Mayaƙan ISWAP sun kashe sojojin Najeriya biyu a Borno
Mayaƙan ISWAP sun halaka sojojin Najeriya biyu da ke aiki ƙarƙashin rundunar Haɗin Kai a Magumeri da ke jihar Borno.
Lamarin ya faru ne yayin da dakarun da ke aiki ƙarƙashin rundunar suka daƙile wani harin ISWAP, abin da ya yi sanadin mutuwar ƴan ta'adda da dama har ma ta kai ga ƙwato makamai daga hannunsu.
Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Leftanar kKanar Sani Uba ya fitar wanda shi ne jami'in yaɗa labarai na rundunar Operation Haɗin Kai.
Samamen dai ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis lokacin da ƴan ta'adda suka yi yunƙurin mamaye wani sansani na rundunar.
Rundunar soji ta ce sojoji sun kai martani cikin sauri lamarin da ya sa suka daƙile harin tare da kashe mayaƙan da dama.
Daga cikin makaman da sojojin suka ƙwato a hannun mayaƙan akwai bindigoyi ƙirar PKT da AK47 da kuma tarin alburusai.
A cewar sanarwa, soja guda da wasu da suka ji rauni na samun kulawa.