Kila Rashford ya ci gaba da zama a Barca, Jackson zai ci gaba da wasa a Chelsea

'

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, '
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Watakila tayin da Saudiyya ta yi wa dan wasan Barcelona Raphinha, mai shekara 29, ya karawa dan wasan Ingila Marcus Rashford mai shekaru 28 fatan komawa kungiyar ta La Liga daga Manchester United (Talksport), external

Yadda dan wasan Netherlands Crysencio Summerville ya buga kwallo a gasar cin kofin kwallon kafa ta Fifa ya shafi zawarcin da Manchester United ke yi masa, saboda a yanzu Paris St-Germain na sha'awar dan wasan kungiyar West Ham mai shekara 24.(Mirror), external

Manchester United ba ta da niyyar sayar da dan wasan Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 23 a bazara, duk da cewa Barcelona da Atletico Madrid na son daukarsa. (Teamtalk), external

Brighton na nazari kan ko ta sabunta kwantaragin Yasin Ayari ko ta amincewa dan wasan Sweden mai shekara 22 barin kungiyar yayin da Newcastle ke zawarcinsa. (Football Insider), external

Arsenal na da kwaring gwiwa Declan Rice zai taimaka wajan shawo kan dan wasan Ingila Morgan Rogers, mai shekara 23, komawa kungiyar daga Aston Villa a wannan bazara . (Mirror), external

Jerin sunnayen wasan da Juventus ke son ta siya a wannan bazara sun hada da mai tsaron ragar Aston Villa da Argentina Emiliano Martinez, mai shekara 33 da dan wasan Ingila John Stones mai shekara 32 wanda ya bar ,Manchester City a wannan bazara . (Gazzetta dello Sport - in Italian), external

Leeds ta gabatar da tayin farko na kusan fam miliyan 20 ga Southampton kan dan wasan Ireland Shea Charles, mai shekara 22.(Teamtalk), external

Dan wasan Senegal Nicolas Jackson, mai shekara 25, ba zai matsa kaimi ba don barin Chelsea saboda yana da niyyar burge sabon koci Xabi Alonso a kakar wasanni ta bana. (Football Insider), external

Stade Rennais na shirin komawa Sunderland dan siyan dan kasar Sipaniya Eliezer Mayenda, mai shekara 21.(Foot Mercato - in French), external

West Ham na zawarcin dan wasan Ingila Adam Webster, mai shekara 31, wanda ba shi da kungiya, bayan ya bar Brighton a karshen kakar wasa ta bana.(Sun), external

Idan Orlando City ta sayi dan wasan Mexico Santiago Gimenez, mai shekara 25, daga AC Milan wannan za isa kungiyar ta Italiya ta maida hankali kan dan wasan PSG da Portugal Goncalo Ramos, mai shekara 25. (Corriere dello Sport - in Italian), external