Bayern Munich za ta ninka albashin Olise,Real Madrid na harin Haaland

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United da Arsenal sun sa ido kan ɗan wasan Bournemouth da Ingila Alex Scott mai shekara 22, amma duk wani ciniki zai iya kai wa kusan fam miliyan 60.(Mail), external

Arsenal na kuma tattaunawa da Leicester City kan dan wasan Ingila na 'yan kasa da shekaru 19 , Jeremy Monga, inda Gunners ke shirin biyan kudi mai kyau ga dan wasan mai shekara 16 domin guje wa shari'ar kwamitin kwadago.(Athletic - subscription required), external

Real Madrid za ta fara tattaunawa da Chelsea kan daukar dan wasan kasar Argentina Enzo Fernandez, mai shekara 25, bayan ta mayar da shi babban burinta a bangaren tsakiya a wannan bazarar.(AS), external

Aston Villa ta nuna matuƙar sha'awa kan ɗan wasan West Ham da Ingila, Jarrod Bowen, mai shekara 29, amma cimma yarjejeniya na iya zama da wuya saboda sai Villa ta sayar da wasu 'yan wasa. (Athletic - subscription required), external

Aston Villa ta kuma ta fito fili karara ta bayyana wa kungiyoyin da ke zawarcin Morgan Rogers cewa ba ta son ta sayar da dan wasan na Ingila, mai shekara 23, a wannan bazarar. (Sky Sports), external

Newcastle United na zawarcin dan wasan Cologne da kuma tawagar 'yan kasa da shekara 21 ta Jamus, Said El Mala, mai shekara 19, sannan suna tattaunawa kan dan wasan Lille da Belgium, Matias Fernandez-Pardo, mai shekara 21. Amma Liverpool ma na zaman jira, idan suka kasa daukar dan wasan RB Leipzig da Ivory Coast,Yan Diomande, mai shekara 19, ko kuma dan wasan Paris St-Germain da Faransa, Bradley Barcola, mai shekara 23. (Mail), external

Arsenal na ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar kulla yarjejeniya daukar dan wasan Atletico Madrid da Argentina, Julian Alvarez, mai shekara 26.(Teamtalk), external

Bayern Munich na shirin ninka albashin dan wasan Faransa, Michael Olise, a matsayin wani ɓangare na yarjejeniya domin rike dan wasan mai shekara 24 a kungiyar har zuwa shekarar 2031.(Christian Falk), external

Real Madrid na harin dan wasan Manchester City da Norway, Erling Haaland, mai shekara 25, idan dan wasan Brazil Vinicius Jr, mai shekara 25, ya bar filin Bernabeu.(Sport - in Spanish), external

Ana sa ran Manchester United za ta fara yin tayin a hukumance domin daukar dan wasan tsakiya na West Ham da Portugal, Mateus Fernandes, mai shekara 21, a cikin kwanaki masu zuwa.(Teamtalk), external

Dan wasan Borussia Monchengladbach da Switzerland, Nico Elvedi, mai shekara 29, ya bude kofar komawa Leeds United.(Football Insider), external

Aston Villa na tattaunawa da Flamengo kan daukar dan wasan Brazil Emerson Royal mai shekara 27.(Talksport), external