Afirka ta Kudu ta nuna damuwa kan shirin Najeriya na kwashe ƴan kasarta

Asalin hoton, Reuters
Afirka ta kudu ta bayyana damuwarta kan shirin Najeriya na kwaso ƴan ƙasarta da ke son komawa gida.
Ministan harkokin wajen ƙasar Ronald Lamola ya tattauna da takwararsa ta Najeriya domin lalubo hanyoyin da za a kawo ƙarshen zaman tankiyar da ke tsakanin ƙasashen biyu.
'' Mun san cewa Najeriya ƙasa ce mai ƴancin ɗaukr irin wannan mataki na kwashe ƴan ƙasarta da ke son tafiya, amma muna ganin cewa yin hakan ba zai magance matsalar shigar baƙi ta hanyar da ba ta dace ba.'' a cewar Ronald Lamola.
A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, ministar harkokin wajen Najeriya Bianca Odumegwu - Ojukwu ta ce har yanzu suna ci gaba da shirya kwaso ƴan Najeriya, kuma ta buƙaci hukumomin Afirka ta Kudu su ɗauki tsatsauran mataki kan kisan ƴan Najeriya.
''Ba za mu zauna muna kallon cin zarafi da wulaƙanta ƴan ƙasarmu a Afirka ta Kudu ba, da kuma kisansu babu gaira babu dalili'' in ji ta.
Ta kuma bayyana damuwa kan yadda ake hantarar yara a makaranta, sai dai Lamola ya ce hukumomin ilimi na ƙoƙari wajen kare yara.
Zanga zangar ƙyamar baƙi da ake yi a makonnin baya bayan nan a Afirka ta kudu ya sanya damuwa a zuƙatan baƙi daga ƙasashen Nahiyar, musamman masu gudanar da kasuwanci, duk da zai zanga zangar na lumana ne.











