Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilai 4 da suka jefa Real Madrid cikin ruɗani
Maimakon makon nan ya karkata gaba ɗaya kan wasan da ke da matuƙar muhimmanci na El Clásico tsakanin Real Madrid da Barcelona, rahotanni sun mamaye shi da labaran rikici da rashin kwanciyar hankali a ɗakin canja kaya a Real Madrid.
Idan Real Madrid ta sha kashi a ranar Lahadi a wasan hamayya a La Liga, hakan zai bai wa Barcelona damar lashe kofin bana karo na biyu a jere, ita kuwa Real Madrid za ta kare kaka biyu a jere ba tare da ɗaukar kofin ba.
Sai dai yayin da Barcelona — wadda ita ma ta taɓa shiga rikici ba da dadewa ba — ke ci gaba da samun nasarori, Real Madrid na fuskantar ruɗani sakamakon rashin jin daɗi daga magoya baya da rashin tabbas kan makomar koci da kuma zarge-zargen rikici tsakanin ƴan wasa.
Rahoton BBC Sport ya duba abubuwan da suka faru a makon da ya gabata da kuma dalilin da ya sa suka ƙara tayar da hayaniya kan kakar da ta fara rushewa a fili da kuma cikin gida.
Rikice-rikice da batun koken magoya baya da matsalolin ladabtarwa.
Rahotanni sun fara bayyana a kafafen yaɗa labarai a Sifaniya ranar Laraba cewa ƴan wasan Real Madrid, Federico Valverde da Aurélien Tchouaméni sun yi zazzafar mayar da juna kalamai a yayin atisaye.
Daga baya Valverde da kansa ya tabbatar da hakan, kuma ana ganin lamarin ya ƙara tsananta ranar Alhamis a cibiyar atisayen Real Madrid.
Majiyoyi sun shaida wa BBC Sport cewa gardamar ta ci gaba bayan atisaye kuma ta kai ga aka garzaya da Valverde asibiti, saboda raunin da ya ji a kai bayan wata hatsaniya a ɗakin canja kaya.
Daga baya Valverde ya musanta rahotannin cewa sun yi fada da juna, yana mai cewa raunin ya faru ne bayan da "ya bugi tebur bisa kuskure" yayin rikicin.
A cikin wata doguwar sanarwa da aka fitar ranar Alhamis da yamma, ɗan wasan Uruguay ya ce na ji "ƙaramin ciwo a goshina wanda ya sa aka kai ni asibiti domin duba lafiyata," sannan ya ƙaryata zargin cewa ɗayansu ya bugi ɗaya.
Daga baya an kira wani taron gaggawa wanda ya haɗa da shugaban ƙungiyar, Florentino Pérez da mambobin masu horaswa da babban koci, Álvaro Arbeloa da ƙyaftin, Dani Carvajal.
Bayan haka Real Madrid ta fitar da sanarwa biyu.
Ta farko ta tabbatar da cewa an buɗe matakan ladabtarwa kan ƴan wasan biyu, tana mai cewa ƙungiyar za ta bayar da ƙarin bayani "bayan an kammala yin binciken cikin gida."
Ta biyu kuwa ta kasance sanarwar koshin lafiyar Valverde, kuma zai bukaci hutu na kwana 10 zuwa 14, abin da ya sa ba zai buga wasan El Clásico na ranar Lahadi ba.
"Babu shakka wani a nan yana yaɗa jita-jita, kuma idan kakar wasa ta kasance babu kofi, inda kullum ake sa ido sosai kan Real Madrid, komai yana ƙara girma fiye da yadda yake," in ji Valverde.
An samu rarrabuwa tsakanin ƴan wasa
Mai tsaron baya, Alvaro Carreras ma ya mayar da martani a wannan makon kan rahotannin da suka danganta shi da wani saɓani daban da abokin wasansa Antonio Rüdiger.
Carreras bai ambaci sunan ɗan wasan kai tsaye ba, amma ya rubuta a Instagram cewa:
"A cikin kwanakin baya, an yi wasu maganganu da zarge-zarge a kaina waɗanda ba gaskiya ba ne.
"Dangane da lamarin da ya faru da wani abokin wasa, al'amari ne na musamman wanda ba shi da wani muhimmanci kuma an riga an warware shi. Dangan taka ta da dukkan ƴan wasan ƙungiyar tana da kyau sosai."
Batun tadardar kirayen a kori Kylian Mbappe
Rahotannin rashin jituwar da ake zargin akwai tsakanin wasu 'yan wasa sun biyo bayan manyan zarge-zargen rashin kwanciyar hankali a ɗakin canja kaya.
An fi mayar da hankali kan fitaccen ɗan wasan gaba Kylian Mbappé.
Dan wasan gaban na Faransa ya ci ƙwallaye 85 a wasanni 100 tun bayan zuwansa Santiago Bernabéu Stadium, amma ya shiga ce-ce-ku-ce bayan ya yi tafiya zuwa Sardinia yayin da yake murmurewa daga raunin hamstring da ya samu a wasa da Real Betis.
Ko da yake kulob ɗin ya amince da tafiyar, hotunan ɗan wasan yana cikin jirgin ruwa sun bazu a intanet yayin da Real ke buga wasa da RCD Espanyol, lamarin da ya jawo suka daga magoya baya waɗanda tuni suka nuna rashin jin daɗi kan matsalolin ƙungiyar.
Wata takardar koke ta intanet mai taken "Mbappe out" ta yi fice cikin sauri a kafafen sada zumunta, kuma yanzu tana da sama da sa hannu miliyan 46.
Álvaro Arbeloa ya ce za a yanke hukunci kan ko ɗan wasan gaba zai buga wasan ranar Lahadi daga baya a wannan makon.
Rashin tabbas kan matsayin mai horarwa
Waɗannan matsaloli da kuma rashin samun sakamakon da ƙungiyar ke samu a lokacin wasannita sun sa hankali ya koma kan babban koci Álvaro Arbeloa da kuma abin da ake gani a matsayin gazawarsa wajen jagoranci da rashin haɗin kai a ɗakin canja kaya na ƴan wasa a wannan lokaci mai cike da rikici.
Tsohon mai tsaron bayan, Real Madrid ya maye gurbin Xabi Alonso, wanda ya yi wata shida a aikin horar da ƙungiyar.
Karancin gogewarsa a matsayin babban koci ya kasance abin tattaunawa tun daga lokacin da aka naɗa shi aiki, tun daga lokacin ake tunanin yadda zai yi aiki tare da taurarin ƙungiyar irin su Kylian Mbappé da Vinícius Júnior.
Abubuwan da suka faru a wannan makon sun tabbatar da rashin iya jaguranci da gogewa a idanun magoya baya da dama.
Da yake wasa huɗu suka rage wa Real Madrid a kammala wannan kakar, babban abin da Arbeloa zai fi mayar da hankali shi ne dawo da kwanciyar hankali da natsuwa da mayar da hankalin ƴan wasa su fuskanci kalubalen da ke gabansu da kuma hana ci gaba da taɓarɓarewar wasa da ladabtarwa.
Ko da yake Real Madrid ba za ta lashe kofi ba a kakar nan, har yanzu akwai buƙatar kammala kakar wasan nan cikin wani tsari na komawa kan ganiya.
Sai dai fiye da wannan ɗan gajeren lokaci, hankali ya riga ya fara komawa kan shugabannin ƙungiyar da yadda za a fuskanci matsalolin nan a kaka mai zuwa.
Yanzu akwai matsin lamba kan shugaba, Florentino Pérez, wanda ke fuskantar ɗaukar matakin da ya dace da zai haɗa da yanke shawara bayan sauye-sauyen masu horarwa da suka kasa kawo nasara mai ɗorewa.
An sauya masu horarwa uku a kaka biyu. Babu kofi ko ɗaya
Zaɓin babban kocin da ƙungiyar za ta yi nan gaba zai kasance mai matuƙar muhimmanci — ba kawai wajen samun sakamako a fili ba, har ma wajen dawo da kwanciyar hankali da komawa kan ganiya.
Hakan kuma zai taimaka wajen gyara martabar ƙungiyar da yanzu take fuskantar suka daga jama'a, kuma tana fatan hakan zai mayar da su kan kololuwa da suka rike a fannin ƙwallon ƙafa a duniya.