'Babu wani ɗan takara da zai kai labari a Nijeriya ba tare da ƙuri'un Igbo ba'

Buba Galadima
Bayanan hoto, Buba Galadima
Lokacin karatu: Minti 3

Wani jigo a tafiyar Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce sun koma jam'iyyar NDC ne saboda gadar zaren da suke tsoron an shirya wa ADC, yayin da Nijeriya ke tunkarar zaɓen 2027.

Buba Galadima ya shaidawa BBC cewa halin da ƴan adawa suke ciki a Najeriya, na buƙatar canza tunani da sake dabara.

''Ai in aka ce a mai da sunan David Mark, ba bu zancen kuma a koma wani kotu, a ci gaba da bahasin abinda ya wuce. Amma fa idan ka mai da mu baya to taradaddin in mun ka tsaya zai iya fa kai mu baɗi, sai dab da zaɓe kotun farko ko ta biyu kafin a zo kotun ƙoli su yi mana abinda bama so''

''Mu ko buƙatar mu ita ce duk yadda za a yi a samu ɗan takarar da zai tsaya da Tinubu a kowace jamiyya ne, in ma ya yayyanke wuyan dukan sauran jam'iyyu, in ɗaya ya yi saura, kai ko da makara ce ta yi saura, amma tana da rajistar cewa za ta tsaya zaɓe, dukanmu sai mu zaɓeta'' in ji shi

Ya kuma jadada zargin da ya yi a kan cewa gwamnati na da hannu a ƙoƙarin tarwatsa jam'iyyun hammaya

''To in mai magana wawa ne majiyin magana ba wawa bane. Dukan abinda ke faruwa a nan ai an san da hannun gwamnati a ciki, Waye kuma gwamnatin'' ?

Ya ce zargin cewa sun sayar da arewa, ba gaskiya ba ne, don kuwa babu wani ɗan takara da zai kai labari a Nijeriya ba tare da ƙuri'un Igbo ba.

''To ai indai kwakwara ne ai ba dan takara da ya kai kwankwaso amma yana da na shi rauni wanda ya ke gani in ya tsaya a kan kafarsa ba zai samun goyon bayan wadanda suke hassada da kiyashinsa ba , ai tunda muna son mu gyra kasa, muna son mu yi mulki, in ka kira shi zallama aiki baka yi laifi ba''

''In ba mu yi zallama, mun yi hobbasa na karbar mulkin ba, ina zamu sami damar da za mu gyra kasa talaka ya amfana, talaka ya numfasa, 'yayansa su samu makaranta, 'yayansa su zama mutane su sami magani a asibiti, a samu hanyoyi''

''Ai rashin fahimta ne, ai abinda ake kira muna goyon bayan iyamuri, duk zage -zagen da ake yi mu na ji kab dinsa amma rashin sanin tarihi ya sa ake wannan''

''Sardauna da Tafawa Balewa su suka fara aiki da inyamuri ya yi mu su shugaban kasa watau Azikiwe, ko baa yi haka ba a tahiri?''

Game da fargabar da ake nuna wa a kan cewa watakila har yanzu akwai wani bangare na alummar ibo da ke tunanin balewa daga Nijeriya sai ya ce:

''To kai ka manta Tinubu da ya ce ba bu ruwan shi da Najeriya shi da kansa ba ma mukarabansa ba, kun zabe shi, yanzu yana galaza mana , ka taba jin Peter Obi ya ce a raba kasa'' in ji shi.