KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 24 ga watan Yunin 2026.

Skip Bidiyo and continue reading
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Kutama
  • xxx
  • Sadis Buba

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Cutar Ebola ta ɓulla a Faransa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Faransa ta sanar cewa ta tabbatar da ɓullar cutar Ebola a ƙasar, bayan wani likita da ya dawo daga aikin jin ƙai a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DRC) ya kamu da cutar.

    Ma’aikatar lafiyar ƙasar ta ce an garzaya da shi asibiti na musamman cikin gaggawa, kuma yana cikin yanayi mai kyau.

    Wannan shi ne karo na farko da aka tabbatar da cutar Ebola a Turai.

    Duk da haka, wani likitan Amurka da ya kamu da cutar a DRC ya taba samun magani a Jamus.

    Haka kuma, Uganda ta tabbatar da ɓullar cutar, inda aka samu mutane 20 da suka kamu, ciki har da mutum biyu da suka mutu.

    An kuma ce cutar ta sake ɓulla a DR Congo a watan da ya gabata, sai dai masana sun yi hasashen cewa ta fara yaɗuwa tun kafin a sanar da ɓarkewar.

    Sama da mutane 260 ne suka mutu sakamakon cutar a DR Congo yayin da fiye da 1,000 suka kamu da da ita a ƙasar.

    Hukumomin Faransa sun jaddada cewa babu wani haɗarin yaduwar cutar sosai ga jama’a.

    Sun kuma ce suna ci gaba da bin diddigin duk wanda ya yi hulɗa da likitan domin hana yaɗuwar cutar, wadda ke yaɗuwa ta hanyar gumi musamman tsakanin ma’aikatan lafiya.

  2. Oman ta ƙiƙiri hanyar wucewar jiragen ruwa na wucin gadi a mashigar Hormuz

    .....

    Asalin hoton, Reuters

    Oman ta sanar a ranar Talata cewa ta ƙirƙiri wata hanya na wucin gadi a teku domin sauƙaƙa zirga‑zirgar jiragen ruwa da ke wucewa ta mashigar Hormuz.

    Hakan ya biyo bayan haɗin gwiwa da Hukumar Kula da Jiragen Ruwa ta Duniya (IMO) domin tabbatar da tsaro a wannan muhimmiyar hanya ta ruwa.

    Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Oman ya bayyana cewa duk jiragen da ke son wucewa ta mashigar dole ne su bi ƙa’idojin da aka gindaya, tare da yin hulɗa kai tsaye da hukumomin Oman da kuma IMO kafin su shiga sabuwar hanyar da aka ƙirƙiro.

    Sanarwar ta zo ne bayan ziyarar da shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya kai Oman tare da tawaga ta diflomasiyya.

    Hakan kuma ya biyo bayan wata sanarwa ta haɗin gwiwa da Iran da Oman suka fitar, inda suka jaddada ƙudurinsu na tabbatar da cewa mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a buɗe kuma mai aminci ga zirga‑zirgar kasuwanci ta duniya.

    Kasashen biyu sun kuma bayyana cewa za su kafa kwamitin haɗin gwiwa domin duba yadda za a tafiyar da mashigar a nan gaba, da kuma tantance kuɗin ayyukan da ake bayarwa ga jiragen ruwa da suke bi ta mashigar.

  3. Yadda Majalisar Najeriya za ta fara muhawara kan samar da 'yansandan jihohi

    ....

    A ranar Larabar nan ne ake sa ran Majalisar Dattawan Najeriya za ta fara muhawara kan wani gagarumin ƙudirin doka da ke neman samar da rundunonin 'yansandan jihohi, matakin da zai iya haifar da ɗaya daga cikin manyan sauye-sauye a tsarin tsaron ƙasar tun bayan komawarta mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.

    Ƙudirin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar a ranar Talata, zai bai wa jihohin Najeriya 36 damar kafa tare da tafiyar da rundunonin 'yansandansu, baya ga rundunar 'yan sandan tarayya ta Najeriya.

    Tsawon shekaru da dama, gwamnatin tarayya ce kaɗai ke da ikon kula da harkokin 'yan sanda a Najeriya, inda ake tura jami'ai zuwa sassan ƙasar ƙarƙashin tsari guda da ake gudanarwa daga tarayya.

    Ƙudirin ya sake tayar da muhawarar da aka daɗe ana yi a Najeriya kan ko ya kamata a raba ikon gudanar da harkokin 'yan sanda a ƙasar da ke da sama da mutum miliyan 220, masu bambancin ƙabila, addini da kuma yankuna.

  4. Meyasa Iran ta dage kan haɗa Hezbollah a yarjejeniya da Amurka?

    Masana na ganin cewa dalilin da ya sa Iran ke dagewa wajen haɗa batun Lebanon da kungiyar Hezbollah cikin yarjejeniyarta da Amurka yana da alaƙa da yadda take kallon tsaron yanki da kuma tasirinta a Gabas ta Tsakiya.

    Duk da cewa an mayar da hankali kan dakatar da rikici tsakanin Iran da Amurka, Tehran na ganin ba za a iya ware Lebanon daga wannan tattaunawa ba.

    A ra’ayinta, Hezbollah wata muhimmiyar kafa ce ta tsaro da kuma tasiri, musamman wajen tinkarar Isra’ila. Saboda haka, Iran na kallon ƙungiyar a matsayin muhimmin abokin kawance wanda ke taka rawa wajen kare muradunta da kuma ƙarfafa matsayinta a yankin.

    Haka kuma Iran na ɗaukar cewa rikice-rikice a yankin na da alaƙa da juna.

    A fahimtarta, ci gaba da yaƙi a Lebanon zai iya yin tasiri kai tsaye kan zaman lafiyarta, don haka tana ganin dole ne a samu warware matsalar a dukkan ɓangarori kafin a kai ga cikakkiyar yarjejeniya.

    Bugu da kari, batun Lebanon ya zama wata dabara ta siyasa a tattaunawa.

    Tehran na amfani da shi a matsayin hanyar matsin lamba domin samun sassauci daga ɓangarorin da take tattaunawa da su, musamman dangane da hare-haren Isra’ila.

    Sai dai wannan tsari na ɗauke da hadari, domin yana iya kawo tsaiko ko ma karya yarjejeniyar gaba daya idan wasu ɓangarori suka ƙi yarda.

    Duk da haka, Iran na ganin cewa kare Hezbollah da tabbatar da zaman lafiya a Lebanon wani bangare ne mai muhimmanci na manufofinta da tsaron yankin.?

  5. Gwamnatin Oyo ta saka dokar hana fita a ƙananan hukumomi 10

    ....

    Asalin hoton, Seyi Makinde/X

    Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince da sanya dokar hana fita na sa'o'i 16 a wasu ƙananan hukumomi 10 kan matsalar tsaro a jihar.

    Sanarwar da sakataren gwamnatin Jihar, Farfesa Musibau Babatunde ya fitar ta ce dokar za ta fara aiki daga yau, ranar Laraba, 24 ga watan Yuni, 2026, kuma za ta kasance tsakanin karfe 4 na yamma zuwa karfe 8 na safe na tsawon sa’o’i 16 a matakin farko.

    Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Oriire da Orelope da Irepo da Saki West da Saki East da Atisbo da Itesiwaju da Iseyin da Olorunsogo da kuma Atiba, musamman waɗanda ke kusa da gandun dajin Old Oyo National Park.

    Wannan mataki ya biyo bayan zanga-zangar da ta ɓarke a jihar sakamakon sace yara da malamai a yankin Oriire a watan Mayu, inda masu zanga-zangar suka buƙaci gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa domin ceto waɗanda aka sace tare da kawo karshen matsalar tsaro a faɗin kasar.

  6. 'Amurka da Isra’ila na shirin bai wa sojojin Lebanon iko a kudancin ƙasar'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni sun ce Amurka da Isra’ila na nazarin wani shiri da zai bai wa sojojin Lebanon iko da wasu yankunan kudancin ƙasar, wanda a halin yanzu sojojin Isra’ila ke riƙe da su.

    Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewa, bisa wannan tsari, sojojin Lebanon za su karɓi iko da yankunan ne bayan sun samu horo da kuma binciken tsaro daga Amurka domin tabbatar da cewa ba su da alaka da kungiyar Hezbollah.

    Majiyoyi sun kuma bayyana cewa Isra’ila za ta ci gaba da zama a yankunan har sai an tabbatar da cikakken tsaro kafin a miƙa su ga sojojin Lebanon.

    Sai dai kawo yanzu Amurka da Isra’ila ba su fito fili sun tabbatar da wannan shiri ba.

    A halin da ake ciki, tattaunawa tsakanin Isra’ila da Lebanon na ci gaba a birnin Washington.

    Batun janyewar sojoji da kuma dakatar da rikici a dukkan ɓangarori, ciki har da Lebanon, na daga cikin muhimman batutuwan da ke cikin yarjejeniyar fahimta tsakanin Amurka da Iran.

  7. Daina yaƙi a Lebanon ginshiƙi ne wajen kawo ƙarshen yaƙi a ƙasarmu - Iran

    ....

    Asalin hoton, IRNA

    Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya ce kawo ƙarshen yaƙi a Lebanon abu ne mai muhimmanci ga gwamnatin Tehran saboda ginshiƙi ne na kawo ƙarshen yaƙi a Iran ne.

    Ya bayyana wannan matsayi ne yayin wani jawabi a taron ƙungiyar majalisun dokoki na ƙasashen Kungiyar Hadin Kan Musulunci (OIC) da aka gudanar a birnin Baku.

    A cewarsa, Iran a shirye take ta inganta hulɗa da sauran ƙasashen Musulmi bisa ginshiƙin girmama juna da kauce wa tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kowace ƙasa.

    Haka kuma Qalibaf ya jaddada cewa tsaron yankin ya kamata ya fito daga cikin ƙasashen yankin kansu, ba tare da dogaro da karfin waje ba, yana mai nuni da cewa su ne suka fi dacewa wajen samar da tabbataccen tsaro.

  8. Trump ya soki matakin majalisar dattawan Amurka kan hana yaƙi da Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kakkausar suka kan matakin da Majalisar Dattawan Amurka ta ɗauka na zartar da ƙudirin dakatar da matakin soja kan Iran.

    Trump ya bayyana cewa sanatoci sun aika saƙo ga Iran cewa ba su gamsu da matakan da ya ɗauka kansu ba, yana mai cewa hakan ya “tallafa tare da karfafa gwiwar abokan gaba.”

    Majalisar Dattawan Amurka ta amince da ƙudirin da ke buƙatar Trump ya dakatar da duk wani yaƙi da Iran ko kuma ya nemi izinin Majalisar Dokoki kafin ya ci gaba da ɗaukar irin wannan mataki.

    Tun da farko ma, Majalisar Wakilai ta Amurka ta amince da irin wannan kudiri.

    Sai dai ƙudirin ba ya da cikakken karfin doka, domin ana kallonsa a matsayin na alama ne kawai.

  9. Assalamu alaikum!

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da Safiya

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.