Hanyoyi biyar da maza za su iya bi don tazarar haihuwa

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Aisha Babangida
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
A lokuta da dama idan aka ambaci batun tazarar haihuwa, hankali kan karkata ne kawai ga mata.
Sau da yawa su ake ganin ke da alhakin amfani da hanyoyin da za su taimaka wajen yin tazarar haihuwa ko rage yawan haihuwa cikin ƙanƙanin lokaci.
Amma masana harkokin lafiya sun bayyana cewa maza ma suna da rawar da za su taka wajen tsara iyali da kuma tabbatar da samun tazara tsakanin haihuwa.
Tazarar haihuwa na taimakawa wajen kare lafiyar uwa da jariri, tare da ba iyali damar kula da 'ya'yansu yadda ya kamata in ji Farida Abdullahi, wata ma'aikaciyar jinya a wani asibitin kuɗi a Abuja.
Farida ta ce duk da cewa akwai hanyoyi da dama da mata ke amfani da su, akwai kuma wasu hanyoyi da maza za su iya amfani da su ko kuma su taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da su.
Ma'aikaciyar jinyar ta yi bayani kan wasu hanyoyi guda 5 da maza za su iya amfani da su wajen yin tazarar haihuwa kamar haka.
Fitar da azzakari kafin fitar maniyyi

Farida Abdullahi ta ce wata hanya da maza za su iya amfani da ita domin yin tazarar haihuwa ita ce fitar da azzakari daga gaban mace kafin maniyyi ya fita.
Ta ce wannan hanya na buƙatar kulawa sosai da kuma iya sarrafa kai daga ɓangaren namiji.
Sai dai ta yi gargaɗin cewa wannan hanya ba ta da tabbaci sosai idan aka kwatanta da wasu hanyoyin tazarar haihuwa, domin wani lokacin wasu sinadarai masu ɗauke da ƙwayoyin halitta na iya fita kafin cikakken maniyyi, amma kuma yana aiki sosai wajen tazarar haihuwa a lokaci guda.
"Idan namiji bai iya sarrafa lokacin fitar maniyyi ba, akwai yiwuwar mace ta ɗauki ciki," in ji ta.
Amfani da kwaroron roba

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikaciyar jinyar ta ce amfani da kwaroron roba na daga cikin hanyoyin da suka fi sauƙi kuma suka fi shahara da maza za su iya amfani da su.
Ta bayyana cewa idan aka yi amfani da shi yadda ya kamata, yana taimakawa wajen hana maniyyi shiga mahaifa, wanda hakan ke rage yiwuwar samun ciki.
Baya ga hana ɗaukar ciki, ta ce kwaroron roba na kuma taimakawa wajen kare ma'aurata daga wasu cututtukan da ake ɗauka ta hanyar saduwa.
Hanyar amfani da kwanan wata

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewar Farida Abdullahi, hanyar amfani da kwanan wata da ake kira da "calender method" na ɗaya daga cikin hanyoyin da ke tasiri idan aka yi amfani da shi domin yin tazarar haihuwa amma kuma yana buƙatar haɗin kai tsakanin miji da matarsa.
Ta ce ana bibiyar kwanakin al'adar mace domin tantance kwanakin da take cikin lokacin haihuwa da kuma kwanakin da yiwuwar ɗaukar ciki ke da yawa.
A irin waɗannan kwanaki ne ma'aurata kan kauce wa saduwa ko kuma su yi amfani da wata hanyar kariya kamar na ɗaya da na biyu na da lissafo.
Farida ta ce "wannan hanya na bukatar mace ta san tsarin al'adarta sosai, kuma tana aiki ne mafi kyau ga matan da al'adarsu ke zuwa a kan lokaci."
Ma'aikaciyar jinyar ta ƙara da cewa idan ma'aurata suka san kwanakin da mace ke cikin lokacin haihuwarta, za su iya dakatar da saduwa na wasu kwanaki domin kauce wa samun ciki.
Sai dai ta ce wannan hanya na bukatar fahimta da hakuri daga bangarorin biyu domin samun nasara.
Daure bakin kwaroron maniyyi

Asalin hoton, Getty Images
Farida Abdullahi ta ce akwai wata hanya da ake ɗaure bakin kwaroron da maniyyi ke fita wanda ake kira da "vasectomy", da ake yi wa namiji ta hanyar ƙaramar tiyata.
Ta bayyana cewa bayan an yi wannan hanya, namiji na ci gaba da fitar da maniyyi yayin saduwa, amma maniyyin ba ya ɗauke da ƙwayoyin halittar da za su iya haddasa ɗaukar ciki.
Farida ta ce mutane da yawa na ɗaukar vasectomy a matsayin hanya ta dindindin, amma a zahiri akwai yiwuwar a sake haɗa bututun a wata tiyata idan mutum ya sauya ra'ayi kuma yana son sake haihuwa a nan gaba.
"Vasectomy hanya ce mai tasiri sosai wajen hana ɗaukar ciki, kuma akwai hanyoyin likitanci da za a iya amfani da su wajen sake haɗa kwaroron idan buƙatar hakan ta taso.
Sai dai nasarar sake samun haihuwa bayan an mayar da ita na iya bambanta daga mutum zuwa mutum," in ji ta.
Ta ƙara da cewa duk namijin da ke tunanin yin vasectomy ya kamata ya tattauna da ƙwararren likita domin fahimtar amfaninta, haɗurranta, da kuma yiwuwar mayar da ita idan ya buƙata a gaba.
Ƙaurace wa saduwa na wucin-gadi

Asalin hoton, Getty Images
Farida ta ce wani lokaci ma'aurata kan yanke shawarar dakatar da saduwa na wani ɗan lokaci domin guje wa samun ciki wadda ita ma na daga cikin hanyoyin tazarar haihuwa ga maza.
Ta ce wannan hanya ba ta buƙatar magani ko wata na'ura, amma tana buƙatar amincewa da juna da kuma jajircewa.
Farida Abdullahi ta jaddada cewa tazarar haihuwa ba nauyin mata kaɗai ba ne. A cewarta, idan maza suka shiga cikin shawarwari da yanke hukunci kan tsarin iyali, hakan na taimakawa wajen samun kyakkyawar fahimta tsakanin ma'aurata.
Ta ƙara da cewa tazarar haihuwa na da muhimmanci wajen kare lafiyar uwa da jarirai da rage haɗarin matsalolin da ke tattare da haihuwar gwannai da kuma ba iyali damar kula da 'ya'yansu yadda ya kamata.
Ma'aikaciyar jinyar ta shawarci ma'aurata su riƙa tuntubar ƙwararrun ma'aikatan lafiya kafin zaɓar kowace hanya ta tazarar haihuwa domin samun cikakken bayani kan amfaninta da kuma ƙalubalen da ka iya zama tattare da ita.











