Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matsalar rauni da koken magoya baya – me ke faruwa da Kylian Mbappé?
Makomar Kylian Mbappé a Real Madrid zuwa yanzu na tangal-tangal, saboda abubuwa ba sa tafiya yadda aka yi tsammani tun a farko.
Duk da cewa ɗan wasan mai shekara 27 ya ci ƙwallo 85 a wasa 100 tun bayan komawarsa filin Santiago Bernabéu, ƙungiyar na daf da ƙare kaka ta biyu a jere ba tare da lashe kofi ba.
A tarihin ƙungiyar mai kofin La Liga 36 da na Champions League 15, wannan gagarumar koma baya ne ga Real Madrid.
Tuni magoya bayan Real Madrid ke nuna fushinsu a fili, bayan jita-jitar rashin jituwa a ɗakin hutun ƴanwasa. BBC Sport ta duba yadda kakar wasa ta biyu mai ƙalubale ga Mbappé a birnin Sifaniya ta ci karo da cikas.
Ce-ce-ku-ce kan hutun da ya je tsibirin Sardinia
A halin yanzu Kylian Mbappe na yin jinya, sakamakon raunin da ya ji a ƙarshen watan Afrilu a wasa da Real Betis a La Liga. Wannan ya sa akwai shakku ko zai iya buga wasan El Clásico na ranar Lahadi da Barcelona.
Real Madrid dole ne ta ci wannan wasan domin hana Barcelona lashe kofin La Liga a ranar.
A al'ada, wannan ne ya kamata ya zama babban abin damuwa da ƴan wasa da mahukunta. Amma a maimakon haka, hankali sai ya fi karkata kan abubuwan da suka faru a wajen filin atisaye.
An bai wa ɗan wasan na Faransa hutu a makon da ya gabata, kuma ya yanke shawarar tafiya zuwa tsibirin Sardinia yayin da yake jinya. Duk da cewa Real Madrid ɗin ta amince da tafiyar, amma hakan bai yi wa magoya baya daɗi ba.
An ga hotunansa yana kan jirgin ruwa na ƙasaita da suka bayyana a kafar sada zumunta a lokacin da Real Madrid ke buga wasan La Liga da Espanyol.
Mai horarwa Álvaro Arbeloa ya ce: "Tunda yana cikin hutu, Mbappé zai iya yin duk abin da yake so, kamar yadda kowane ɗan wasa zai yi."
Sai dai rashin jin daɗi daga magoya bayan Real Madrid ya kai su ga ɗaukar mataki.
An fara da rubuta takardar koke (petition) a yanar gizo mai taken "Mbappé ya bar ƙungiyar", wadda ta bazu sosai a kafafen sada zumunta, tana ƙarfafa neman sa hannun daga magoya baya su nemi sauyi da kuma ɗaukar mataki kan makomar ɗan wasan a ƙungiyar.
An yi niyyar tattara sa hannun mutum 200,000, amma sai aka samu sama da miliyan 12 da suka sanya hannu cikin ƙasa da awa 24.
Ko da yake ba a san ko duk waɗanda suka sanya hannu magoya bayan Real Madrid ba ne, wannan martani ya zo ne a wani lokaci mai matuƙar muhimmanci.
Real Madrid na dab da kammala kakar wasan bana ba tare da lashe kofi ba, tana mataki na biyu a teburi da tazarar maki 11 a gasar La Liga, sannan an fitar da ita daga UEFA Champions League a matakin kwata fainal.
A wannan yanayin, ana ƙara sa ido sosai kan manyan ƴan wasa, kuma Mbappé, duk da kasancewarsa kan gaba a yawan zura kwallaye a ƙungiyar a wannan kakar, yanzu yana fuskantar suka mai tsanani.
Mataki na gaba kan Kylian Mbappé
Kocin Madrid ya ce, "A Sifaniya mun shahara wajen ƙirƙirar labarai daga ƙananan abubuwan da muke gani game da ƴanwasa."
"A cikin makonnin da Real Madrid ta yi wasa mara kyau, wani ɓangare na muhawarar shi ne: me ya sa Kylian Mbappé ba ya gudu sosai? Me ya sa ake samun matsala idan an haɗa shi wasa da Vinícius Júnior? Kuma me ya sa yanzu shekara biyu ke Real Madrid za ta yi ba tare da lashe kofi ba tare da shi a ƙungiyar?"
Arbeloa ya ƙara da cewa, "A ganina, wannan muhawara ba daidai ba ce gaba ɗaya — kowa yana son Mbappé, kuma kasancewarsa a ƙungiyar ba matsala ba ce; matsalolin suna wani wuri dabam."
Ya ce matsalar ita ce idan aka ga Mbappé yana hutu tare da budurwarsa duk da cewa yana bin duk shawarwarin likitoci don murmurewa daga jinya ko kuma aka gan shi yana sauka daga jirginsa a Madrid ƙasa da minti 18 kacal kafin Real ta fara wasa, sai ake ganin hakan a matsayin matsala.
"Wani abu da mutanen da ke kusa da Xabi Alonso ke faɗa daga lokacin da yake Madrid shi ne cewa Mbappé ya fi damuwa da kafa tarihi da ƙwallayen da ya ci a tamaula."
"Wannan na iya bayyana dalilin da ya sa, duk da cewa bai ji daɗin raunin gwiwarsa ba bayan an yi bincike sai agano raunin, amma ya so ya buga karawar domin ya yi ƙoƙarin wuce ƙwallo 59 da Cristiano Ronaldo ya ci a cikin shekara guda. Ke nan da alama yana son yin tasiri shi kaɗai, ba kawai tare da ƙungiya ba."
Sai dai kocin ya ce har yanzu ba a gama yanke hukunci kan Mbappé ba. "Amma wasu lokuta yana kame jikinsa daga magoya baya, ina tuna Raúl González yana cewa abu ɗaya da magoya baya suke so shi ne ka yi gudu ka karɓo ƙwallo ko wadda za ta fita mai dai ɗan karen wahala. Mutane suna son hakan."
Tabbas da Real Madrid tana yin nasara, labarin zai bambanta. Tambayar ita ce: ba sa samun nasara ne saboda masu hororwa ba sa iya morar kwazon Mbappé , ko kuma saboda shi ne baya yin abinda ya kamata ƙungiyar ke bukata?
A farkon zuwansa Madrid, ya shiga wani lokaci na fara fuskantar yadda ake gudanar da wasu abubuwa a Real Madrid, kuma yana yin abin da aka umar ce shi a ƙarƙashin Carlo Ancelotti.
Sai dai bayan yaarar da bugun fanareti guda biyu a wasa da Liverpool da Athletic Club, ya shiga damuwa sosai, kuma ya ce "zan bi tsari na kaina."
Daga nan ne ya fara zura ƙwallaye, kuma ya zura da yawa a raga a ƙarƙashin Ancelotti. Amma a kakar barar, abubuwa ba su tafi yadda ya kamata ba — ko a ƙarƙashin Xabi Alonso ko Álvaro Arbeloa.
Yaya ake ganin lamarin a Sifaniya?
Kafofin yaɗa labarai a Spain sun mayar da hankali sosai kan Kylian Mbappé, wanda hakan ke nuna muhimmancinsa a Real Madrid da kuma matsalolin da ƙungiyar ke fuskanta a wannan kakar wasan.
Gidajen jaridu a fadin Spain su kan yi binciki ba kawai yadda yake taka leda ba, har ma da halayensa a wajen fili. Tafiyarsa zuwa Sardinia an fi kallonta a matsayin abin da bai zo a lokacin da ya dace ba, ba wai laifi kai tsaye ya aikata ba.
Rubuce-rubucen ra'ayi suna ƙara mai da hankali kan yadda ya haɗu da sauran ƴan wasa da kuma tasirinsa a tsarin ƙungiyar. Musamman, ana ta muhawara kan ko Mbappé da Vinícius Júnior za su iya taka leda tare cikin tsarin kai hare-hare da ƙungiyar za ta amfana.
A talabijin da rediyo kuwa, masu sharhi suna kuma tambaya ko ana yi masa hukunci fiye da yadda za a yi wa wasu ƴan wasa a irin wannan yanayi. Wasu marubuta kuma suna ganin sukar da ake yi masa ta samo asali ne daga rashin ƙyaƙƙyawar kakar wasa da Real Madrid ke yi, ba shi kaɗai ba.
Gaba ɗaya, salon rahotannin Spain yana sukar ɗan ƙwallo, amma ya rabu gida biyu. Wasu suna kare shi saboda yawan ƙwallayensa da muhimmancinsa, yayin da wasu ke tambayar jagorancinsa da tasirinsa gaba ɗaya a wannan kakar mai wahala.
Haka kuma akwai batun cewa samun mai horor da ƴan wasa da ya dace zai kasance muhimmi wajen dawo da haɗin kai da kwarin gwiwa a cikin ƙungiyar, bayan wannan kakar da ba ta yi kyau ba.
Saƙon da ke bayyana a yawancin sharhi a bayyane yake: kakar wasa ta uku ba tare da lashe kofi ba, babu wani korafi da mahukunta da magoya baya za su amince dashi a baɗi.