An kuɓutar ƴar Faranasa da mijinta ya tsareta na tsawon shekara 12
Ƴan sanda a Pakistan sun kama wani mutum da ake zargin ya tsare matarsa da ƴaƴansa a gida tare da cin zarafinsu fiye da shekaru goma.
Matarsa, ƴar asalin ƙasar Faransa mai suna Sylvie Yasmina, ta yi iƙirarin cewa mutumin yana cin zarafin iyalinsa ta hanyoyi daban-daban “a kowace rana” tare da bayyana shi a matsayin “mai mugun hali” kamar yadda ƴan sandan yankin suka shaida wa BBC Urdu.
Ɗaya daga cikin ƴaƴansu ya yi nasarar lallabawa ya kai rahoto ga ƴan sanda, lamarin da ya haifar da farmaki kan gidansu da ke Bara, wani gari mai nisa a lardin Khyber Pakhtunkhwa mai cike da tsaunuka.
‘Yan sanda sun gano Yasmina da ƴaƴanta guda biyar a cikin wani ɗan ƙaƙanin ɗaki da ya dagargaje da raunuka a jikinsu.
An kai Yasmina da ƴaƴanta zuwa gidan kula da mata da ke Peshawar. Suna shirin komawa Faransa, in ji ƴan sanda.