An busa hutu - za su je su huta
Za su huta minti 15 daga nan su dawo a karasa minti 45 a wasa na bibiyu a gasar cin kofin duniya a rukuni na 10.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mohammed Abdu tare da taimakon AI
Za su huta minti 15 daga nan su dawo a karasa minti 45 a wasa na bibiyu a gasar cin kofin duniya a rukuni na 10.
Argentina tana ta kashe lokaci, inda take bani in baka daga hagu zuwa dama tana tuttura kwallon baya daga nan ta kara matsawa gaba.
Messi yana ta tafiya a cikin tdakiyar fili ba abinda ya dame shi.
Ko Austria za ta farke kwallon da aka zura mata ko Argentina za ta je hutu da wannan sakamakon?
Argentina tana da maki shida da cin kwallo hudu a wasa biyu daga cikin rukuni na 10 a gasar cin kofin duniya.
Ita take rike da kofin da ta lashe a Qatar a 2022.
An bai wa Stefan Posch katin gargadi, sakamakon rike Thiago Almada da ya yi.
Shi kenan ya kafa tarihi!!!!
Lionel Messi shi ne dan wasan da ya fi yawan zura kwallaye a gasar cin kofin duniya, yayin da ya ci Austria kwallo mai kyau aka bugo daga gefen hagu, shi kuma yana gidan Austria bai bata lokaci ba ya buga ta faɗa raga.
An kafa tarihi a filin wasa da ke Dallas a Amurka.
Argentina ta ruga da gudu da kwallon ta hannun Lautara Martinez amma mutum biyar sun hau kansa, ya yi kokarin bai wa Enzo Fernandez kwallon amma ta yi yawa.
Nahuel Molina ya yi kuskure a tsakiyar filin bayan da ya kayar da Marcel Sabitzer har kasa ƙasa.
Dan wasan Austrian yana taka leda mai kyau, kuma karo na 100 da yake buga wa kasarsa tamaula.
Lionel Messi ya shiga cikin gidan Austria ya kuma buga ta taba gola ta koma wajen abokan hamayya.
Argentina na samun damar maki a karawar nan. Messi na barar da kwallaye kam da yanzu sun kai wasu ukun rigis.
An ci gaba da wasan, kuma Austria na kai kora, kamar Argentina ta koma tare gida, amma wasan ya fara kyau.
Wasan dai na tafiya, amma Austria na buga karawar da kwarin gwiwa.
Amma da Argentina ta ci bugun fenariti da watakila jikinsu ya yi sanyi, amma yanzu suna kazar - kazar
Daman wasan nan ba zai zowa Argentina da sauki ba, itama Austria sai kai kora take daga hagu zuwa dama, har ma ta samun bugun kwana. An kuma buga ba wani hadari.
Lautaro Martinez ya yi wa Konrad Laimer keta, kuma alkalin wasa bai bayar da katin gargadi ba.
Kadan ya rage Messi ya ci kwallo bayan da ya yanke mai tsaron bayan Austria, sai nan da nan ya buga kwallon, amma a lokacin mai tsaron raga ya fito shi ne ta doki kafarsa ta yi gefe da yawa.
Marcel Sabitzer ya buga kwallo zuwa cikin gidan Argentina amma ba ta yi kyau ba.
Lionel Messi ya yi ƙoƙari ya ja kwallo amma an kwace.
Messi ya buga fenariti da kafarsa ta hagu zuwa daman turken Austria, amma ta yi fadi ta yi waje ya kuma sunkuyar da kansa kasa.
Messi ya dauki kwallo zai buga ko zai ci?
Ana tunanin da akwai fenariti - an kuma duba alkalin wasa ya bayar da fenariti.
Ana duba lafiyar Lautaro, wanda ya je cin kwalo yan wasan Austria biyu suka rutsa shi a tsakiya lokacin da zai sa kafa ya buga kwallo suma suka sa kafafunsu, alkalin wasa ya ce ba komai a lokacin da dan wasan ya fadi.
Filin wasa a Dallas makil da yan kallo dauke da launin shuɗi da fari. A zahiri, wasan tamkar gida ne ga Argentina a nan.