Da gaske ne Iran na amfani da kifaye a matsayin ƴanƙunar baƙin wake?

Picha ikionyesha pomboo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Picha ikionyesha pomboo
Lokacin karatu: Minti 4

A wani taron manema labarai a Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, ɗaya daga cikin tambayoyin da manema labarai suka yi ita ce, "shin Iran tana amfani da ƴanƙunar baƙinwake?"

Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth ya mayar da martani da cewa "Ba zan iya tabbatarwa ko musanta amfani da kifayen dolphins a matsayin ƴanƙunar baƙinwaƙe ba, amma zan iya tabbatar da cewa ba su da su."

Janar Dan Caine ya ce bai taɓa jin rahotannin ba, kuma ya yi tambaya kan ko labari ne kawai.

Kalaman na magana ne kan wani labari da aka wallafa a Wall Street Journal kwanaki biyar da suka wuce mai taken "Iran na neman mafita kan toshe tashoshin jiragen Iran".

Labarin ya nuna cewa toshe tashoshin jiragen ruwan Iran da sojojin ruwan Amurka ke yi ya bayyana rauni a dabararsu na iko da mashigar Hormuz, sannan kuma Iran na neman hanyar yin amfani da giɓin don amfaninta.

.

Asalin hoton, Getty Images

Jaridar Wall Street Journal ta kuma ce

"Jami'an Iran Iran sun ce Tehran na iya amfani da makaman da ba ta taɓa yi ba, daga jiragen ƙarƙashin teku zuwa kifayen dolphins ɗauke da bama-bamai don kai wa jiragen yaƙin ruwan Amurka hari. Rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) ta yi barazanar zafafa rikici ta hanyar katse wayoyin sadarwa na ƙarƙashin teku da ke mashigar Hormuz, wani mataki da ka iya kawo tarnaƙi ga sadarwar intanet a duniya."

Duk da cewa yin amfani da kifayen dolphins da sojoji ke yi na iya zama wani shaci-faɗi, an ɗauki tsawon shekaru ana yi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shekaru 26 baya, ranar 8 ga Maris ɗin 2000, BBC ta ruwaito cewa Iran ta mallaki kifayen ƙunar baƙin wake.

Rahoton ya ce an sayar wa Iran kifayen dolphins ɗin da suka samu horo daga sojojin ruwan Soviet, amma babu masaniya kan abin da za su yi a yankin Persian Gulf a lokacin.

Ƙwararru a Rasha sun horar da kifayen na dolphins da wasu dabbobin ruwa kan yadda za su far wa maƙiya da jiragen ruwa da ƙwararrun masunta amma an tura da yawansu zuwa wuraren adana kayan tarihi saboda ƙarancin kuɗi.

Boris Jurid, mai horas da kifin dolphin ne sannan ya soma aikinsa a matsayin jami'in jirgin ruwan ƙarƙashin teku.

A lokacin, an ce ya sayar da dabbobin ruwan ga Iran saboda ba zai iya ɗawainiyar abinci da kula da su ba.

Wani rahoton BBC a lokacin ya ce an tura dabbobi 27, har da kifayen dolphins, da giwar ruwa daga Sevastopol da ke yankin Crimean Peninsula zuwa yankin Gulf na Persia ta jirgin dakon kaya.

Kifayen dolpins huɗu da kifin whale sun samu horo a wajen Jurid a sansanin sojin ruwa da ke tekun pacific kafin turasu daga Crimea a 1991. An bai wa dabbobi horo kan yadda za su kai wa maƙiya hari ta hanyar amfani da wani makami mai tsini da aka rataya a bayansu ko kuma su janyo su daga wuta don a ɗauke su.

Sjan Ruwan Amurka tare da kifinsa na dolphin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sojan ruwan Amurka mai horar da dabbobi Bud Bickford ya taimaka wa kifinsa na dolphin mai shekara 33, Makai, sake shiga ruwa bayan yin iyo a Umm Qasr Harbor ranar 29 ga Afrilun 2003. Bayan kutsen da aka yi wa Iraki, sojojin ruwan Amurka sun yi amfani da horarrun kifayen dolphins wajen ganowa da kuma kwance nakiyar da aka dasa a ruwa.

Kifayen dolphins da suka samu horo na iya farwa jiragen ruwan maƙiya ta hanyar kai hare-haren ƙunar baƙinwake, su ɗauki na'ura da za ta fashe da zarar sun doki jirgin.

An ce kifayen dolphins ɗin suna iya tantance tsakanin jiragen ƙarƙashin tekun Soviet da na baƙi ta ƙarar na'urar da ke taimakawa jirgi ya yi motsi.

Ba ya ga Rasha, ƙasar da aka sani tana horar da kifayen dolphins don amfanin ojoji ita ce Amurka, wadda ke da wani shiri a San Diego da ke Californa.

A shekarun baya-bayan nan, akwai rahotanni da ba a hukumance ba na ƙoƙarin da wasu ƙasashe kamar Koriya ta Arewa ke yi na horar da kifayen dolphins.

Tun bayan mamayar Ukraine, rahotanni na cewa Rasha ta ƙara yawan kifayen dolphins a tashar Sevastopol domin tunkarar maƙiya da kuma kare jiragen sojinta a Baharul Aswad.

Wani kifin dolphin da ya samu horon sojan ruwan Amurka domin gano nakiyar da aka sa a teku

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hoto daga 1973: Wani kifin dolphin da ya samu horon sojan ruwan Amurka domin gano nakiyar da aka sa a teku

Akbar Hashemi Rafsanjani, wani littafi da ya wallafa mai taken "Sauye-sauyen da ake samu lokacin yaƙi", ya yi rubutu kan abubuwan da suka faru a Fardarvin 2 1990.

"Kifayen dolphins dabbobi ne masu basira kuma suna bin umarni sosai, sai dai idan aka zo batun waƙa."