwar Twisha, ƴansanda sun shigar da ƙorafi na kisa kan batun sadakin aure a kan iyalan Singh.
A farkon wannan mako ne Cibiyar Binciken Manyan laifuka ta Indiya ta karɓe batun binciken.
Kisan Twisha ya ja hankalin al'umma sosai, inda jaridu da gidajen yaɗa labarai suka dauki rahoton.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wannan batu ya sake dawo da muhawarar da ake yi kan kisan mata sanadiyyar kudin sadaki.
Dubban mata ne ake kashewa a kowace shekara saboda sun kasa biyan kudin sadaki da yawa, duk da cewa an haramta wannan al'ada a shekarar 1961.
Haka nan lamarin ya ƙara janyo hankalin al'umma ne saboda iyalan sanannu ne.
Twisha ta kasance tsohuwar sarauniyar kyau kuma ƴar fim ce, yayin da mijinta da surukarta dukkansu lauyoyi ne.
Iyayen marigayiyar sun ce an fara hantarar ƴar tasu kan batun sadaki ne jim kaɗan bayan yin auren.
Sun kuma ce a lokacin da matar ta samu juna-biyu sai mijin nata da surukar suka zarge ta da cin amanar aure, har ma suka buƙace ta ta zubar da cikin.
Iyalan mijin sun musanta waɗannan zarge-zarge, inda suka ce marigayiyar tana fama da matsalar taɓin hankali ne kuma ita ce ta kashe kanta, kuma sun ce ita ce da kanta ta riƙa tunanin zubar da cikin.
Yanzu haka mijin marigayiyar, wato Singh na hannun ƴansanda. Tun farko ya tsere bayan mutuwar tata, amma ƴansanda suka samu nasarar kama shi ranar 22 ga watan Mayu a birnin Jabalpur.
A ranar Lahadin da ta gabata ne aka ƙona gawar Twisha bayan an yi gwaje-gwaje. Iyalanta sun yi ƙorafin cewa gwajin farko da aka yi bai yi ba sannan suka zargi ƴansanda da neman yin rufa-rufa, ƴansanda sun musanta hakan.











